Sashe 56
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawo shi yanzu. Bata da mai bata amsa, sai ma kira daya shigo wayarta a dai-dai lokacin. Wayar dake acan saman mirror ta an zubama ido, sai ta tsinta kanta da jin nauyin jiki har kiran ya tsinke. Wani kiran ne ya sake shigowa, sai hakan yay dai-dai kuma da fitowar AA hannunsa auke da wata bag arama. Har ya wuce batare daya kalleta ba itama ta mi e da nufin aukar wayar sai ta hangesa agaban mirror in kamar mai neman wani abu. Komawa tai ta zauna, sai kawai jin arar wayarta tai a asa. Da sauri ta ago, wayar tata ce kuwa, yayinda shi kuma yake du e yana duba abu a drawer in jikin mirror in tamkar ma baiga abinda ya faru ba. Oum dake fitowa ta ce, Subahannahi kako yaddoma Auta waya Auta Tsabar rainin hankali irin na AA sai ya juyo irin as bai lura in nan ba ya auki wayar yana jujjuyawa, arasowa itama Oum in tai inda yake ta amshi wayar ta duba. Gaba aya tayi tatsa-tatsa. Screen in yay wani irin zuuuuu alamar ya tashi aiki shima. Babbar waya ce, dan SS ce babba Daddy ya saya mata ita gift in kammala karatun ta. Auta kayi arna Oum ta fa a tana sake jujjuya wayar. Fuskarsa dake a tsuke ya yamutsa babu alamar damuwa a tattare da shi ya ce, Oum ban lura bane. Kawo zanba Ahmad da safe ya gyaro . Yay maganar yana mi ama Oum hannu. Kanta kawai ta girgiza da ora masa wayar a hannunsa. Shi kuma batare daya ce komai ba ya auka bag insa ya fice. Ajiyar zuciya Oum ta sauke tare da juyawa ta dubi Maanal. Karki damu kinji Auta, nasan in sha ALLAHU zai bada a gyara kafin wucewar mu goben Murmushin ya e kawai Maanal taima Oum. Babu komai Oum . Itama Oum in sai tai murmushi tana jinjina mata kanta. Haka sukai shirin barci suka kwanta. Dan har Oum in kwanciyarta tai a gadon tana fa in, ALLAH ya yarda yau zan sake kwanciya gado aya da Babyna Siririyar dariya Maanal ta saki, yayinda Oum ke tayata itama zuciyarta cike da nisha in yanayin..... __________ Washe gari da safe bayan sunyi wanka suna dining da shirin karyawa harda Ya Fawzan AA ya shigo. Da mamaki Oum daya fara gaidawa take kallonsa. Dan a shirye yake tsaf cikin ba en suit da suka sake fiddo ainahin cikar haibarsa da madarar yau. Yau ba Saturday ba na ganka da shirin office? . Oum ta fa a cikin kasa ha uri. Hannu ya mi ama Yaya Fawzan yana bata amsa da, Oum project in nan da nake gaya miki yau zamu fara aikinsa da Engineers inmu Okay aina ma shafa'a, ALLAH yasa ayi cikin nasara ya kuma aga darajarsa. Maza to zauna ka karya dan bazaka fita da yunwa ba Agogon hannunsa mai matu ar nauyin ku i da zama designer daba ako ina zakaje ka samesa ba sai ga wanda ya isa ya kalla. Cikin ata fuska ya ce, Oum Please zansha coffee a office Ban yarda ba kuwa. Zauna in ba hakaba nasa Fawzan ya ri e min kai na maka Dariya sosai Fawzan yake yi, ya ce, Tsaf kuwa zan danne miki shi Oum dan wannan girman jikin nasa da arfuna suka bubbu e ba tsoro zai bani ba. Harararsa AA yayi, dan dole yakai hannu yaja kofin gaban Maanal da tunda ya shigo tai masa kallo aya ta maida kanta bata sake ba, daga tsayen da yake ya kai shayin bakinsa, dai-dai Maanal in tana agowa ta kallesa da mamaki, hakama Fawzan da Oum duk kallonsa sukayi. Amma ya wani basar kamar bai gani ba. Sai Oum ce tai masa nuni da kujera. Maza zauna tunda kadai san babu yau shan abu daga tsaye Baice komai ba ya zauna in, sai faman kallon agogonsa yake yi alamar dai a agare yake. Barrah da Haneeff ne suka fito daga kitchen tare da mai aiki. Dan sunce su noodles zasu ci shine taje dafa musu suka bita. Ganin AA ya sasu nufosa, cikin ha a baki da okin ganinsa sukace, Uncle good morning A mamakin kowa sai ya saki murmushin nan nasa na rowa tare da shafa kawunansu ya na amsawa. Good morning Handsome & Oum na. Fatan kun tashi lafiya? Uncle Alhamdullah Suka fa a cikin ha a baki. Murmushi ya sake sakar musu da cewa, Masha ALLAH . Daga haka ya mi e yana ajiye kofin da sauran shayi a inda ya auka. Sai Maanal ta samu kanta da tsurama kofin ido kawai har yay sallama dasu Oum ya fita kafin ta farga. Yaya Fawzan ne ya katseta. Kayan shayin ya tura gabanta yana fa in, a wani shayin tunda ya shanye miki kinji Lilly an murmushin ya e Maanal tayi, cikin muryar nan tata mai sanyi ta ce, Yaya akwai a ciki ya isheni Kin tabbatar? Kanta ta jinjina masa. Oum dai Murmushin ta take irin na manya batace komai ba. Sun kammala breakfast in babu jimawa sai ga RK. Da gudu su Haneeff suka ma alesa suna murna. Hakan yasa Oum sake fahimtar akwai sha uwa sosai tsakaninsa da yaran. Fawzan ma har yanzu yana a sashen Oum in suna hira, sai kawai RK in ya baje aka dora da shi bayan mai aiki ta ha o masa breakfast dan yace bai karya ba. Anan falon ya karya suna hirar, idonsa akan Maanal dake kwance kanta a cinyar Oum tana karatun novel in nata na fama. Sai ara jinjina sha uwar Oum in yake da Maanal in, dan kuwa yanda Maanal in ta saki jiki ya ishesa shaida. Musamman idan yay dubi da miskilancin tsiya irin na Maanal in.... ____________ Da mamaki Shahidah ke sauraren Linda dake mata bayanin fitar Huznah tun 8. Ranta ne ya fara aci da iskancin Huznah in. Yaya tana a gidanta amma bata da mutuncin da zata dinga gaya mata zata fita. Kai ko gaisuwa tunda Huznah tazo gidan nan bata jin ta mata. Shi kansa Abbansu Barrah duk kawaicinsa yau da safe sai da yay magana. Shine ma dalilin da yasa yanzu da zasuyi zaman breakfast taima Linda magana akan ta tado Huznah in su karya. Amma sai take sanar mata wai ta fita tun 8. Da alama kuma anguwa ta tafi dan taci gayu. Komai batace da Linda in ba ta juya tabar dining in. Bedroom in ta ta shiga ta au waya tayi kiran Ammie. A lokacin Ammie na tare da Daddy dan yau itace da shi. Bata aga kiran ba har ya tsinke. Cikin hikima tacema Daddy tana zuwa dan wayar tata dama a silent take. Sashenta ta koma sannan tai kiran Shahidah in. Bayan ta amsa gaisuwar da Shahidahn ke mata ta ce, Mike faruwa da safen nan kira Shahidah? Cikin matu acin murya Shahidah ta ce, Ammie akan yarinyar nan ne Huznah. Nifa gaskiya ina jin tsoro. Tunda tazo fa ba zama take ba, da mun fita aiki take shiryawa itama ta fice gidan nan wani lokacin ma sai mu rigata dawowa. Yau kuma da take weekend ma kinji tun 8 tabar gidan nan. Ammie ina jin tsoron kar wani abu ya faru ace a zamanta nan ne ban saka ido a kanta ba fa Numfashi mai nauyi Ammie ta sauke. Cike da nazarin maganganun Shahidah in ta ce, Kenan akwai dai abinda tazo yi Abujan, saboda uban ya barta suka jinginata da zuwa gidanki ta zauna. Ki kwantar da hankalinki in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Zuwa anjima zan kira Yazeed nai masa bayani ya sanya ido a kanta tunda yana Abujar. Ajiyar zuciya Shahidah ta sauke cike da gamsuwa tace, Yauwa Ammie hakan dai yafi kam gaskiya. Dan shi ka ai ne maganinta nikam bajin maganata zatai ba tana ganin shekarunmu aya. Yasu Hameed da Aunty Sakina Lafiyarsu alau gaba aya. Ya batun dubiyar da su Auta sukaje jiyan? Gaban Shahidah ne ya fa i, amma sai cikin wayancewa ta ce, Lafiya lau Ammie babu wata damuwa. Dan yanzu haka ma barci takeyi To Alhamdullah, dan inata tunanin kar taje gidan mutane ta nuna bata son yaronsu. Ni kuma harga ALLAH yaron ya shiga raina saboda nutsuwarsa da sanin darajar mutane. Tunda al'amarin Yazeed ya koma wani iri gara ta ha ura da Rafeeq in ayi a wuce wajen zaman nan nata damuna yake yi Ammie adai cigaba da addu'a, in sha ALLAHU komai zai dai-daita, nawa ma Maanal in take, rigimarta ce ta sata gama karatu da da wuri amma da yanzu ne fa ma ya kamata ta shiga jami'a. Rafeeq kam baida matsala mutumin kirki ne. Ya cancanta ai masa komai, kuma sun dace da Maanal in. Sai dai nasan akwai rikici Ammie..... Rikicin mi kuma? Wani abu ya faru ne? A'a babu abinda ya faru Ammie. Kawai nasan janyewar Yazeed akan Maanal bazai kasance mai sau i ba. Dan yana matu ar sonta, auren nan dan baida yanda zai yi ne kawai uwarsa tafi arfinsa ne. Yanzu haka kullum cikin ro on Maanal yake akan ta bari a ha a bikin ayi gaba aya zaifi samun kwanciyar hankali. Ni wlhy duk sai ma tausayinsa ya fara damuna Nima ina jin tausayin nasa Shahidah. Sai dai su ha ura da junan sai yafi alkairi fiye da yin, dan nasan wacece Hajiya Sadiyya. Komai zata iya yi kamar yanda ta fa a. ALLAH dai ya kawo mafita cikin sau i. Bari anjima mayi wayar na bar babanku shi ka ai ina wajensa kika kira To Ammie ba damuwa sai anjima ........... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .........A angaren Huznah tana can