Sashe 63
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da kasancewa asa- asa tamkar ba namiji ba ya furta, Mi kike bu ata? Kai! Kai nake bu ata AA. Ina son yin magana da kai Please Lips insa ya an ciza sai kuma ya janye idanunsa daga kanta. arin wucewa yay batare daya tanka mata ba yana kallon Designer agogonsa da sai ka gama kara ewa baka samo sa ba, dan shi duk wani agogon sakawarsa ana masa shi a companynsa kuma shi ka ai, sai idan wani ne yace yana so ayi irinsa daga nan shi kuma yabar saka Design in sai kuma wani. Da sauri ta bi bayansa suka shige cikin elevator daya bu e. Anan in ma dubansa tayi da son yin magana sai dai ta gagara sakamakon ganin fuskarsa babu alamun wasa. A haka suka fito tanata arin ganin ta daidaita tafiyarsu. Aiko hakan yaja hankalin ma'aikatansa matu a. Dan duk inda suka gitta idanu yuuu akansu. Masu us nayi masu jinjina kai nayi. Yayinda zukatan mafi yawansu suka sake yarda da eh lallai da gaske itace boss in nasu zai aura kuwa. Dan abune da basu ta a gani ba boss da mace kamar haka. Ina dai ka gansu da wata to lallai abokiyar kasuwanci ce, dan shi hatta a cikin family baya kula ar kowa, in dai kina sama da shi zai yi respecting inki. Suna gama ficewa sai in ya aru, yayinda wasu suka maida hankalinsu ga hotunan dake akowacce kusurwa ta Company in na mace mai ni ab da hijjab. Wadda da yawansu sun gagara tantance hoto ne ko zane ne. So suke su tantance ko wadda suka fita taren ce. Sai dai sam babu wani alamu ko kamanni daya nuna hakan. Dan baka isa tantance ainahin wacece a hoton ba tako ina.... Yana fitowa drivern sa dake can wajen securitys suna hira ya mi e da sauri. Sai dai koda ya iso garesa sai ya mi a masa hannu murya asa- asa yana fa in, Don't worry, give me the key, I want to drive myself Babu musu driver ya rissina ya mi a masa key in. Sai kuma ya bu e masa motar da sauri. Ka sama mata taxi Ya sake fa a yana arin shiga motar, kallon Huznah driver yayi, sai kuma ya amsa da sauri cike da girmamawa. Huznah kam dake tsaye kamar zata saki kuka kallonsu kawai takeyi, tana ji tana gani a gabanta ya birka motarsa ya fice cike da warewar iya tu i na nutsuwa da cikar kamala.... Lallai yau taga madarar wula anci da babu ko gauraye a cikinta, wato mutumin nan cikin ruwan sanyi yake tsula maka tsiya babu hayaniya babu hargowa ko yawan magana. Dole ne ta koma Kaduna su sake shiri kam, amma zata fara bari ta ha u da mahaifiyar tasa dan taga yaya nata takun itama, hakan zai sa susan irin shirin da zasu musu su duka.. da wannan tunanin ta ballama drivern harara ta fice da afarta..... Maanal ta jima a wajen tana kuka, sai da ta fara jin zuciyarta na mata nauyi a cikin irjinta kafin ta ago kanta da yar, office chair insa ta zubama ido sosai tamkar shine a wajen, har yanzu hawayen na cigaba da ziraro mata. Tunanin dake neman tasiri a ranta ta ture da arfin tsiya tare da mi ewa ta nufi restroom in kamar yanda ya fa a, dan itama tasan ko giyar wake tasha bazata fita a haka ba ai. Sosai restroom in ya ha u, gashi al sai amshi yake zubawa kamar ba toilet ba. Ta jima tsaye tana kallon kanta a mirror in bayin tana hawaye kafin ta wanke fuskar tata ta fito bayan ta gogeta da aramin towel fari tas dake a bayin. Harta nufi ofa ta koma da baya, shopping bag in daya ajiye a gabanta ta auka kasancewar ganin abinda ya rubuta a takardar daya ajiye a sama, sai kuma ta maida ta ajiye. Nan ma ta juya zata tafi idonta suka sake sauka a novel in nan nasa. Baki ta tura gaba sannan ta auka shi dai ta ficewarta.. Koda ta fito bata kula kowa ba a wajen ta shiga ha an tarkacen kayanta, kallonta kawai su Zaharadeen suke cike da gulma. Sai Yaqub ne daya mi e tsaye yana kallonta tun shigowarta ya furta, Sister Maanal are you okay? Kanta kawai ta jinjina masa batare da dace komai ba. Kafin ya samu damar sake magana ta kwashi kayanta zata wuce. Cikin sauri ya bita yana fa in, Ina zaki je? Gida Ta bashi amsa a takaice. Cikin tashin hankali ya bu e baki zai sake magana a fusace ta ce, Please Yakub! Nace ba komai. Leave me alone . Daga haka tai gaba abinta fuuuu. Shiru yay kawai yana kallonta, gaba aya fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa da tashin hankali. Shin mike faruwa? Mi akai mata? A office na CEO fa aka kirata! Miya faru acan . Rashin mai bashi amsa ya sashi juyawa jiki a sanyaye ya koma ciki. Sai kuma ya sake tadda wani abun takaicin, su Zaharadeen ne suke bu e babin gulmar Maanal in. Wai maybe ta fa ama CEO tana sonshi ne shine ya koreta a aiki, sai ALLAH ya ara suke mata da kiranta mai girman kai da fa in rai. Takaicinsu ya saka Yakub ko kulasu baiyi ba...... ______________ Alhamdullahi ranka ya da e aiki ya kammala. Wannan shine cikakken bayani akan ainahin mahaifinta dama zuri'arta baki . Rabilu ne mai maganar fuskarsa washe da murmushi yana mi ama Sen.. Bukar bayani akan Maanaal daya binciko kamar yanda ya bu ata. Sosai fuskar sa ta washe da murmushi. Dan shi ka ai yasan yanda yake azabtuwa da so da aunar yarinyar nan data mamaye dukkan illahirin jinin jikinsa. Yanzu haka yau har gaban Mawaad company yasa drivern sa yaje ya faka mota har Maanal ta iso. Fitarta a motar Shahidah da dukkan abinda ya faru a wajen kan idonsa ne. Ji ya dingayi kamar ya sato ta saboda yanda tai matu yawu a cikin kwalliyar ta yau. Rabilu ya cigaba da fa in, in asalin su an jihar Kebbi ne, aramar hukumar suru a wani auye da ake kira giro. Mahaifin nata an sanda ne, dan har ya kai matakin DPO amma yanzu ya ajiye aiki sakamakon doguwar jiyyar da yayi. Ita kuma mahaifiyarta bata tare da shi a yanzu, dan sun rabu shekaru kusan takwas kenan, a yanzu haka tana auren wani Alhaji Usman Chalawa ne anan kaduna, yana ri e da su kuma tamkar mahaifin nasu koma fiye da shi. Cike da zumu i ya furta, Rabilu kaje wajen Oler ka amshi key in motar ka sabuwa dal, zuwa dare zan nemeka idan na koma gida Cikin matu ar washe baki Rabilu ya shiga godiya harda an zamowa daga visitors chair da yake zaune ta office in Sen.. Aifa cike da zumu i ya bar office in. Kai tsaye gidan Sen.. Bukar ya nufa domin amsar al awarinsa dan yasan baya magana biyu akan alkawari irin wannan daya shafi mata. Zai iya cewa dukan matan alhajin idan ka cire uwargidansa duk shine ya masa bincike akan sauran biyun. Ya kuma taka rawar gani akan samuwar auren fiye da zaton mai zato. Sai dai ya fahimci kamar Senator in yafi sakin ku i da oki akan wannan ar shilar. To ar shila mana. Akan matan Alhaji ai manaal ar shila ce. Dan ko jikansa na farko ya girmi Maanal sosai. Aiko ina sha ALLAHU zai yi iya arinsa dan ganin tako ina Alhaji bai samu matsala ba, ya kuma mallaki yarinyar da gaggawa. Dan yasan irin wannan kari ujin arzi in da ire-irensa sunta zuwa kenan. Zama kuwa ai ba nashi bane ba.... ____________ Cike da nutsuwa Daddy ke kallon Yazeed. Yayinda shi kuma kansa ke du e a asa rauninsa na sake bayyana akan fuskarsa. Karo na farko Daddy ya an saki murmushi, yayinda tausayin yaron nasa ke ratsa masa zuciya. Ya jima da fahimtar tsananin so da Yazeed kema Maanal, sai dai bai sake tabbatarwa ba sai a an tsakanin nan. Musamman yau da yazo masa da ro o da magiyar janye batun sai nan da wata biyar ayi aurensa da Manaal. So yake a ha esa gaba aya anan da sati biyun daya rage shi da Nazeefa. Gyaran murya yay da gyara zamansa. Hakan yasa Yazeed agowa ya an kallesa. Yazeed kasan dai ina bayanka nima ari bisa ari akan zancenka da Maanal. Sai dai ina son kamar yanda su Baba Kalla suka fa a wannan karon naje da kaina da baba nema maka aurenta ga mahaifinta. Hakan shine zai bada salama game da tujarar mahaifiyarka akan al'amarin Daddy nima na yarda da hakan, amma dan ALLAH ina sake neman alfarmar ha ewar gaba aya. Nasan ko'a cikin satin nan zaku iya zuwa ga mahaifin nata, idan kuma ka amince min ni saina fara zuwa na ganshi an jimmm Daddy yayi, sai kuma ya shiga jinjina kansa. Shike nan na yarda da zancen naka in sha ALLAHU za'a ha e bikin nan da sati biyun, zan samu Baba da batun shima sai mu saka ranar zuwa muga mahaifin nata, kai ka tsahirta sai bayan mun dawo in. Kadai je ka cigaba da shirinka na zama angon mata biyu a rana asa Yazeed yay da idanunsa wani murmushi na su uce masa. Yayinda zuciyarsa ke wani irin washewa da farin ciki mara misaltawa. Ji yake kamar an masa gafarar zunubansa. Yana fitowa ya shiga neman layin Maanal dan yay mata albishir, sai dai bata shiga ba. Duk da yasan yanzu tana office kasa ha uri yayi ya shiga neman Shahidah. Bayan sun gaisa yake tambayarta Maanal fa. Cikin girmamawa ta sanar masa har yau ba'a dawo mata da wayarta data samu matsala ba ne, amma tana yautata zaton yau za'a kawo mata, sai dai idan ta tashi zata ha asu..... ___________ Shiru kawai Ammie tai tana kallo Daddy dake mata bayanin sabon hukuncin daya sake yankewa akan dawo da zancen bikin Maanal da Yazeed anan da sati uku. Za'a ha aurin auren kawai idan ma bikin Maanal in ne za'a aga nan da zuwa ko wata aya ne idan ita bata shirya ba to. Sai kuma batun zuwa ga dangin mahaifinta kamar