← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 104

Sashe 77

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ke tsakanin Rafeeq da su Ajwaad. Ni wlhy nama rasa wane tunani zanyi. Dan tabbas akwai ura babba. Anzo ga ar fa da dole Ammie tasan halin da ake ciki kin san dai Auta da taurin kai da kafiyar tsiya Amma kin san zamusha fa a akan oye matan da mukai. Sannan na fa a miki jiya naje gidan na samu Daddy na shirin zuwa Kebbi domin ganawa da wa an can mutanen na Giro. Na tabbatar kuma yau in nan sun tafi ma shiyyasa nake ta nemanki tun safe. Yanzu haka can gidan zanje dan Hameed ya kirani ya sanar min Ammie na ciwon kai yau gaba aya a kwance ta yini kuma yaga Daddy ya fita daga wajenta da safe kamar a fusace. Kinga ko ya tabbata akan zuwa Giro in ne maybe ta nuna bata so ko Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un Amaal komai zai iya faruwa kam. Wannan wace irin ga a ce mai rikitarwa da tada hankali. Aiko muma bamuga ta zama ba dole na auka hutu Kona kwana hu u ne muzo Kadunan gobe idan ALLAH ya kaimu. Daga nan kawai har biki To gaskiya hakan ne ya kamata kawai ku taho. Bara naje naga halin da Ammien ke ciki Jiki a sanyaye Shahidah ta amsa ta da to kawai suka yanke kiran. Bata le a Maanal ba sai bayan sallar magriba, ta sameta tana karatun Alkur'ani. Zama tai dan haka Maanal tana kaiwa inda ya kamata ta tsaya ta dakata. Duban Shahidah tayi da da fa in, Didi kina son wani abu ne? A'a Auta, ina Huznah take? Sai da Maanal ta an ta e baki sannan tace, Naga Yaseerah ta kiranta yanzun nan ta saka hijjab ina ta fita a rikice. Ban san mita gaya mata ba amma da alama Yaseerahn na wajen gidan nan ma dan naji tana cemata gata nan zuwa ba sai ta shigo ba Kai kawai Shahidahn ta girgiza da fa in, To ALLAH ya yauta. Dama zance miki ne inaga gobe in sha ALLAHU zamu wuce kadunan gaba Didi aikinki fa? Wani abu ya faru ne? Babu damuwa zanma Abban Barrah magana ya nema min hutu na kwana hu u tunda oga na abokinsa ne. Kinga idan biki ya tashi sai mu taho gaba aya kawai Magana Maanal taso yi, sai kuma ta ce, Okay ALLAH ya kaimu to ...... _____________ angaren AA kam shima bayan wucewar su Maanal ya matsa aka sallamesa. RK yaso in yin hakan amma ina. Ganin yana neman birkice musu Oum tace yasa a sallame san kawai. Sun iso gida Mamy da Abah na shirin zuwa asibitin dubashi. Dan shi Abah yau yaje gidan gwamnati tunda safe sakamakon kiran daya samu daga mataimakin shugaban asa. Ita kuma Mamy ta fita dan ko kai AA in asibiti bata san anyi ba sai da ta dawo ko sashenta bata shiga ba taci karo da Abah ya fito zaije asibitin. Shine yace ta juya suje dan yasan halinta zata iya in zuwa saboda kawaici. Bata ce masa komai ba suka nufi motarta data ajiye yanzu, dai-dai nan kuma sai ga an asibitin ma. Sai kawai suka rungu a zuwa sashen Oum dan AA yace shi can zaije baya son sashensa. Can in kuwa aka nufa da shi har akin Oum. Anan suka zagaye sa cike da kulawa da tsantsar soyayyar da kowa ke masa a gidan.... Abdul-hakeem mijin Yaseerah yazo gidan kawoma Mamy sa o data manto a wajen mamansa shi kuma yaje gidan ta bashi ya biyo Mamyn dashi ya samu batun ciwon AA in bai sauka ba da har yau ya kaisa ga zuwa asibiti. Shine ya kira matarsa Yaseerah yace tazo itama ta duba shi sai su koma gidan tare. Ita kuma ta kira Huznah ta kuma biya ta akkota a gidan Shahidah kamar yanda mijin nata ya bata umarni. Koda suka shigo kai tsaye sashen Oum suka nufa dan har lokacin itama Mamy na acan dama duka an gidan har su Saheeba da Nibras da Nuratu. Mai aikin Oum Mamy ta saka shigowa da su Abdul in har falon sama na Oum. Duk suna a falo, idan ka cire AA dake can bedroom in Oum da yay barci. Sai Babban Yaya da bai dawo gidan ba tun baro asibiti da yay azun. Nibras da Nuratu na'a falon asa suna girki. Nuratu ce ta fara cewa zata girka ma AA abinci kamar yanda uwarsu da suka kira suna gaya mata abinda ya faru a asibiti ta basu shawarar yi. Sai ita kuma Nibras ta ce itama zatayi dan wani irin tsanar Nuratu take ji tuni batun yanzu ba. Abinda ma ke an sassauta mata inta ganin yanda shi AA in baya wani shiga sabgarta. Itama dai taci kuka bayan dawowar tasu daga koro sun da akayi daga asibiti. A hakan ma ba wani tarihin Maanal ta sani cikakke ba game da ala arta da AA, amma ta auki aniyar bugar cikin Fawzan ta sani yau dan tasan irin matakin da zata auka akan Maanal in da dukan ahalinta ma. Dan itafa a yanda take jin AA a ranta ALLAH ko mahaifansa da su Fawzan zata iya kawarwa ta mallakesa ita ka Su Huznah sun hawo Nibras da Nuratu dake a kitchen basu sani ba. Sai da har su Abdull sun gama gaishe da Abah da Mamy da Oum Abah na tsokanar Abdull sannan suke haurowa da kayan abincin da suka shirya harda mai aikin Oum. Sannu Oum da Mamy ke musu, duk suka amsa tare da tambayar Mamy ina za'a kai masa abincin. D/table Mamy tace su ajiye. Dan haka duk suka ajiye a can in. Juyowar nan da Nuratu zatai tana magana da Abdull sai idanunta uru- uru a cikin na Huznah da tun shigowar Nuratu falon mamaki da ru ani suka baibayeta. Cikin kuwa an waro ido na nuna mamaki Nuratu ta ce, Kai wai wa nake gani kamar Huznah? Murmushin arfin hali Huznah in tayi, sai kuma ta sinne kai asa wai ita kunyar surukai na wajen ta ce, Nice Nurry Idanu Yaseerah da Abdul-hakeem suka ha a. Yayinda Mamy ta saki wani murmushin jin da in ganin Nuratu da Huznah ma kenan sun san juna. Dan haka sai kawai ta mi e tana fa in, Kunga muje can kafin Maman an nan tace zamu hana mata shi barci Dariya Oum tayi dan sanin da ita Mamy take. Oh abun ma harda ar sharri. To shike nan kuje in dai dan kuwa ban san a tada shin Mamy ma dariyar ta sake yi. Ai nasan gaskiya na fa Shima Abah dariya yaketa musu. Haka Mamy ta fice tare da su Huznah. Nuratu ma tai wuff ta bi bayansu. Suna gama fitowa daga apartment in Oum in caraf Nuratu ta ri o hannun Huznah dake kusan arshe. Cak Huznah ta tsaya, sai kuma ta juyo tana kallon Nuratu. Murmushi ta sakar mata da fa in, Oh oh friend ashe kece? ALLAH duk kin saka mamaki yama rufe ni da ganinki gidan nan kodai gidanku ne? Nuratu da zuciyarta keta watsal-watsal a irji ta ce, Eh gidanmu ne. Amma ba inda aka haifan ba. Gidan da zanyi aure kenan, kuma wanda zan aura in ma kuka zo dubawa. A ina kika san Abdul-hakeem? Tsabar yanda zuciyar Huznah tai wata girgiza har taurari ta dinga gani na mata yawo a cikin ido. Cikin rawar baki ta ce, Waye zaki aura Cike da gadara da alfahari Nuratu ta bata amsa da, Ajwaad Aliyu Abubakar Darma, wato AA Darma Ai zabura gefe Huznah tayi tana mai fisge hannunta daga cikin na Nuratu, sai ko gata jikin bango kamar mage ta gamu da kare a kwanar da babu hanyar illewa. Yanda tai in ya saka Nuratu kafeta da ido itama zuciyarta na wantsalawa a karo na biyu. Sai kuma ta matsa gaban Huznah tana fa in, K jira-jira wai badai dama Yaya AA kike bibiya ba?. Babbar bala'i wai dama shine kika bamu labari? . Bata jira amsar Huznah ba tai saurin fara danna wayarta ta latso hoton AA dake cikin wani lallausan farin yadi da yay masa shegen yau ta nuna mata. Shine wannan? Jinjina mata kai Huznah tayi a mutu ar harmutse. Kambu are you mad? Wai dama mijin aurena kike bibiya. Ehhhh ahhh lallai kin taro match yarinyar nan. Yau naga ba ar shegiya ubanwa ya aiko ki? . Tai maganar da nufar Huznah gadan-gadan tana neman kai mata hannu ta sha ota. Hannun nata Huznahr ta ri e caraf, a dai-dai nan Fawzan ya iso wajen. Kai kai kai lafiya?!! Ya fa a cikin daka tsawa. Dan shima abinda Nuratun tayi a asibiti har yanzu haushin bai bar ransa ba. Dakatawa Nuratu tai daga shirin sha e Huznah. Sai dai cikin wani irin ihu da hargowa ta ce, Yaya Fawzan wai har wannan tsinanniyar ce zatace tana son Yaya AA. Son shi take amma tazo ta ra u da jikina inata bata shawarar yanda zata sameshi. Ni wannan ar iskar zata maida bahuwa. Na rantse da ALLAH yau saina ha a miki jini da majina ta yanda bazaki ta a sake sha'awar yima kowa wacen saurayi ba dan ........ ta arasa da ashariya mai girman gaske tana sake zaburowa kan Huznah. Cikin anin lokaci rikici ya har ume a tsakaninsu da hayaniyar ta saka su Mamy fitowa. Hakama Oum sai gata da Abah harda masu aiki duk sun yo waje. Itama Nibras da Saheeba haka. Wani irin jan faratunnan arin da Nuratu tayi a hannunta tai a saman fuskar Huznah,tun daga wajen kunnenta har zuwa bakinta. ara Huznah ta saki na azaba tana mai dafe fuskarta da duka hannuwan biyu jikinta na rawa. Aiko cikin tashin hankali Mamy da Oum sukai kan Huznah in, ita kuma Saheeba ta ri e Nuratu. Mugun ciwo Nuratu taima Huznah , dan yanda kasan tsagar yarbawa irin na farkon arnin nan haka suka kasance har sanda hu u na yatsunta. Jini tuni ya ji e wajen abinka da farar fata jiki kuma babu wahala. Ai Fawzan baima san ya kwashe fuskar Nuratu da mari ba. Yana arin sake kai mata wani Abah ya ri e hannunsa yana mai girgiza masa kai. Kuka Huznah take sosai na azaba, hakama Nuratu kukan marin da Fawzan ya mata take yi.
Chapter 77 · 0% Book details