← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 104

Sashe 22

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

auke kansa ya basar. Ita kuma taja aramin tsaki ta ida hayewa. Daga haka bata sake sanin sanda yabar gidan ba. Dan wanka ta samu tayi a akin Shahidah tai kwanciyarta sai barci. Dama sunce zata dinga samun isashen barci yanzu hakan ne zai dawo da kuzarinta data rasa... Bayan sallar la'asar Nene dasu Amaal suka wuce. Sai suka koma daga ita sai Shahidah da mijinta da yaranta biyu a gidan kawai. Sai kuma masu aikinta guda biyu. Jitai kuma duk babu da i, dan tana matu ar son ta gansu su duka a waje aya hakan na sakata a farin ciki. Sai dai yaya ta iya aure ya rarrabasu. Hira suke da Shahidah, koma ace Shahidah ke hiran dan Maanal dai daga guntun murmushi sai eh ko a'a ne nata. Muneff ne ya shigo da an gudunsa, autan Shahidah, dan daga shi dai har yanzu bata sake ba ko tana hutawane ko ta tsaya oho mata. Muneff ban hanaka wannan guje-gujen ba wai nikam? Shahidah ta fa a cikin taka masa birki. Yaron bai damu ba ya ce, Mamy Uncle Yazeed ne yazo Uncle Yazeed na kd? Eh Mamy. Yana waje ma Kallon Maanal Shahidah tayi. Itama Maanal in ita take kallo. Kije ki shigo da shi Ni Didi afata ke ciwo Kai kawai Shahidah ta girgiza tana mi ewa. Hijjab inta da takan ajiye a falo saboda ba i irin haka ta auka ta saka sannan ta fita. Babu wani jimawa sai gata ta dawo Yazeed biye da ita. Yana shigowa idonsa akan Maanal ya fara sauka. Itako ta urama television ido kamar bata san da shigowar tasa ba......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama .......Sai da suka gama gaisawa da Shahidah sannan ta an kallesa ta ce, Yaya Yazeed ina yini Sai da yaja kusan minti aya kafin ya amsa da, Lafiya lau. Yaya jikin naki? Alhamdullahi Masha ALLAH . Ya fa a yana maida kallonsa ga Shahidah. Shine aka sallameku Shahidah ban sani ba. Sai da naje asibitin yanzu akace kuna gida Kayi ha uri Yaya Yazeed anyi kuskure kam. Amma banyi tunanin zaka dawo yau bane, azatona kuma kasan da sallamar ne ma wlhy. Tunda muma munje kai musu breakfast Nene ke sanar mana ai doctor yace zai sallemeta yau, da daddare yake sanar musu. ALLAH ya ara lafiya to, ya kuma kiyaye gaba. Ina su Nenen? Nene ai yanzu na tabbata suna gab da shiga Kaduna. Mijin Amal ne ya wuce dasu gaba Kai da sauri haka?. Ita Nene ko an hutawa bazatayi ba Aikam bazata zauna ba. A hakama dan zaman asibiti ne. Yau kam muna dawowa tace bafa zata sake kwana a garin nan ba Murmushi kawai yay da fa in, Shike nan zan sameta har gida ai. To kema sai ki shirya mu wuce da safe ko, tunda yanzu yamma dai tayi kam . Ya are maganar idonsa akan Maanal. Ni Ammie tace ai na zauna anan Anan kuma? To saboda mi? Shahidah ce ta bashi amsa da, Bana zaton wani abune gaskiya. Inaga dai tana son ta ara murmurewa ne dan suma likitocin sunyi garga i sosai akan ta huta a waje mai arancin jama'a da hayaniya. Amma tana ara murmurewa zata dawo Yaya Yazeed Badan ya gamsu da bayanin Shahidahn ba ya ce, Okay shike nan ALLAH yasa kaffara ne. Nima dai ina nan Abujan har zuwa jibi in sha ALLAHU, dan akwai abinda zanyi ALLAH ya taimaka ya bada nasara . Shahidah ta fa a cike da girmamawa. Dan suna matu ar giramam yazeed, koba komai suma yana girmama musu Ammien su. Su kansu yana mutuntasu, dan bazasuce ya ta a musu wani abu na ashsha ba tun daga zamansu gidansu har zuwa aurensu. Hasalima a auren nasu ya zame musu tamkar babban yaya ne a komai. Tashi tai ta bar musu falon. Hakan yasa shi tashi ya koma kujerar kusa da Maanal shima. Cike da kulawa murya can asa ya ce, Baki jin komai dai zuwa yanzu? Kanta ta jinjina masa alamar eh. Alhamdullahi haka ake so ai. Nasan kece kikacema Ammie baki son komawa KD ko? Cikin marairaice fuska kamar zatai kuka ta ce, Ni ALLAH babu ruwana. Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya an murmusa tare da du o da kansa ka an murya asa- asa ya furta, Adana shagwa ar nan ba yanzu ba Kanta ta du ar ziciyarta na gudu da sauri-sauri a irjinta kamar zata fito waje. Sai kuma ta yun ura zata tashi. Cikin bada umarni ya ce, Koma ki zauna . Babu yanda ta iya dole ta koma ta zauna in tana ata fuska.... _______________ Da alama wannan karon mijinki yana son nai matu ar cin mutuncinsa Sadiyya. Ki taho gida tsahon kwanaki goma amma bai biyo bayanki ba saboda yana son nuna min iyakata. Ban san yaushe Usman ya fara maida kansa sakarai a gidansa ba. Ace mace ke juyaka yarinya arama Hawaye Hajiya Yaya ta sake matsowa tare da du ar da kai kamar ta ALLAH. Muryarta na rawa ta ce, Baba wlhy yamafi yanda kake zatonsa a yanzu. Ni shiyyasa ma nace kawai kasashi ya sakeni na gaji da wannan zaman uncin, ai ba haka mukai da shi ba. Shi da kansa yace min duk macen da zai kawo gidan nan sai dai ta kasance a ashin ikona da umarnina. Amma duk ya manta da wannan al awuran da girmana agaban ana da matansa yake tozartani. Wai har yake iya gaya min sai dai matarsa idan ta juya naga bayanta amma ba'a zaman gidansa ba, wai ni Usman ke tarema mace fa a a gabana Baba . Ta fashe da kuka. Kinga ya isa kukan haka kinji, barni da shi ai nasan maganinsa. Shi kuma Yazeedu daketa kai kawon ki koma saboda baida kishin uwarsa shima zan gyara masa zama. Share hawayenki abinki zakiga matakin dazan auka jeki kwanta Kai Hajiya Yaya ta jinjina tana mi ewa hannunta a saman ido tana share hawaye kamar wadda akacema baban ne ya mutu. Sai d a ta gama ficewa mahaifiyarta dake zaune a falon bata tofa ko a ba a maganar tasu ta nisa a hankali. Tsohuwar kirki mara yawan son hayaniya kenan. Idanunta akan Baba ta ce, Nikam da zakaji shawarata dattijo da baka goya bayan Sadiyya ba a wannan karon. Kai kanka kasan halin yarinyar nan sarai da abinda zata iya. Tunda kaga kuma Usman ya watsar da ita a wannan karon wlhy ba banza ba. Dan haka ka kirashi cikin dattako ka zaunar dasu su duka kaji bakin kowa. Idan ta kama ma can gidan nasa zakaje ka tasata gaba ka ha asu har abokan zaman nata. Karfa dan ka raini Usman ya zama kana tauye masa hakki akan ar da ka haifa. Ai ke kinji matsalarki, idan har abu zai taso akan yaran nan sai kin nuna ban iya ba ke sarkin tawakkali da gaskiya ko Ba haka bane Dattijo. Masu iya maganafa sunce kaso naka duniya ta isa, ka isa duniya ta soshi. Usman na maka matu ar biyyar da kosu an da ka haifa ba kowa ke maka irinta ba. To bai kamata a cigaba da antar da shi ba akan abinda ya isa da shi. Wannan fa rayuwar aurensu ce. Kuma shine shugaba a gidan, yin kutse a al'amarin kamar antar da shi ne. Dan ALLAH kada ka biyema yaran nan ana ganin ka da kima da mutunci irin na uba kuma shugaba Shiru yay na kusan minti biyu, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. Hakane kuma Adama nagode da tunatarwa. In sha ALLAHU gobe zan tasata gaba muje gidan. Sai dai ance min shi Usman in baya asar, amma dai inada tabbacin kamar yau ne da dare zai dawo To Alhmdllh gobe idan ALLAH ya kaimu in sai kuje, ALLAH ya ta aita al'amarin kuma ya daidaita su
Chapter 22 · 0% Book details