← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 104

Sashe 12

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

da mintuna biyu ba, kafin Maanal ta gama tattaro abinda ya dun ule mata nunfashi Najma da Amra suka dawo. Rungumeta Najma tai tana farin ciki wai zata zama matar Uncle inta. Surutanta take amma ita Maanal sam bata wani fahimtar komai.... _____________ Wai nikam lafiya duk kin zama wata sukuku ko duk gajiyar bikin ce haka Auta? Didi Shahidah ce mai maganar tana zama kusa da Manaal dake kwance a doguwar kujera idanunta a lumshe. Tunda suka shigo gidan ta zube a wajen tana bitar abinda ya faru a Zaria. aramin murmushi ta sakar ma ar uwar tata. Sai kuma ta yun ura ta tashi zaune sosai. Babu komai Didi. Kawai na kwanta ne dai Murmushi Didin tai mata, sai kuma ta kai hannu ta an shafi fuskarta. Auta gyaran jikin nan na amsarki sosai. Idan kika yosa duk sai ki canja kamar wata amarya dake Da sauri Maanal ta ata fuska. Zatai magana aka buga ofar falon da arfi har duk sai da suka razana. Hajiya Yaya ce sai yaranta biyu biye da ita. Cikin hargagi da masifa ta shiga wala kiran ainahin sunan Ammie. Duk mi ewa sukayi, dan yanda take a birkice zakasan babu lafiya. Ita kanta Ammie da sauri ta fito ankwalinta a hannu. Ya salam Hajiya miya faru? . Ammien ta fa a tana arasowa cikin falon da sassarfa. Oh tambayata ma kike miya faru? Wai Asiya nikam kodai ke kika haifar min Yazeed a gidan nan ne? A hankali Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana mai girgiza kanta. Sai kuma a nutsenta ta bata amsa da Hajiya kiyi hakuri ban san akanmi kike magana ba. Yazeed ai kowa yasan kece kika haifesa To kuwa tunda kin san ni na haifi abina ki fitar min sabgar yaro. Dan wlhy idan ma kina mafarki ne ki farka. Ki kuma je ki sanarma bokanki anan anfi arfinki anfi arfin tsafinsa. Alhajin dai da kika iya mallaka har kika aura kinci nasara, wataran kuma ruwa zai arema an kada shima. Amma Yazeed har gaban abada bazai auri wannan ar taki ba, wancan ya samu ya gudu da yar ko nace uwarsa ta mi e tsaye a kanku shine ni za'a udubar min yaro da tsafi da asiri a ha ashi da sauran ciwo. Kuma wlhy daga yau sai yau, kika sake aukar min yaro ya kaiki anguwa duk abinda nai miki kece kika jashi a gidan nan, mayyar mata kawai....... Haba Mamma nafa miki bayani Daddy ne yace muje ba laifin Ammie bane ba . Yazeed daya shigo falon ya katseta cikin sar ewar murya. Kansa ta juya da masifa kamar zata cinyesa. Harda fa in idan har bai rabu da Maanal ba ALLAH sai ta aga masa mama. Sai kuma ta juyo ga Ammien ta cigaba da mata zagi na rashin mutunci da gori. Gaba aya rayukansu Shahidah sun gama aci, yayinda Amal ta kasa ha uri ta yun ura zata tanka mata Ammie ta hanata. Dole tai shiru. Da gudu Maanal tabar falon kuka mai arfi na wace mata. Hakan yasa Amal bin bayanta itama zuciyarta kamar zata kama da wuta. Sam bata so Ammie ta hanata ba. Amma koba yau ba ta auki alwashin sai ta gogema matar nan abinda ke kanta. Haba wanna abin ya isa haka mana. Tasara miyyasa mutanen nan basu da adalci sam, kowa dai Ammiensu kowa Amminsu sai kace itace ka ai kishiyarsu. Taga dai suma kishiyoyin juna ne, amma basa fitinar juna sai Ammie, shin sai yaushe ne Ammiensu zataji da in rayuwar aurenta?. A gidan mahaifinsu bata zauna lafiya ba, fitinar miji data uwar miji, aka dawo ta kishiya har sai da ta bar musu gidan, yanzu kuma anan ta kishiyoyi har biyu.... Sosai Hajiya Yaya ta diga jidali da tujara wa Ammie kamar ta samu iyarta. Ammien kuma bata tanka ba bata bar anta sun tanka ba. Hakan kuma shine mafi mata ciwo, kai su duka su wannan shirun da Ammien ke musu akoda yaushe na ona musu zuciya da ruhinsu. So da yawa suna mata abu dan ta tanka amma sai ta basar. Da yar Yazeed ya lalla ata ta fita. Suka bar Ammie da su Manaal cikin matsanancin acin rai. Ga Ammie ta hana kowa maganar har dare sashen nasu babu da i. Hakan yasa duk suka kwanta da wuri. Sai can cikin dare Maanal ta bar akinsu da ayanzu yake nata ita ka ai sai idan sauran an uwan nata sunzo gidan ne ta koma na Ammien. Ta sameta tana salla, dan haka itama ta fasa kwanciyar tayo alwala tabi sahunta. Sai da sukai sallar asubahi suka an sake kwanciya Maanal in dai nata daurewa dan bata jin da i...... ____________ Wai Auta bazaki tashi a barcin nan naki ba haka nan. Jibafa lokaci ko kari bakiyi ba, ga an uwanki na jiranki ki rakasu gidan mai gyaran jiki. Suna fara damunki kuma nasan zaki manta da yunwar cikinki ne ku tafi an Maanal ta bu e idanunta ta an kalla Ammie mai maganar ta maida ta lumshe tare da sake na e jikinta waje guda. A yanayin mai barci da yanayin muryarta mai zurfi ta amsa da, Ammie bana jin da . Da sauri Ammie ta ajiye abinda ke hannunta ta nufeta. Zama tai a bakin gadon tare da janye duvet in da take a ciki ta aura hannunta a goshinta, da sauri ta janye ta maida a wuyanta. Ya salam, Manaal kinga tashi muje asibiti jikinki zafi, amma bayan kinyi sallar asubahi ne ma zazza in nan dai? Hannun Ammien ta ri o ta rungume a irjinta. Cikin rauni ta furta, Ammie abinne zai zo, ga kuma irjina yamin nauyi, kwana biyu kenan kullum da safe nake zazza in, shekaran jiya ma da muka taho banda lafiya Sosai rauni da damuwa suka bayyana a fuskar Ammie. Muryarta har rawa yake wajen furta, Yaushe ya dawo yimiki kuma Maanal? Ammie duka watannin nan da banzo gida ba yanayi. Na arshen nan kwanana uku a hospital ma, hakkin ma ji nake kamar zai dawo Ya arrahaman. Amma a watannin nan idan na tambaye ki kuma kita cewa babu damuwa. Haka kika dinga shiga cikin halin nan Manaal amma kina oye min? Shiyyasa tunda naga duk kin sake figewa nasan kin oyemin abubuwa ne. Nikam wannan ciwon naki na tayarmin da hankali, dan ALLAH Maanal ki cirema ranki duk wani abu, itafa rayuwa aya ce, sannan bawa baya kasancewa a cikinta sai da jarabawa dama. Bakiga na ha ura nima na manta komai ba, hakama an uwanki?
Chapter 12 · 0% Book details