← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 104

Sashe 84

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su duka gidan su AA in suka shiga. Tun a ofar falo Maanal ke wala kiran Oum. Sai dai Oum na aki bata amsa ba. Haka ta shigo ta nufi hanyar akinta. Sai dai kafin ta shige sukaci karo da Mamy dake fitowa daga kitchen. Dakatawa Maanal in tayi, tare da fa in, Mamy ina yini Amsa mata Mamyn tayi da kulawa, tare da tambayarta makaranta. Maanal ta ce, Alhamdullah tana wucewa akin Oum. Shima Ajwaad dake biye da Maanal ya gaishe da Mamyn, batare data kallesa ba ta amsa kawai tana wucewa abinta. an Binta yay da kallo, ganin kamar zata juyo sai ya auke kai ya shige akin Oum abinsa. Oum na sallar magriba Maanal baje a gadonta. Ya ajiye bags in nasu yana kallon Maanal in. Malama sallan fa? Ya fa a yana hararanta. Baki ta tura gaba da fa in, Zan huta ne na gaji. An jima ba sai nayi ba Harara ya sake zuba mata, batare da yayi magana ba ya wuce toilet in Oum, alwala ya auro ya fito, gadon ya nufa, inda Maanal ta sake bajewa tana lumshe ido alamar barci ma take son yi. Duka hannayensa biyu yasa ya jawo afafunta iyyyy har arshen gadon, ita kuma ta buga ihu tana kai masa duka da fa in, Ni ka barni ba nace zanyi ba anjima Ko kulata baiyi ba ya direta a tsaye, cike da tsiwa ta dubesa zatai magana ya ce, ALLAH kika sake magana sai na ata miki rai. Wuce alwala konaje na ha aki da Babban Yaya ko Ammie A duniya Maanal na tsoron Babban Yaya da Ammie, dan sune ke cimata aniya a zauna kafiya. Cikin jin haushi ta cire an hijjab inta ta jefa a gadon Oum sannan ta wuce bayi fuuu. Shima ficewarsa yay batare daya sake kulata ba. Koda tayo alwalar kusa da Oum tazo tayi sallar itama... Koda aka idar da sallar shi da Fawzan suka dawo, direct akin Oum suka shigo, sun samu Maanal a saman jikinta kwance tana mata surutu. Fawzan ya gaida Oum, shima Ajwaad haka. Amsawa tai fuskarta da murmushi tana kallon Ajwaad, sai kuma ta kalla Fawzan suka saki murmushi. Ajwaad in na kallonsu, amma bai tanka ba ya zauna kusa da Oum in shima yana akko bag in Maanal na islamiyya. Sai da ya gama fiddo books in duka sannan ya kalla Maanal dake ta surutu wa Oum. Parrot tashi kiyi aikin islamiyya idan anyi isha'i mayi na boko Cikin ata fuska alamar fushi take da shi har yanzu, Tace ni kayi min barci naje ji Ko mutuwa ko? Ya fa a cike da gatse. Tashi Maanal tai zaune idanunta cike da walla tana kallonsa. Sai kuma ta kalla Oum da fa in, Oum kin gansa ko, so yake ma na mutu ya huta ban girma naga ya zama kamar Daddy da Baabu ba Da yar Oum ta danne dariyarta, A'a in sha ALLAHU Auta bazaki mutu ba sai kinga girman Auta ya zama kamar Daddy da Baabu. Yo ina dalili Auta gaskiya ka bari. uruciya tare tsufa tare in sha ALLAHU Dariya Fawzan ya sanya da fa in, Wato Oum soyayyar nan fa na tafiya da ni..... Harararsa Ajwaad yayi, sai kuma ya rufe books in zai tashi Oum tai saurin kama hannunsa ta maida shi ta zaunar tana gumtse dariya. Sai kuma taima Maanal nuni data matsa suyi karatun. arfin dariya Fawzan ya ara tare da mi ewa ya fice yana fa in, In dai nine ma nayi nan. Bara dai naje mu daidaita da Amaal nima kozan samu Besty na Filo Oum ta auka ta jefa masa. Ai ko ya arasa fita a guje. Shi dai Ajwaad bai kulashi ba. Sai aikin da suka fara shi da Maanal na islamiyya. Basu tashi ba kuma sai da aka kira magrib. Ana idarwa ya dawo suka arasa suka fara na boko kuma anan falo. Dan Oum sam bata barinsu su biyu a aki, shiyyasa ma aka saka camara a akinsu duk da ba'a ta a kama ko ayansu da wani halin rashin tarbiyya ba gaskiya.... Da yar Maanal ta bari suka kammala homework in nan. Abinci ma tace ta oshi sai da Oum ta lalla ata ta bata tea. Ai ko tana gamawa ta ingire a jikinta ta hau barci. Sai da barcin yay nisa Ajwaad yazo ya auketa ya kai akin Oum ya kwantar, dan yasan ta gaji in kam, kuma yanda tayi barcin nan duk bala'in dama za'ayi ayi bazata yarda tayi wanka ba. Dama haka take, kusan rayuwarta raba dai-dai ce a tsakanin nan gidan su Ajwaad da can gidansu. Dan ko kayanta a rarrabe suke saboda ko'ina a gidajen biyu tana zama. Wani lokacin sai tai sati bata le a gidansu ba sai kewarta ta ishi Baabu ne ya aiko a kirata sannan. Idan kuma an arzi in na kanta kullum sai taje ta gaida Ammie da Baabu in. Idan kuma aljanun nata suka koma can gidansu kullum zata zo ta gaida Oum ne...... _________ A kwana a tashi asarar mai rai. Yau ga su Maanal da yin graduation na gama primary. Zokaga rawar kai wajan mutuniyar. Balle da taji Oum ta shirya musu party ita da Bestyn nata. Duk da dai shi ya nuna baya so, amma Oum tace babu fashi sai tayi tunda Maanal naso. Babu yanda ya iya dole shima ya sakko aka hau shirye-shirye. Ammie kanta ba son fatin take ba, dan tasan hanyar kashe ku i kawai Oum ta iro ma kanta. Dan koda ta sanarma Babu ma kai tsaye yace shifa gaskiya bai da ku i. Cikin sanyin murya ta ce, Aunty ce fa dama ta shirya musu bawai ku i zaka bayar ba. Naga ya kamata ka sani ne shiyyasa Oh to ALLAH ya taimaka. Dan nima ina da nawa uzirin ne ma shiyyasa. Tunda hutun nan mai tsayine ina son muje gida gaskiya. Gwaggo nata magana akan hakan Wani irin fa uwa gaban Ammie yayi, a take zufa ta shiga tsatstsafoma goshinta. Ganin ya juyo yana kallonta saboda jin tayi shiru tai saurin gyara yanayinta tayi an murmushin ya Kai amma nasan yaran nan zasuyi murna sosai. Musamman ma Maanal da tunda aka baro garin ba'a koma da ita ba shekara kusan shida....... Oh ke baki murna kenan? A'a haba yazance bana murna ni da garinmu. Baka fahimceni bane ba dai Komai bai sake cewa ba sai shigewa toilet ma da yayi dan dama shirin wanka yake yi. Jagwab Ammie takai zaune zuciyarta na wani irin farfashewa a irjinta. Gaba aya jikinta rawa yake. Tabbas ta cancanci tai kewar tushenta, sai dai rasa wani gi i da babban alubalen data baro yasa mata jin tsoro da rashin son zuwa garin. Sai dai tasan ko giyar wake tasha bata isa bijirewa umarnin mijin nata ba kuma an uwanta. Jin motsin zai fito yasa ta mi e da sauri ta fita a akin, tana mai arin danne komai.......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .........Babu bai sake bi takan bikin su Maanal ba, yama maida hankali a shirya musu tafiya gida. Yayinda Ammie taketa arfin halin yin nata shirye-shiryen itama batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ayatar. Anci ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta ingire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a akinta. aukarta tai cak ta maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta. Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye akin Oum Abah ya shigo. Yakai zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce, A'a anan surukar taki tai barci? Dariya Oum tayi tare da fa in, Kaji Aban su da wata magana suruka kuma? Murmushin sa ya sake fa awa shima da fa in, Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban mamaki. Zan so wannan abotar tasu arshenta ya kasance hakan To ALLAH ya za a abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har cikin raina nake jin matu aunar yarinyar nan wlhy Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumu i ba nifa da a yanzu zan aura musu aure kawai Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace, Ayi ha uri dai a barsu sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren fiye da ita Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a azun Baban nasu ke sanar min zasuje gida hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai. Kai masha ALLAH, ai ni har arin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu na an sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji. Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara girma Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano dan tana jin
Chapter 84 · 0% Book details