Sashe 94
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aya suka tashi, shi ya koya mata komai taya dama kike tunanin zaki shiga wannan gidan ki samu farin ciki? Haihuwa da kike ganin bazatayi ba? Humm irin su Alhaji Aliyu Darma da kike gani ba wannan bane a gabansu.... Yaya ni dai naji. Koma minene dai ya riga ya faru ai. Kawai yanzu ina bu atar dawo da yarana hannuna kota arfin tsiya. Musamman Ajwaad. Wlhy yaron nan yi yake tamkar ma bai san muna da ala a ba. Har tayata kishi yake fa. Dan ALLAH ki taimkeni Hummm ai wannan yaron ta adari ne daga gani. Kuma ba kowa ya busar masa da zuciya ba sai ita. Ga shegiyar yarinyar nan da suke alatar juna ar ma waftanku, kai na tsani yarinyar nan da uwarta wlhy saboda aminiyar Fateema ce Wlhy Yaya na fiki tsanar Asiya. Dan haka koma mi za'ayi sai dai ayin wannan ha in auren bazai yiyu ba. Sai kace ma ita na haifamin an kenan A da'alama kam ita in kika haifamawa. Ba kuma makircin kowa bane sai na Hajiya Fateeman. Kinga idan yaran sun auri an Asiyar ai itace zata cigaba da juyasu ko. Ke wannan fa ulline babba wlhy. Amma karki damu zamuyi maganinsu. Kizo ki sameni gobe Aunty sai dai weekend. Dan yanzu ina cemasa zan fita zai iya zargin wani abu kin dai sanshi da kaifin tunani. Amma weekend zan tambayesa zuwa kitso sai na zo To hakan ma yayi ALLAH ya kaimu. Kidai kwantar da hankalinki Humm Yaya kenan, amma in sha ALLAHU zan yi ari sai anjima .... ___________ SU WAYE SU OUM?. Abah da Oum jini aya ne. Makusanta sosai dan kuwa da mahaifiyarta da mahaifinsa uwa aya uba aya suke. Kunga kenan su cousins ne. Asalinsu an jihar Adamawa ne, a wata ruga da ake kira RIGAR DARMA. Baffa Ishaq Darma da Gwaggo Halima sune tushen zuri'ar. ALLAH yayma Baffah Ishaq Darma arzi in kiwo da noma matu a gaya. Dan yana da shanaye, tumaki, awaki, ra uma, harma da dokuna da shi kansa bai san adadinsu ba. Sannan yana noma da ake kira noma ba wasan yara ba tun duniya na kwance. Yaransu hu u. Mata biyu maza biyu. Abubakar shine babba, suna kiransa da suna Sardauna. Sai Umar, sai Maryam, sai auta Khadijah. Baffah Ishaq baiyi karatun boko ba daga shi har matarsa. Amma hakan bai saka ya tauye yaransa ba daga yi. Su duka sunyi karatun boko mai zurfi har matan. Kafin Sardauna ya fara aure bayan kammala degree insa na farko. Ya auri ar aminin Baffa Ishaq da yakema kallon tamkar an uwa. Ansha shagali matu a irin na nunama tsara a wancan lokacin, amarya da ango suka tare acan cikin garin Adamawa. Bayan auren Sardauna da kusan shekara hu u sannan Umar shima yayi tare da Maryam a rana aya. Shima Umar ya auro ne daga iyar dangi anan cikin Rigar Darma, ita kuma Maryam aka aura mata wani an Alhaji da suke hu a da baffah tsahon shekaru. Yana zuwa ya sayi dabbobi masu yawan gaske a duk arshen shekara, a hankali zuminci ya ulle tsakaninsa da Baffan har suna kallon kansu tamkar an uwa (mutanen da kenan masu girmama alkairi). Shi wannan Alhaji dai yana zuwa daga jihar Kano ne, asalinsa kuma an garin Kura ne. ansa aya tal a duniya mai suna Kasheem. Yana karatu a turai. Yazo wani hutu gida Nigeria ya biyo babansa nan Adamawa shine ya ga Maryam itama a lokacin tazo hutun makaranta daga Yola. Aifa yace yaga mata, Baffa kuma yace ya bashi halak malak. Ansha biki nan ma na nunama tsara, Umar ya tare da matarsa anan Rigar Darma, ita kuma Maryam aka wuto da ita Kano. UBANGIJI mai hikima shakara aya tak ALLAH ya sauki matar Umar lafiya, har kuma lokacin yayan su Sardauna ALLAH bai bashi haihuwa ba shi. Dan matarsa ko atan wata ma bata ta a yi ba. Kaf family sunyi murna, sun kumayi farin ciki, an sha shagalin suna shanaye sun sha wu a da ananun dabbobi yaro yaci suna Aliyu (Abah kenan UBANGIJI mai rahama matar Abubakar bata yaye Aliyu ba sai ga wani cikin. Dole aka cire Aliyu daga nn, sai kawai matar Sardauna ta amshesa ta yaye. Daga wannan yaye ne kuma bai sake dawowa wajen iyayensa ba su Baba Sardauna suka cigaba da ri o tunda su har lokacin ALLAH bai kawo iyaka ba. Matar Umar ta sake haihuwar namiji yaci sunan Hamza, shima bata yaye ba ta kuma samun wani cikin. A ta aice dai sai da ta jera yara hu u duk maza sannan itama Maryam ALLAH ya kawo ciki. A kusan tare kuma suka sake haihuwa da matar Umar da tai mace a wannan karon. Itama dai Maryam iya mace ta haifa da taci suna Fateema (Oum kenan Itama Maryam matar Babban Yaya wato Sardauna suka kawoma yayen Fateema. Bakuma su sake waigawa ba dan a lokacin ne ma suka bar asar. Hakan da sukai na nufin suma sun barma Sardauna Fateema har abadan. Wannan abu ya saka Sardauna da matarsa kukan farin ciki da sake jin auna da soyayyar an uwansu. Basu haihu ba amma gashi suma sun mallaki a. Bayan nan itama Auta Khadijah tayi aure anan cikin garin Adamawa. Itama kuma babu jimawa ta fara haihuwar. Itama kuma anta na fari haka ta mallakama Sardauna shi kamar yanda sauran an uwanta biyu sukayi. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH fin shekara goma sha sai ga matar Sardauna da ciki. Zamu iya cewa wannan zuri'a basu ta a tsintar kansu a irin farin cikin da suka samu kansu ba na wannan tsakanin. Dan tuni Maryam ta baro asar waje tazo gida Nigeria. A lokacin yaranta biyu da Kasheem Kura bayan Fateema da sukai yauta. Majdiya, Sulaiman. Itama Khadijah nada biyu bayan Sa'eed da sukai auta ma Sardauna. Sai matar Umar nada biyar bayan Aliyu da sukaima Sardauna yauta suma. Ansha matu ar shagali da bidiri na wannan ciki har ALLAH ya kaishi haihuwa aka haifo an biyu duk maza. Kwantata muku irin shagalin da akai ai bashi misaltawa. Musamman Aliyu da Fateema da Sa'eed da akai anne. Zuwa yanzu Aliyu ya fara zama saurayi, dan yana da shekara kusan goma sha bakwai a duniya. Yayinda Fateema keda goma sha aya cif. Akwai wata irin sha uwa da aunar juna a tsakanin Fateema da Aliyu mai ban mamaki. Sun tashi tamkar wasu tagwaye duk da Aliyu ya bata shekaru sosai. Soyayyar ce mai arfi irin wadda zaman rubutata ma jan lokaci ne. Gashi suna matsanancin kamanni dan ita Fateema ta ebo dangin mahaifiyarta ne gaba aya. Sauran yaran Maryam kuwa sun biyo mahaifinsu Kasheem Kura sosai. Hakama yaran Umar annen Aliyu kaf insu sun ebo gida ne, babu wanda ya biyo mahaifiyarsu, suma yaran Khadijah duk suna kamanni da danginta. Sai su an biyu. Wannan yasa suke jin alfahari akan su jininsu nada arfin da suke ebo kamannin gida ne. Yanda su iyaye ke kamanni da juna haka suma an duk suka ebo. Hatta da yaran Maryam dake kamanni da mahaifinsu sun ebo wasu abubuwan nasu, ita dama Fateema gaba ayanta sune. Soyayya da sha uwar Aliyu da Fateema yasa Baffah Ishaq bama ansa shawarar ha e yaran aure saboda gudun shai an a tsakaninsu, dan sha uwar tayi yawa matu a komai zai iya faruwa. Babu kuwa wanda yayi musu akayi hakan. Fateema nada shekara goma sha biyu da wasu watanni, Aliyu nada goma sha tara da wasu watanni aka aura musu aure. Akai kuma shagalin biki irin na gata sai dai sun tare anan gidan Baba Sardauna in dan yace yaransa bazasuyi nesa da shi ba. Balle kuma gasu yara anana basu kai warin da za'a barsu su ka ai ba tukkuna. Soyayya ta ara arfi a tsakanin Fateema da Aliyu, yayinda a gefe suke ta karatunsu ga kuma kulawar iyaye. Aurensu nada shekara uku ALLAH yayma gwaggo Halima rasuwa. Kaf wannan zuri'a ta Darma sunji wannan mutuwa matu a, sunyi kuka har sun rasa hawaye musamman ma Baffa Ishaq Darma daya rasa mata ar uwa uwar ansa. Bayan rasuwar tata kuma shima duk sai lafiya tai masa aranci. Shekara biyu tsakaninsu shima yace ga garinku nan. Matu ar ru ani wannan family sun sake shiga, har takai Baba Sardauna da Baba Umar sun kasa jin da in zaman garin Adamawa sukayo hijira zuwa Kano. A lokacin shekarun auren su Aliyu biyar cif a duniya. Fateema nada sha shida, Aliyu nada ashirin da uku. Ya kammala karatunsa na jami'a, ita kuma zata shiga ss a sakandire. Shekarar da Fateema ta kammala sakandare a shekarar ALLAH ya bata ciki. Murna da farin ciki ba'a magana. Dan wannan zuri'a na matu ar son haihuwa. Sosai cikin ke bata wahala, kullum tana nane da Ummanta. (Matar Sardauna) Dan soyayya take musu ta ha a da sam bama su san ainahin ba itace mahaifiyarsu ba sai lokacin da akai musu aure. Hakan kuma bai sa sun canja daga soyayya da aunar da suke mata ba. Itama kuma haihuwar da tai baisa ta sassauta soyayyar da take musu ba a matsayin a har gobe. Haka dai akai wannan rainon ciki Fateema kullum na sashen iyayensu. Har abun na damun Aliyu dan idan yana son ya kasance da ita sai yayi mata wayo da yar tazo nasu sashen da aka ware musu a gidan. A haka ALLAH ya kai wannan ciki lokacin haihuwa. Sai dai yazo da doguwar na uda. Tun ana hasashen haihuwa a kusa har al'amarin ya fara bama kowa tsoro aka yanke shawarar yimata theater. A wancan lokacin matu ar tsoron theater akeyi dan kodai a rasa a ko a rasa uwa. Dole da wahala cikin biyun nan aya bai kasance ba sai idan duk suna da tsohon kwanan ne uwar da an. Aliyu kuka ya sanya akan bai amince ba, sai da likita yayta lallashinsa da su Baba Sardauna sannan da yar ya amince aka shiga theater da Fateema....... _(Ina fatan dai kuna gane kan labarin . Fateema itace OUM a yanzu, Aliyu ne ABAH a yanzu ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani