← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 104

Sashe 29

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baki a bu e, Mawaad Company ko kamfanin Rolex bazasu nuna masa yatsa ba a angaren agogo. Basa aukar ma'aikaci sai wanda yasan abinda yake yi. Sannan babu zancen sai an wane ko sanayya, akwai turawa ma'aikata anan tun daga Chinese harma da Europe da sauran asashen ba en fata. Komansu da a'ida da doka yake tafiya. Kayansu ba kayan yara bane, manyan sarakuna da attajirai ke iya sayen kayansu a kowacce kusurwa ta duniya, tunda kikaga turawan nan da larabawa na tururuwar amfani da agogunan Mawaad ai ba sai na cigaba da cewa komai ba. Barama dai na daina cewa komai, ke da kanki zakizo kina bani labari watarana in sha ALLAHU. Abinda nake so dake dai ki nutsu wajen interview nan. Dan harda boss in companyn da kansa za ai miki ita, ina nufin CEO na companyn. Duk da dai nasan banda matsala dake in sha ALLAHU. ALLAH ya bada sa'a da nasara idan alkairi ne. Muje na rakaki har ciki. Zan jiraki har ki kammala sai muje ki duba Aunty babba ko? A'a ka koma wajen aikinka kawai ba damuwa. Idan na gama zan koma da kaina. Tunda bamu san yanda abin zai kasance ba. Duba Aunty kuma basai ka kaini ba zanje da kaina ne Hummm ya fa a fuskarsa auke da murmushi. Daga haka suka fito a tare. Idan ka gansu dolene su birgeka matu a. Dan sun dace da juna. A jere suke tafiya cikin tsari da nutsuwa. Dan shima RK dai-daita tafiyar tasa yay data Maanal duk da kasancewarta mai sanyin tafiya da tsantsar nutsuwar iya taku. Sam bata da hauma-hauma ko garaje a tafiya ita. Sun tsaya a ha iyar ofar wajen data kasance ta zallar gilashi, koda yake bama ofarba shi kansa ginin akwai gilashi sosai a cikinsa shiyyasa ya zauna da yau kaikace ba'a Nigeria kake ba a wata Chaina ce can dan sune mayu. Sai dai kuma a cikin Abuja wannan ba komai bane kasancewar akwai gine-gine na awa da asaita da sukafi Mawaad Company komai ma. Duk da sanin da securitys ofar sukaima RK sai da ya saka I'd card in aikinsa akan wani computer sannan ofar ta bu e masa da kanta. Ya gaisa da securitys in idanunsa akan Maanal datai kicin-kicin da fuska. Juyawa yay ya musu an ta aitaccen bayani a kanta. Cikin gamsuwa suka shiga jinjina masa kai... (Eh lallai ashe kallo na daga ciki) cewar Maanal a zuciya. Dan kuwa tabbas Companyn nan ya ginu da iya nasa tsarin da awa. Sun fara iske reseption, anan suka tsaya suka saka sunansu sukai signing kamar yanda tsarin Companyn yake ga ba o ga ma'aikaci, kafin ma'aikatan dake a floor na farko, zamu iya cewa wani department ne anan na sashen Companyn, duk sun du ufa aiki, yayinda wasu ke faman kai kawo da uzirin gabansu daya shafi aiki. Tunda suka shigo wasu ke kallonsu, wasu na zungurar wanda basu gani ba, yayinda wasu ke uskus, wanda ke an kusa da su kuma na gaishesu. RK ka ai ke amsawa, Maanal kan an jinjina kanta kawai itadai tana mai kallon komai. Daga haka suka isa ga elevator, shi ya danna ta bu e, ya mata nunin ta fara shiga sannan shima ya shiga. Shine ya sake daddana number floor in da zasuje sannan ya matso kusa da ita yana magana a hankali. Kin fara ganin yanda tsarin yake ba? Maimakon amsa masa da baki sai ta ce masa, Uhmm . Kawai, dai-dai nan suka iso inda suke son zuwa. Sai da ta gama bu ewa suka fito. Sun samu matashiyar budurwa auke da files a hannu zata shiga elevator in. Tana ganin RK ta saki an murmushi da fa in, A'a ashe shiyyasa yau garin kamar da hadari, ashe babban ba o ne damu a Mawaad Murmushi yay mata da amsa mata da, Kedai masheranciya ce Labibah. Ykk ya aikin? Babu wani sharri sai gaskiya. Aiki gashi nan muna ciki. Nikuma ina lafiya To Masha ALLAH. Iji dai boss na nan? Humm zaune kuwa. Kasan baya wasa ai sai da dalili ko zai le a office in gwamnati. Yanzu naga ya dawo dan ya shigo da safe sai kuma ya fita. Okay, to bari mu arasa Babu damuwa. Sis.. barka tunda shi ya kasa gabatar min dake Karan farko Maanal data auke kai daga garesu ta an juyo ta kalleta. Hannu ta bata kawai alamar suyi musabaha batare da tace komai ba. Sai shine ya ce, Labibah bazaki ta a canjawa ba. Da kinyi ha uri ai zanzo da ita har office inki ne idan na gama da boss Ato shike nan babu damuwa kuje. Nima zanje office in CMO ne Okay tom ba damuwa sai mun fito Daga haka ta saki hannun Maanal ta shige elevator in su kuma suka wuce. Office in Assistant insa shine farko kafin na boss dake ciki. Ya tarbesu da girmamawa alamar akwai sanayya tsakaninsa da RK in sosai. Dan RK in yata tsokanarsa kafin yace masa bari ya sanarma boss in zuwansu. Ita dai Maanal hankalinta ma nakan an bin Office in da kallo. Komai tsaf kuma al babu wani tarkace ko hayaniya. Baifi mintuna hu u ba ya fito yana sanarma RK oga yace ya shiga shi ka ai. Murmushi kawai RK yay da an girgiza kansa. Kafin ya matsa inda Maanal take zaune dan shi dama yana daga tsaye ne. Kinga ina zuwa. Minti biyar kawai Kanta ta jinjina masa batare da nuna damuwar da yay tsoro ko acin rai daga fuskarta ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta ciro novel inta daga bag ta cigaba da karatunta. Shima Assistant in barin Office in yay da alama akwai inda zaije. Kusan mintina hu u sai gashi ya dawo. Mazauninsa ya koma ya zauna bayan ya ajiyema Maanal ruwa da lemo. Baice mata komai ba itama batama kulashi ba balle kallon abinda ta ajiye. Tana nan a zaune fin mintuna goma sannan RK ya fito. Zama yay a kusa da ita yana bata ha urin da ewarsa. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, Ba komai . Ta maita hankalinta ga book inta. Shima dai wayarsa aka kira, dan haka ya mi e ya fita aka sake barinta ita da Assistant. Suna nan a haka wani an abu dake desk insa yay ara, mi ewa taga yayi ya nufi hanyar officer in ogan kamar yanda suka fa a. Bai wani jima ba ya dawo, cikin mutuntawa yace mata ta taso suje. Littafinta ta saka a bag ta mi e batare da tace dashi komai ba. Ta wani elevator ba wanda suka shigo ita da RK ba suka shiga da Assistant in, cikin sakanni ya saukesu inda suka nufa, koda suka fito nan ma sai taga offices ne a wajen. Sun shiga wani waje da alama ta nuna conference room ne, sai dai bai arasa da ita can ciki ba ya nuna mata wajen zaman daga nan ta inda aka shirya kamar masau in ba i. Tana zama wata ta kawo kofin coffee ta ajiye mata da drink. A tare suka bar wajen ita da Assistant in sai ita ka ai kenan. Babu abinda ta ta a ta sake ciro novel inta ta cigaba da karatu...... Fin tsahon mintuna talatin tana a wajen babu wanda ya sake zuwa, har ranta ya an fara sosuwa sai ga wasu mutane uku sunzo sun gittata sun shiga conference room in, tsakanin inda suka bin da inda take akwai ar tazara, shiyyasa bata wani shaida kowa ba. Bayan shigewarsu fin mintuna biyar wasu biyu suka sake wucewa, kasancewar bata ago ba a yanzu sai da suka gama shigewa taji motsin rufe ofa. an mintuna ka an Assistant ya zo wajenta yace ta shiga. Kanta kawai ta jinjina masa tare da maida book inta a bag ta mi e. A ranta tana mamakin wannan abu kamar wula anci, ana tattalin aukar ma'aikaci da alama su nan yanga sukeyi. Da wannan tunanin ta tura glass door in a hankali ta shiga da sallamar da bata tunanin zasuma iya jinta saboda yanda ta yi ta ciki-ciki, dan wani irin bugawa ziciyarta ke mata da sauri-sauri da batasan dalili ba, amma haka ta danne tana arama zuciyar tata arfi. Sai dai kuma da alama sun ji sallamar tata in, dan wasu a cikinsu sun amsa. Taji hakan ne a bayyane dan ba kallonsu take ba su duka. Sai da aya a cikinsu ya furta, Bismillah zaki iya zama . Sannan ta ago ta kallesu tana mai jinjina kanta zuciyar tata dai na cigaba da bugu. Mutane ukun dake fuskantar inda zata zauna kawai ta iya ma kallo cikin sakan biyu. Wanda ke zaune kuma a kujerar dake gefen inda take bata ko kallesu ba. Sai kujerar dake tabbatar da oga kan zauna yayin meeting shima bata wani dubesa ba. Shima kuma kansa a du ufe yake yana duba wani magazine kamar ma bai san da zaman kowa ba a wajen. Kujera aya taja ta zauna zuciyarta na mamakin ai mutane biyar kawai taga sun shigo, ya akai taga kusan takwas anan?, rashin mai bata amsa ya sata shiga gaidasu. Amsa mata duk sukayi, sai dai bata jin shi wancan ya amsa in. Shiru kamar na mintuna biyu kafin aya a cikinsu ya fara mata tambaya. Babu ko ar a tare da ita ta amsa masa. Kansa ya jinjina sosai dukansu suna mamakin ta. Wanda ke tsakkiyar sa shima ya sake jeho mata tasa tambayar. Nan ma ta sake amsawa babu ko wani ar. Dukansu kam sai da suka sake dubanta wannan karon saboda jarumtarta da kaifin basira da suke kallo a bayyane, sai dai abinda basu sani ba dannewa kawai takeyi, dan tana cikin wani hali da ita kanta ta gagara bashi fassara. Gashi a masu mata interview ba wai ba enmu bane balle ma ace hausawa. Hausawa biyu ne ma kawai a cikinsu sai CEO in da har yanzu bataga fuskarsa ba. Amma dai hannunsa dake sa ale da wani shegen Designer agogo da zoben dake neman harmutsa tunaninta na azurfa ya nuna bakin fata ne duk da kallon fisha tai masa kawai. Na ukunne da baice komai ba tun azun a yanzu cikin turancinsa mai fita da harshen Chinese ya furta Woow, You are
Chapter 29 · 0% Book details