← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 104

Sashe 26

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta sanar mata akinsa ma a kulle yake. Waya ta aga tai kiransa. Batare da amsa sallamarsa da gaisuwarsa ba tace yazo tana nemansa. Ha uri ya bata akan shi fa ya koma Abuja. Dan ya samu kira na gaggawa. Ranta ya matu aci amma sai ta danne bisa shawarar da Sabuwa ta bata na a dinga lalla ashi yanzu har ayi a gama lafiya. Cikin sau a murya tace shike nan idan ya dawo sayi magana. ALLAH ya bada sa'a. Ya amsa mata da Amin, dan ko yaya ya an ji sau i a ransa na jin bata fushi da shi. Yazeed mutum ne mai kiyaye fushin iyaye, sannan yana da takatsantsan akan al'amarinsu. Ko wannan maganar Manaal in da ace babu goyon bayan Daddy duk son da yake mata da tuni ya ha ura saboda mutuntasu.... ________ A Abuja dai kam RK ya ri ema Maanal wuta. Dan kullum sai yazo gidan Shahidah sai ya fake da dubata yazo yi kasancewar dama sun sanar dasu hakan. Sai dai abinda basu sani ba duk tsarin RK ne dama akan batun zuwa gida dubatan kullum. Ya cigaba da kwa aita mata zancen aiki. Tun tana dojewa harta sanarma Shahidah. A mamakinta sai Shahidah ta bata goyon bayan mizai hana ta amshi tayinsa. Ai abune mai yau neman nakanka musamman a wannan zamanin. Cikin damuwa Maanal ta ce, Amma Didi kin san Ammie bazata yarda ba. Hakama Daddy zaiga kamar mun nuna gazawarsa ne musamman idan mukai dubi da duk yaransa mata babu wadda ya bari tayi aiki, ko ku sai da kukai aurene yace idan mazanku sun yarda kuyi aikinku. Idan ni kuma nazo masa da sabon tsari sai yaga kodan bai haifemu bane ba Hakane Maanal. Amma idan aka duba naki al'amarin ke ai yana bu atar uziri. Bazamu yanke hukunci ba yanzu ki bari zan sanarma Ammie to. Itama Amal zanyi magana da ita. Amma ko nan Daddyn su Barru shi goyon baya ya bada ari bisa ari, ya kuma ce in dai dan Daddy ne shi a barsa zaiyi magana da shi. Kinga an samu sau i kenan ai Shike nan ALLAH ya za a mana abinda yafi alkairi. Amin ya rabbi, wannan dama itace addu'ar daya kamata kiyi tun farko. Sannan dan ALLAH idan yazo ki daina aure masa fuskar nan taki, hakama idan ya kiraki kina auka Auta. Wula anci sam bashi da Didi ba wula antasa nake ba nima. Bana son ya saki jiki akan abinda bazai samu bane kawai Hummm Maanal kenan. ALLAH dai ya za a mana abinda yafi alkairi Maimakon ta amsa da Amin sai Maanal in kawai ta koma ta kwanta dama tana a akinta ne tana karatun novel in nata na fama Shahidahn ta sameta........ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ........Shahidah ta kira Ammie ta sanar mata da komai game da abinda RK yazo ma Maanal da shi. A mamakin Shahidah sai ji tai Ammie na maimaita kalmar Alhamdullah. Kasa daurewa tai ta ce, Ammie kin amince kenan kema tayi aikin? Sosai kuwa Shahidah. Dan wannan wata mafita ce da masalaha UBANGIJI ya kawo mana. Ban sanar daku bane kawai amma tunda muka baro Abuja na dawo gidan nan a cikin cakwakiya ake da tashin hankali duk kuma akan batun auren Maanal da Yazeed ne. Namayi mamaki da kikace yau kusan kwana biyar bai le oku ba tunda yana Abujar shima. Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana arin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko aura musu aure kukai? Ko har yanzu Mamma in ce ke tijarar bata son? ar dariya Ammien tayi da fa in, Kefa da ina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan dai Hajiya Yaya ne da batun auren...... Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu. Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq in amma ha ata kishi da wannan ar iskar yarinyar sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya ha e kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata ta buga. Amma kinga Rafeeq in nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal in ce ta i sakin jiki da shi kin dai san halinta Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu'a. Watarana ai sai labari. Amma in sha ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su arata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na ha ashi da abokin nasa. Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi A'a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar? Alhamdullahi Ammie jikinta na yau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels in nata na fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu To Masha ALLAH, ALLAH ya ara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next week haka komai ya ara lafawa. ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba? Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ananun Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama.... ___________ Kamar yanda Ammie taima Shahidah al awari ta tunkari Daddy da batun aikin Maanal. Sai dai kuma kamar fa yanda tai tunani ya nuna acin ransa. Ya kuma tujareta da masifa dan dama yana ri e da takaicinsu ita da Hajiya Basariyya a rai. Kasa magana Ammie tai sai du ar da kanta kawai tai tana saurarensa. Sai da yay mai isarsa yay shiru dan kansa sannan ta tashi ta kwanta dan dama itace da shi a yau in. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga rige-rigen sakko mata. Sosai tausayin kanta dana iyalanta ke ara girma a zuciyarta. A rayuwarta tayi farin ciki ne da samun ancin kai na shekarun uruciya kawai. Amma tun daga randa aka lullu a mata zanen aure zata iya cewa daga lokacin ADDARARTA ta fara. Daga lokacin ta fara tantance gatan iyaye da acin rabuwa da su. Daga lokacin komai ya canja, sunanta na Asiya sarauniya ya canja zuwa Asiya baiwa. Eh dole tace bauta, duk da a zahiri baza'a kalli rayuwar tata ata mai bauta ba kasancewar wasu abubuwa sun mata ado a bayyane. Sai dai wanda yasan ainahinta ne kawai zai san minene mizanin bautar da take magana da ancin kai. Ansha gwagwarmaya na tsawon shekaru kafin ALLAH ya iyakance, iyakancewar bai zama sau i ba kai tsaye, wata sabuwar jarabawar aka sake shiga, ta yanda zaren addarar ne ya kawota a wannan matsayin da take a yanzu kuma. Bazatai butulci ma UBANGIJI ba, domin kuwa Alhamdullah, ta samu canje-canje masu yawan gaske a sabuwar rayuwarta, sai dai anan in ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani...... Asia! Kuka kike yi? Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan ta juyo garesa fuskarta da murmushi. A'a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana ank..... Ya arrahaman . Ta fa a da sauri tana mai gaggawar aura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu hawayen da take ri ewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba aya. Dan ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban ta a raba ayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema a. Kana musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan ba anta maka rai ba ko antar da dokar ka b..... Shiiiii!! Ya isa kukan haka to Daddy ya fa a yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfi e a fuskarsa. A hankali yake shafa bayanta cike da lallashi. Tsahon minti aya kafin ya furta, Nasani Asia. Na kuma yarda dake ari bisa ari. Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A'a ku dukanku kowa da inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin ana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya auke mata kewa
Chapter 26 · 0% Book details