Sashe 57
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan Yaseerah. Dan dama sunyi da ita yau da wuri zataje gidan kasancewar tunda tazo sai dai tayi zuwan fisha. Ta samu ko barci basu tashi ba. Saboda weekend ne mijinta na gida. Sai kawai ta shige ayan bedroom in Yaseerah ta kwanta itama ta ora barcin da bata samu yi ba a daren jiya isashe. Sai wajen sha aya Yaseerah da mijinta suka fito. Suna a d/table zasu fara breakfast mai aikinta ke sanar mata zuwan Huznah in. Mijin nata ta kalla tana an murmushi. Baby Uncle inka fa ya rikita min awata. Munata binsa kuma ya i bamu muhimmanci. Yakamata ka shiga lamarin nan haka nan Murmushi yay shima dakai kofin tea bakinsa. Ai dama na fa a mata tun farko, shi bana wasan yara bane. Dama Uncle Fawzan ne da sau i, amma Uncle AA tab in, ina tausaya mata ALLAH. Da zata ji shawarata da ta jima da manta ta ta ama saninsa kawai. Bazan iya haka ba Abdul-hakeem. Dan a yanzu bani da wani burin daya wuce mallakar Uncle inka. Muryar Huznah da basu san da zuwanta wajen ba ta ratsa kunnunwansu. Gaba ayansu juyawa sukai suna kallonta, ganin yanda hawaye ke sauka mata da gudu a saman yawar fuskar ta ya sasu mi ewa. Hannunta Yaseerah ta kamo ta zaunar a kujerar kusa da ita, itama takai zaune tana ri e hannunta alamar lallashi. Shima zama yay mijin Yaseerah in, wani irin tausayin Huznah na ratsa shi. Tabbas yasan ta aukarma kanta abinda yafi arfinta, amma ko ya cigaba da gaya mata gaskiya yasan ba lallai ta fahimcesa ba. Gyaran murya yay a hankali, hakan ya sasu agowa su duka suka kallesa.. In sha ALLAHU zan taimakeki. Sai dai ki sani wlhy Uncle AA nada wahalar sha'ani. Amma akwai mafita aya da nake miki hasashen idan kin gwada maybe ki dace.... Jikin Huznah har rawa yake ta ce, Wace irin mafita ce. Komai wahalarta ALLAH zan gwada, komai alubalenta kuma zan jure Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya sauke numfashi. Batun yanzu ba nasan Grandma suna fama da Uncle AA yay aure. Kuma a yanzu haka ma suna gab da masa auren ne amma bani da tabbacin sun sama masa matar ko basu sama masa ba, duk da dai akwai wata sister in mu dake sonsa matu a kuma naga duk dangi nason a ga asu aure, shine dai bai maida hankali ba. To ina ganin mafita aya ce na baki number in grandma, ko kuma ki shirya na kaiku ke da Yaseerah kamar zaku gaisheta sai muce ai ke budurwar Uncle AA in ce. Idan ALLAH ya taimaka aka dace sai kiga ya amsheki dole bisa umarninsu. Hakan yayi miki? Cike da zumu i ta amsa masa, tana share hawayenta ga dariya. Shima murmushi yayi hakama Yaseerah. Ya ce, Sai ki zama cikin shiri dan sai nan da kwana uku Miyasa ba yau ba? Ta fa a cikin damuwa. Bata nan ne shiyyasa, amma ina saran dawowarta gobe ko jibi in sha ALLAHU Ajiyar zuciya Huznah ta sauke. Badan taso hakan ba tace ALLAH ya kaimu. Dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Koda ta duba sai taci karo da Yaya Yazeed. Mamaki ta kamata, dan hakan kan jima bai faru ba ganin kiran yayan nasu. Haka dai ta daure ta aga dan tasan in har wayar ta tsinke bata aya ba sai taci ubanta a hannunsa. Ko amsa sallamarta baiyi ba cikin kaushin murya ya ce, Kina ina nazo gidan Shahidah ba ya nan? Rawa jikinta ya fara, cikin karkarwar harshe tace, Yaya wlhy bawani wajefa naje ba ina gidan Yaseerah ne nazo gaisheta Na baki mintuna ashirin kawai ki dawo gida. Idan ba haka ba hummmm! . Ya yanke kiran. Kanta tai wani irin dafewa dan takaici, batama san ta fara antayama Yazeed in zagi ba Yaseerah na tayata. Babu dai yanda zatai dole ta kimtsa mijin Yaseerah in ya auketa domin maidata da kansa. Dan hakan kawai zatai ta ku uta daga bala'in Yaya Yazeed. Dabarar tata kuwa ta taimaketa, dan ganin Abdul-hakeem in ya sassauta tanadin da Yazeed in yay mata. Sai dai duk da haka taci zagi da fa a akan fitar sassafe babu kuma sanarwa. Ya kuma ja mata dogon garga i akan in har ta kara fita a gidan wlhy sai ya mata dukan mutuwa. Yana tafiya ta koma aki tai kiran uwarta ta gaya mata tana kuka. Zage-zage itama Hajiya Basariyyar ta dinga yi da tsinar Yazeed in. Sai da sukai san ransu ta koma lallashin Huznah da kwantar mata da hankali akan zatama Yazeed in magana da kanta. Daga haka sukai sallama. Bata ko ara fita a akin ba duk uruntun da su Shahidahn keyi akan shirin tarbar ba i su Oum. Sai ma nacin son samun AA take a waya amma hakan ya gagara. Da alama ma yayi blocking in ta ne ita bata gane ba. Ai ko saita zauna tanata kuka. Sai da tayi mai isarta barci yay awon gaba da ita..... ___________ arfe hu u da kusan rabi dan areriyar motar Fawzan ta iso gidan. Yana gama parking Barrah da Haneeff suka fice zuwa cikin gida aguje suna wala kiran mamansu. Dariya Fawzan ya dingayi, dan shi ALLAH ya aura masa son yara matu a. Kodan har yanzu ALLAH bai bashi bane. Dan matarsa bata ta a ko atan wata ba shekara shida kenan. Oum ma dariya take ma yaran. Maanal dai komai batace ba, sai ma jagorantar su Oum tayi zuwa cikin gidan. Sun sami Shahidah na arin fitowa tarbar su Oum, dan haka sukaci karo a ofa. Cike da wani irin farin ciki Shahidah da Oum suka rungume juna. Sai kawai Shahidahn ta saki kuka. Harga ALLAH tana matu ar son Oum, dan mace ce ar halak da bazasu ta a mantawaba a tarihinsu. Ta matu ar taka rawar gani a garesu da Ammien su ta yanda baki yayi ka an ya bada labari. Itama Oum in hawaye take da murmushi duk a lokaci aya, ta ago Shahidah tana mai share mata hawaye. Uhm-uhm kefa yanzu kin girma Sheedan Oum, ke uwa ce babbar yaya kuma Dariya Shahidah ta shigayi, hakama Fawzan dan tuno wani abu daya shu e. Maanal ma dai murmushi ne mai fa i akan fuskarta. Abinda a yanzu yake da matu ar tsada da wahala a gareta. Sai da Shahidah ta saki Oum sannan ta lura da Fawzan, cike da mamaki ta ri e ha a da fa in, Oh ni ALLAH wanake gani haka ya zama dattijo? A'a tsoho na zama ba dattijo ba . Fawzan ya bata amsa yana hararta. Dariya duk suka sanya masa. Shahidah ta ce, ALLAH kuwa ka yarda ka zama dattijo yanzu Yaya Fawzan Kema kin zama dattijuwar ai Ya fa a dai-dai suna kaiwa zaune a ayataccen falon nata. Dai-dai nan mijinta ya fito. Cike da mamaki idonsa akan Fawzan ya ce, Kai kai wanake gani haka kamar Darma a gidana Ya arrahaman Busam! Shima Fawzan ya ambaci sunansa yana mi ewa. A tare suka cafke alamar lallai sun san junan kuwa sani bana wasaba. Ai sai su Oum suka koma an kallo. Sai da yar Shahidah ta iya fa in, Nifa ban gane ba, wai dama kun san juna ne? Farin sani ma kuwa. Darma tare mukai degree master namu ai a Germany, sannan a yanzu haka akwai ala ar aiki a tskaninmu. Kawai dai baya son zumuncine shiyyasa baki ta a ganinsa a gidan nan ba..... Wula anci ai kai zumuncin kake so? Nadai fika tunda ni naje gidanka har sau biyu . Cewar Abban su Barrah. Dariya Fawzan yay da fa in, Gori kenan. To yanzu ai gashi ALLAH ya kawoni, ashema ni anwata kake aure kai wannan abin kunya da yawa yake Ato kaima dai ka fa Cike da girmamawa Abban Barrah ya gaida Oum. Itama ta amsa masa da kulawa cike da farin ciki. Nan fa aka alle ta i tsakanin Oum da Shahidah, Fawzan da Abban Barrah. Yayinda Linda tuni ta cika musu gabansu da kayan ciye-ciye Maanal na tayata. Duk wannan bidiri da ake Huznah na aki tana sha ar barci abinta. Sai da Maanal ta taje akin ajiye kaya ta ganta baje a gado. Komai bataceba ta ajiye ta dawo wajen su Oum. Sai ga RK da dama yay musu alkawarin samunsu a gidan. Nan fa hirar ta ara armashi dan tuni Abban Barrah ya janyesu sun koma falon ba i dan Oum ta sake itama suyi tasu hirar. Hakan yama Oum in da i sosai, dan ta samu tattauna abubuwa da yawa da Shahidah wanda Maanal ta kasa sanar mata komai saboda zurfin ciki da miskilanci. Sai da akai magriba sun dawo Huznah ta fito. A an yatsine ta gaishe su, sai dai saukar idanunta akan Fawzan yaso birkita mata lissafi. Sai da ta nutsu ta fahimci ashe ba AA inta bane kammanni ne kawai. Dan suna kama sosai da AA in, sai dai wasu abubuwa da suka an babbanta su. Hakama kuma suna kamanni da Oum matu a. Hankalin Huznah ne ya tashi, dan haka kawai take ji a ranta wannan mutumin na kama da AA in ta hakama matar, sai dai yanda ta gaishesu yasa daga amsa gaisuwar kowa ya watsar da ita musamman RK da kamar basu aunar juna ita da shi. Su Oum na gidan nan har tara, dan har sai da Autan ta ya kirata yana damunta shi dai ta dawo ya koma gida tun azun duk basa nan gida babu da i kuma yana jin yunwa. Dariya Oum take masa da tsokanarsa akan wannan hali nasa na afa, ya girma amma bai san ya girma ba koda yaushe yana la afe da ita. Idan tai masa aure yaya kenan. Shi dai ro onta ya cigaba da yi akan su taho kawai. Tace shi bazai zo ya samesu anan ba yace ya gaji. yalesa tai tace gasu nan tahowa. Amma wayar Maanal fa ba'a gyara bane?. Sai cemata yay eh wai mai gyaran yace sai Monday ma. ALLAH ya kaimu ta bashi amsa tare da sanar masa gasu nan dawowa. Sosai Shahidah ta ha ama Oum shata ta arzi i, duk da tasan tafi arfin duk abinda ta batan. Saboda suma su Maanal haka