← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 104

Sashe 66

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

masa zataje, sai dai yana gab da shiga sashen ne Dr Ranjet yay kiransa cewar gafa Maanal an kawo asibiti. Shine ya juya a guje ya fa a mota ya fice. Fitar tasa dai-dai da shigowar motar Fawzan shima daga wajen aiki. Matarsa na a gefensa dan itama tana fita aikin, motarta ta samu matsala ne ta barta a office tai kiransa ya biya ya akkota suka nufo gida. Ganin babban yaya ya sasu fitowa da sauri Fawzan na tambayar ko lafiya yaga Uncle Rafeeq ya fita a guje?. I don't know why! Na fito kiransa ne nima fa A da alama gaskiya babu lafiya, dan kamarma waya yake hankali tashe. Maybe asibitine suka kirashi kasan Uncle da patient in nan nashi. Amma lafiya kuwa? Auta ne babu lafiya Ai Fawzan ma bai samu damar sake cewa komai ba suka nufi sashen AA su duka ukun. Sai dai Babban Yaya na arin kiran layin family doctor insu a waya da shima ke aiki a KK HOSPITAL in. Kafin doctor ya iso su duka sun rufu a kansa hankalinsu duk a tashe. Kallo aya zakaima wannan taron kasan AA an gatan dangi ne. Dan amaryar Abah ce kawai babu a wajen. Sai da matar babban yaya ta aga waya tai kiranta sannan sai gata ta iso. Kusan tare suka shigo da doctor. Itama dai macece yawa, tana da an jiki na iba dan har tafi Oum ma. Sai dai Oum ta fita tsayi da haske dan ita fara ce kamar yanda Abah ke fari tas. Kai hasalima suna kama sosai da Abah in tabbacin auren zuminci ne a tsakaninsu. Hakama duk yaran kama suke dasu, idan ka cire AA da yake da duhun fata sai dai kamanin fuskar Oum da Abah in na tare da shi shima. Duk fitowa sukai aka bar Oum da Doctor yana duba shi. Duk da cikin fa a yake mitar shi abarsa kar doctor in ya ta asa. A barshi haka baya bu atar kowane magani. Hawaye Oum take tana arin tausarsa da shafa lallausar sumarsa daya tara take cin ku e. Yayinda idanunta ke zubar da hawayen tausayin yaron nata dan gaba aya yanayinsa ya nuna alamomin tashin ciwonsa. Sam bata fatan hakan, bata son abinda ya shu e suke murna ya dawo. Sun azabtu matu ar azabtuwa da halin da AA ya shiga a shekarun baya. Da yar da addu'oi abubuwa suka sassauta. Sai tabon dake zuciyarsa da sun san har ya koma ga ALLAH bazai warke ba kamar yanda suma nasun yake zaune daram. Sai kuma gashi addara na neman sabunta abubuwa cike da ban al'ajabi da mamaki a duka angarorin biyu......... ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp channel_* https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ .........Sai da Doctor yay masa allurai masu matu arfi a cikin drip in da aka saka masa har kala uku a tare sannan barci ya aukesa. Cikin kwantar ma su Oum da hankali yace musu karsu damu in sha ALLAHU komai zaiyi normal. Dan dama akwai malaria ne a jikinsa sai kuma damuwa data saka jininsa haurawa sama sosai, kuma da alama ya kwana biyu da damuwar a ransa amma ya cigaba da jigata kansa da sabgogi kuma. Hankalinsu ya an kwanta jin abun da sau i, sai dai a asan ran kowa maganar damuwar da yake ciki ta damesu. Oum da Fawzan ne kawai da suka fahimci musabbabin damuwar zuciyarsu ke suya. Sai dai basuce komai ba akai dan ko Babban yaya daya dawo Kano basu gaya masa zuwan Maanal gidan ba. Bayan sun shiga sun gaggansa yana barci fuskar nan fayau sai dai a takure na rashin wal'wala tamkar yana ido biyu. Yayinda Oum ke zare masa takalman afarsa a hankali. Amsa Babban yaya dake kusa da ita yay ya ajiye gefe, batare daya zare masa socks in ba ya maida duvet in ya rufe masa afafun a yanda suke. Tie insa da tuni ya sassautoshi da kansa dama Oum ta arasa zarewa shima. Sai ar rigar saman long sleeve shirt insa itama ta alle botiran. Itama shirt in ta rage botira uku na sama. Su dai sauran duk suna tsaye suna kallonta, musamman Abah dake mata kallo cike da so da aunarta. Matarsa dabance a cikin mata, idan yace daban yana nufin daban inne a cikin daban. Har yanzu bai iya samun abinda zai kwatanta Fateeman sa da shi ba. Murmushi ya saki mai sanyi sakamakon ha a ido da sukai da babban yaya da shima ke murmushin, sai kuma duk suka janye ya an kalla amaryarsa itama. Itama dai Oum in take kallo fuskarta da an murmushi. Jiyay itama so da aunarta na sake dasuwa a ransa. Kai shi kam ya gode ALLAH da samun mata nagartattu na warai. Su in aljannar duniyarsa ne. Sallar magrib ce ta fita da su a sashen, amma Oum bata fitan ba sai ma umarni ta bama Fawzan akan ya kawo mata kayan sallarta nan. Da girmamawa ya amsa mata yana fita. Yayinda Abah dake kallonta cikin marairaice fuska ya furta, Amma baiwar ALLAH tunda an naki ya samu barci ai yaji tausayina kizo ki bani abinci ata fuska Oum tayi tana girgiza masa kai, Ni dai gaskiya babu inda zanje nabar yarona a wannan halin, in dai abinci ne ai na kammala Mamy ta shirya maka kuje ku arata Dad daya rasa ma abin cewa juyawa yay yana kallon Mamy, murmushi ta masa kawai da fa in, Kaima kasan ba kulamu za'ai ba an gwal babu lafiya. Mu rufama kammu asiri muje muci abinci dan nikam har uku hu u nake ganin mutane an hararar wasa Oum tai musu tana murmushi. Eh kwaji da gulmarku dai, dan kawai kanwa na kawo sai na bar yarona a halin ciwo na koma kanku Dariya sosai Abah ya kwashe da shi, sai kuma ya nunama Mamy hanya yana fa in, Kinga Kamilah muje dan na kula itama uwar an sai a hankali. Dama haka an ya akkomu a airport yana mana mazurai kamar sabon dan doka da mai laifi. Kwaji dai da shi, ba kulaku zamuyi ba sai mun warke . Oum ta fa a tana murmushi. Ficewa sukai suma suna dariya. Dama tuni matan su Fawzan sun fice. Dai-dai nan Fawzan in ya shigo da kayan sallar Oum. Ajiye mata yay shima ya fita dan kar ya rasa jami'a. __________ Alhamdullah washe gari su dukansu jikin nasu da sau i. Musamman ma AA da Oum ke faman riritawa kamar wani wai. A yanzu haka tana zaune ne bakin gado kusa da shi tana bashi breakfast, sai faman mata shagwa a yake ita ko tana lalla ashi. Su Fawzan duk sun wuce aiki bayan sun shigo sun duba shi, hakama Abah tunda ya shigo ya gansa ya fita dan yana da uziri. Mamy ma ta shigo ita da matar babban yaya. Sai dai bata wani jimaba ta tafi tabar Oum da matar babban yayan dan ita bata aiki Bussines takeyi na kawo kaya daga Chaina tana rabama ma'aikata. A yanzu haka ma da Oum ke faman lalla a shi tana zaune tana faman musu dariya. Shi dai ba wani kulata yake ba dan tsakaninsa da matan yayyan nashi gaisuwar girmamawace da mutuntawa. Amma ka gansa yana hira dasu ko wani wasa da dariya abune mai wahalar gaske dan duk anne suke a gunsa. Kai shifa mai ganin dariyarsa yanda ya kamata daga Oum sai an uwansa, musamman Fawzan ma da suke kamar wasu friends ba brothers kawai ba. Dan shi Fawzan akwai barkwanci kamar Abah, sa anin babban yaya da kusan halinsa aya da AA Oum Please ki bari haka zanyi amai . AA yay maganar a hankali yana kwantar da kansa a kafa ar Oum in cike da shagwa a. Murmushi itama tayi da kai hannu ta shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake luf-luf duk da yau ko gyara bai samu ba. To shike nan an barsa haka, ai kamayi ari, kaida in baka da lafiya abinci ya zama ma iyinka duk sonka da shi. Yanzu sai mi kake bu ata? Cikin lumshe idanu da sake maida muryarsa can asa ya ce, Barci To Alhamdullah kar a wannan ruwan addu'an kasha, Mamy ce tayo maka an jim yay yana kallon kofin, sai kuma ya auke kansa da fa in, Oum ga naki ma ban shanye ba. Ki bari saina gama da shi No na i wayon, shima kasha ai ba'asan inda za'a dace ba Fuska yaso atawa amma dai ya amsa yasa kofin a baki, bayan yayi bismillah ya shanye yana mi a mata kofin. Yauwa ko kaifa an albarka. Shike nan kwanta abinka ka huta nima bara naje na idan abinda ya rage kafin ka tashi na nema maka lunch Kansa kawai ya gya a mata yana zamewa a gently ya kwanta. Dai-dai tana tattara kwanikan matar babban yaya mai suna Saheeba na tayata. Knocking akai tare da sallama, Oum ta amsa tana bada izinin shigowa dan su duka sun gane mai muryar. RK ne ya shigo cikin takunsa na nutsuwa, suna ha a ido da AA ya saki murmushi cikin tsokana ya furta, Ayya my son ashe an kusa a gangara Harararsa AA in yay yana auke idanunsa a kansa. Yayinda Oum ke dariya Saheeba na tayata. Sai da ya kai zaune a bakin gadon ya gaida Oum, Saheeba ta gaisheshi da tambayarsa aiki ya amsa mata da kulawa da tambayarta ina yara. Amsa ta bashi da cewar suna Kano basu dawo ba sai gobe da sassafe zasu taho da mamanta. Ya jinjina mata kai kawai yana maida hankalinsa ga AA. Sorry my dear Son ai ban san abun haka ya kasance ba, sai azun Fawzan ke sanar min ashe jiya ina arin
Chapter 66 · 0% Book details