Sashe 85
Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da in zaman garin...... Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa. Lafiya Autana? Oum ta fa a tana kallonsa. Fuska ya an yamutse kamar zai saki kuka ya ce, Oum kaina ke ciwo. Kuma ina jin yunwa Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba? Kansa ya aga mata alamar Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya.... ___________ Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumu i banda Maanal da tace idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun cigaba da shirinsu kawai. angaren Ajwaad in ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu. Har ya samu Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da batun. Amma sai ya kwa esa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar zuwa Adamawa suga gida... Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da bada ala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashir an kamar zata shi e. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya shige aki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga arshe da zazza i ya yini ranar. Har washe gari sai da aka sanya masa arin ruwa. angaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama arshe zazza i ya rufeta. Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka an tsaya aka dubata. Washe gari suka auki hanyar Suru da shima keda an nisa daga nan cikin birnin Kebbi in. Dan a ranar in ma basu isa ba sai da zuhur.. Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ato bane can sosai. Ba kuma arami bane ba. Suna da wutar lantarki sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan. Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a asar da ake damawa da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka auka, nan kam basu isa ba sai yamma sosai. Giro dai aramin garine, amma auyene mai yau da ayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumu i musamman ganin harda ba in fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin. Tun daga waje zaka san gidan aton gaske ne. Dan ofa ce wangamemiya warai da gaske. Sai atuwar bishiyar ce iya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta ka an massalaci ne da akuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a sanyaye Ammie ta fito fuskar ta auke da murmushin arfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da an wayonta. Tuni yaran sun fara kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. akuna ne guda biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke bu e wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan buzu yanata rubutu a wani atoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman afarta zuciyarta na mata an sanyi, ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu... Barka da hutawa Baffah Ammie ta fa a a hankali kanta a du e dai-dai tana shiga cikin akin. Sai lokacin tsohon ya ago ya an kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta, Lale da mutanen garin dabo Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo ri e da hannun Maanal data dogare a ofa. Sai da suka kai zaune tsohon ya sake fa in, Ashe zaka cika al awari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani kafin na koma ga ALLAH? Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta, Ai min afuwa Baba, ai min afuwa Murmushi tsohon yay mai fa in gaske. Sai kuma ya mi ama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana ma e kafa a alamar bazata je ba. Turata Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce, Wuce kije mana ban son raini Duk da tsohon bajin abinda Babu ya fa a yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a arare. Bai iba ya kama hannunta ya zaunar a gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta, Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwa ayin ku ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne ALLAH ya huci zuciyarku Baba Babu ya sake fa a da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta ora da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk suka shiga gaishesa. Hannu duka ya mi a musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk ya ta a kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal na an inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye ar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya na a akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar alewa dake cike da wata warya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan..... Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai aton gaske ne da sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da a alla sun kai kusan ashirin. Yara ne sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake tsaitsaye wasu ma daga su sai karin irji. A hakan kuma alilanne a matan gidan, wa an nan wanda bazasu iya ha uri bane saboda zumu in son ganin Ammie da yaranta. Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na ra e jikin Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na arin gaishesu da kalmar Ina yini . Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ar shekara biyu. Yanzu ko gashi tana ar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar.. Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne akin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene aka dan katange da akuna guda uku. aya na Gwaggo mahaifiyar Babu aya nata. Sai ayan na kishiyarta da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ara mata ba in jini a gidan da ma wajen surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani an dutse daga ofarta tana alwala. Sau aya ta ago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa da fara'a yana fa in, Barkanki da wannan lokaci Gwaggona Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana fa in, Sannu Gwaggo! Mun sameku lafiya? Maimakon ta amsa su su duka a da ile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi. Babana kasha hanya Murmushin arfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya an sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa ya maida mata da murmushin yana fa in, Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma ina da alwala Kanta kawai ta jinjina masa. Ya mi e yana kallon su Shahidah dake raku e suna kallon Ammie dake du e kanta a asa har yanzu. Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana Jikinsu a sanyaye suka aga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu da i. Yasan dole sai ha uri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani. Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na damunsa matu a. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin iyayyace wannan mai zafi........ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 *_WhatsApp