← Book details Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 104

Sashe 14

Ajiya A Duhu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In sha ALLAHU koda yaushe cikin yi muku nake. Kuma Alhamdullah da sauyin rayuwa da UBANGIJI ya bamu mai tazara sosai, idan mukai dubi da baya. Tashi kiyi wanka naima bana maigadi magana ko zamuje wajen mai maganin nan tunda nasa anji da insa Amma Ammie shima kuma gashi ya dawo ai Duk da haka Manaal, ai kin samu ban iska tunda an samu sassaucin wahalar nan da kike sha kusan na shekaru bakwai Kanta ta an jinjina cike da damuwa. Dan ita kanta ciwon nan na aga hankalinta, ga shi kusan duk sanda zatai period sai abun ya e mata da ciwon mara da take fama da shi shima, dan kamar ciwon maran yana zama sanadin tada ciwon zuciyar ne sakamakon tuno mata da abubuwan da suka faru baya da hakan keyi a duk irin lokacin. Har rama take farayi idan akace maka lokacin nan ya matso mata. Dan ita ka ai tasan irin kalar azabar da take sha a rayuwarta. Duk yanda zata misalta ba lallai a fahimta ba. Shiyyasa idan akace mata haihuwa nada ciwo sai taita mamaki da ganin anya zata kai azabar da take sha a ciwon mara idan zatai period. Itafa nata ma dabanne dana duk wanda ta ta a sani, an uwanta ma duk sunayin ciwon idan zasuyi prioud in, amma bai kai ko rabin nata ba. Kuma sunayin aure duk suka daina. Ammie tace ita suka gado, dan itama tasha fama har sai da ta haihu sannan. To ita abin nata ya zama biyu ne, ga ciwon zuciya kuma, shiyyasa hankalin kowa ke matu ar tashi a duk sanda irin haka ya taso musamman akan ita Manaal da nata yafi tsauri. Ammie da kanta ta taimaka mata har zuwa bayi bayan ta ha a mata ruwan zafi. Haka ta daure tayo wankan ta fito sai kuma rawar sanyi. Kasa zaman shafa mai ma tayi ta haye gadon ta sake udundunewa. Dai-dai nan Amaal da Shahidah da Ammie tai kira a waya ta sanar musu suma Baba maigadi magana akan maganin Maanal in dan an uwansa ne ke bata suka shigo akin. Su kansu su Shahidahn duk fuskokinsu sun nuna damuwa. arasawa sukayi inda Manaal in ke udundune suna mata sannu. Sai kuma Shahidah ta juya ta fita tana fa in bari na amso maganin dan kamar sallamar Baba maigadin. Ilai kuwa shine, dan babu jimawa ta dawo da magani a gora. Da taimakon Ammie suka bama Maanal in saboda rashin sonta da magani. Tana gama sha kuwa sai amai, dama haka yake mata, sosai tayi aman har ta basu tausayi. Haka suka taimaka mata suka gyara mata jiki ta sake yo wanka ta canja kaya ta koma ta kwanta. Cikin amincin UBANGIJI sai kuma barci mai nauyi sosai yay awan gaba da ita. Ajiyar zuciya suka dinga saki a tare, saboda in sha ALLAHU suna ganin kuma shike nan. Barci kuwa tayi sosai, dan bata farka ba sai bayan azhar. Alhamdullah taji da in jikin, ta samu ta sake yin wanka Ammie da kanta ta bata abinci, sai da taci sosai dan Ammien nata lalla ata ga kuma waya da sukai da Nene zata zo gobe in ALLAH ya kaimu ya sake sakata jin da i saboda matu ar son Nene da take a rayuwarta. Ga kuma an uwanta zagaye da ita. Hakkanne ya sake arfafata zuwa bayan la'asar tace suje ta rakasu gidan mai gyaran jikin zata iya. Koda sukace a'a sai Ammie tace suje ai fitar zata saka ta sake jin arfin jikinta ta kuma warware. Da wannan shawarar sukai amfani suka tafi........ ZAFAFAN DAI ALBIM (Mamu gee) IRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull) Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000 0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070 Kati MTN:- 09032345899 an NIGER 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu [2/11, 8:42 PM] Maryam anas: *_Typing *_ AJIYA A DUHU.... *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ *_My TikTok account https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_Arewabooks_* Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30 _Duk wanda bai fallowing ina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama ______________ Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumes Numbers 08034469681 08135142610 Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuries TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries Facebook ummu_mahnoor_luxuries _________ .........Fitarsu babu jimawa ashe masifar Hajiya Yaya ta jiya bata are ba. Dan yau yinin nan guda bata gidan, sai yanzu zuwa yamma sai gata ita da anwarta da suke kira Aunty Sabuwa a gida da yaranta ammata guda biyu. Nan fa wata sabuwar fitinar ta tashi dan har sashen Ammie suka sameta wai sun sake zuwa mata garga i ita da Maanal akan Yazeed. Yayinda aka nuna aramar ar Aunty Sabuwar wai itace Yazeed zai aura dan haka sai Maanal da Ammie su maida maitarsu a kansa. Ba aramin zafi kalaman sukaima Ammie ba. Ga shi lokacin su Manaal ma basa gidan taje raka su Shahidah gidan mai gyaran jikin da za'ai musu. A yanzun kam kasa daurewa Ammie tai ta yayya a musu magana. Fuskarta kuma auke da murmushin da yake ona zuciyarsu ta kalli Sabuwa mai kora bayanin.. ALLAH sarki ai mu wannan abin farin cikinmu ne Sabuwa. Ina kuma taya Yazeed murna da fatan alkairi dan ko bai auri Maanal ba har gobe a yake a gareni tunda ina auren mahaifinsa. Daga ke har Yaya kuma ku daina agama kanku hankali akan Maanal, dan ita dama sam bata bu atar wannan ha in, ta kar a ne kawai dan maida alkairi da hallaci. Har miye abin kace nace da acin rai akan abinda ALLAH ne maiyi kawai. Wani rabon zafi ne da shi musamman ma na aure, idan aka tsananta sai ya kawar da rayuwa kuma ayi abinda ba'a son a bayan ran masu adawar Oh kina nufin zaki kawar damu kenan ki aurama Yazeed ar ki? Hajiya Yaya da kalaman Ammie suka shige ta ta fa a a hargitse. Murmushin Ammie ta sake yi da fa in, Rayuwa da mutuwa ai na ALLAH ne kawai Hajiya. Ina fargar da kune dan ikon ALLAH yafi gaban wasa, ku daina matsawa da yawa dan ALLAH Wannan fa kalamai na Ammie sune suka sake tunzura wutar wannan harmutsi. Dan takai har Hajiya Yaya na i irarin maka Ammie a kotu wai tace zata kashe su ta aurama Yazeed arta. Haka ta kira maigidan tana zazzaga masifa. Ta gama ta fice zuwa gidansu ita da ar uwarta suka sanar da mahaifinsu. Lokacin da su Manaal suka dawo gidan sun tadda komai a hargitse matu a. Ga su Hajiya Basariyya an biki sun dawo daga Abuja ita da yaranta. Aiko ta shiga tai kane-kane tana arama wutar fetur a bayan fage. A yau kam Maanal data jima da mutuwa mai rashin ragi ga duk wanda ya ta ata sai gata ta dawo. Wani irin acin rai ya rufe idanunta. Cikin razananniyar tsawa ta ce, Kai haba ya isa haka mana. Nace ya isa!! Ya isa!!!. Wai shi Yazeed in anyisa da gold ne ko diamond ko tagulla ko azurfa ne? Ko na ta a ce muku dama ina son aurensa ne? Gashi nan ku tambayesa ko sau aya nata amsa masa ina son sa? Shin Yazeed na ta a cewa ina sonka? Ka fa a musu mana ko zasu kama kawunansu. Ni nan da kuke ganina bama Yazeed ba kowanne namiji bana bu ata, domin Manaal ta jima da amincewa zata rayu a matsayinta na MACE kawai batare da kowanne NAMIJI ba takowanne fanni. Kun ta a ganin wanda ya mutu yana son kasancewa da rayayye? Mi matacce zaiyi da rayayye? Ko shi rayayyen mi zaiyi da matacce?. Dan haka idan kunso ku aurama Yazeed mata hu u a rana aya ko duka matan duniya shine zaku birgeni ko kanku dan ALLAH, damuwarku ce wannan. Ku daina fakewa da maganar Yazeed kuna cin zarafin Ammien mu, idan ba haka ba wlhy wlhy zakuga ainahin Maanal kuwa. Dan kaf inku sai kunsha matu ar mamaki ba tsoro yasa ake yaleku ba girmama kaine da darajar shi Yazeed in da Daddy. Saboda ina girmama wa an nan mutanen guda biyu a cikin TARIHINA. Zan iya ce muku sune suka saka zuciyata banbanta sunan MAZA daga jam'in da nai musu. Amma tunda kunce ku baku san kawaici ba kumuje zuwa daga yau a gidan nan ni daku an halak ka fasa. Na fiku iy..... Manaal!! Ammie ta fa a cikin tsawa tana arin ri ota. Kanta ta shiga girgizawa sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tana cigaba da fa in, Ammie ki barni na gaji, nagaji haka nan Ammie. Mi mukayima rayuwa ne? Mi muka tare musu ne? Mi mukayi musu da zafi haka da kowa ke son ganin ya wula anta rayuwarmu, na ta a ce musu bazan rayuwu ba sai da wani NAMIJI ne Ammie?. Basa tunanin kafin su ina dake ba! Basa tunanin ba dole bane sai mace ta rayu da namiji zata amsa sunan mace? Basa tunanin na ha ura da wanda ma yay sanadin kawoni wannan duniyar bisa izinin UBANGIJI balle su, su in nan da ba komai ba a rayuwata. Su in nan da zan iya canjawa da ire-irensu a duk lokacin da naso. A tunaninsu dole-dole sai da sune zan RAYU?! Ko babu su zan rayu Ammie, zan rayu dake ka ai da an uwana kun isheni, kun wadatar dani a wannan rayuwar, bana bu atar kowanne namiji, suje, suje ban bu atarsu..... kuka ya sar e ta sai tari. ull!!! ull!! Jini ya dinga ambulowa ta bakinta ta hanci. Wani irin firgitaccen kukan tashin hankali Ammie ta saki jikinta dake ri e dana Maanal na rawa. Tuni Shahidah, Manaal da Yazeed sun yo kansu a ari. Su kansu su Hajiya Yaya da tawagarta da sauran jama'ar gidan al'amarin ya matu ar firgitasu. Dan a wai-wai suke jin Maanal nada matsalar ciwo mai ha ari, amma basu ta a ganinta a ciwon ba, kai zasu ma iya rantsuwa basu ta a ganin ana aman jini ba sai yau musamman wannan da takeyi ta baki ta hanci. Kowa ya rikice an rasa mai cewa a tafi
Chapter 14 · 0% Book details