← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 183

Sashe 99

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe bayan Ummi, Saratu, da Hibba sun gama karyawa ne.
Shatu da tunda tai sallan asuba ta koma ta konta kan sallayar sai yanzu ta fito.
Tayi wonkanta fes ta ƙenƙesa ado da kolliyar ta ba irin mai ramɓatsau ɗin nan ba.
Komai dai-dai tayi abunta.
Riga da siket ne na Mateyal mai taushin gaske, White Coffee mai kyau.
sai ɗan ƙaramin gyale ta yafa a kanta, cikin nitsuwa ta fito.
A falo ta zauna tare da juyowa ta kalli Ummi dake shirya abinci a Dinning table.
"Ina kwana Ummi".
Tace cikin muryarta Normal.
Cikin kulawa Ummi ta juyo tare da cewa.
"Lafiya lau Shatu. Kin taso kenan".
Murmushi ta É—an yi tare da cewa.
"Ummi meyasa baki tadani ba, kika shiga kitchen da kanki".
Kai ta jinjina tare da É—aukan cup mai É—an girma,
Tea mai kauri ta haÉ—a a ciki kana,
ta taho inda take miƙa mata cup ɗin tayi tare da cewa.
"Gashi amshi kisha, aiki kam ai saida lfy".
Amsa tayi tana murmushi a hankali tace.
"Lfyata lau ai Ummi kawai dai baccin ne ban san meyasa nake ta yinshi ba".
Kai kawai Ummi ta gyaÉ—a mata,
Kana ta juyo tace.
"Hibba kawo mana namu abincin nan muci.

Najiyo Muryar Jamil suna zuwa, kuwa wata ƙil dasu Imran zasu zo".
To tace kana ta É—auko musu nasu Foodflaks É—in da plate and spoons da ta kawo musu.

Jolof É—in taliyace da kifin banÉ—a dasu Kabeji da karas da green beans da dai sauran kayan haÉ—in.
Sai kuma, ferfesun kayan ciki.
A plate É—aya Hibba tasa musu, da ita kana ta sawa Ummi.
Kana tasa musu fork, tare da cewa.
"Bismillah Aunty Shatu sauƙo muci ko".
To tace kana ta sauƙo,
suka fara cin abincin.
Amman ina tayi loma É—aya sai ta kusan 4 minute bata kuma sawa a bakiba.
Sai dai ta shanye tea ɗin ganin hakane yasa Ummi ta ƙara haɗa mata wani shayin.
Shima ta shanye abinta fes, taliyar kuma baifi cokali biyar ba tayi.

Su Jalal kuwa suna shiga suka wuce Dinning area suma sukayi breakfast É—in kana suka fita, sabida hidimomin salla. Domin yau za'ayi hawan daba, Jalal kuma mayene mai zaman kanshi a kan sarrafa, doki, É—an daga Affan sai shi.
Bayan Sheykh a iya sarrafa doki kab Masarautar JoÉ—a .
Amman shi Sheykh ya daÉ—e da cewa shi ya girma da yin wannan sakarcin.

Su Ummi kuwa, kitchen Suka kuma shiga.
Sanin yau tabbas akwai baƙi masu ɗimbin yawa da masarautar Joɗa zata amshi baƙoncinsu.
Domun ƙananan sarakunan wasu garuruwanma duk zasu zo da tawagar su.
Haka yasa suka shiryawa taron haiƙan ƙadaran ko wani Side dake gidan za'ayi abinci a ciccika manyan kuloli a kai fadar Lamiɗo, wani a kai sashin bayi.
Kana kuma ko wani Side da baƙin su.
Haka yasa su Ummi da Saratu da Larai zagewa.
Sukayi abinci kala-kala kana suka ciccika kulolin aka kai fada akai wurin bayi.
Sannan sukayi nasu kuma suka sassaka a Foodflaks masu É—an karen kyau suka jera a Dinning table,
tare da plate, spoons, and forks. Kana sun cika Fridge kuma da drinks kala-kala.
Sun kuma yi Pepper Checken mai zafi na zabbi.

Sai kusan ƙarfe ɗaya suka gama komai,
Su Saratu suka kimtsa komai kana suka tafi.

Su kuma duk suka shiga É—aki da nufin yin wonka.
Tuni zuwa lokacin Masarautar Joɗa ta fara ɗinkewa da baƙi tako wani sashin.

Sheykh Jabeer kuwa, tunda ya tashi.
Ya nufi cikin Garden É—in nan da ababen tarihin masarautar JoÉ—a yake.

Zazzagayawa yakeyi yana dubawa, dan tabbatar da babu wani abun da zai cutar da wani ko wata.
Sabida yasan yau manyan baƙi zasu shigo ciki.
A nuna musu ababen tarihi da dai sauransu.

Gefen da curin da macijiyar nan yake ya nufa.
Ya dudduba ƙofofin ba hayaƙi ba komai.
Sai dai in mutun ya kasa kunne zaiji sautin numfashin macijiyar ka da ƴan ƙanana kuka irin na ƙananan macizai.
A hankali ya ƙara matsowa bakin curin. Cikin nitsuwa yayi gyaran murya.
sai kuma yaji sautin kukansu da kuma numfashin uwar ya ƙaru sosai.
A hankali yace.
"Assalamu alaikum, ya ke wannan halittar Ubangijin sammai da ƙasai".
Gyara tsayuwarshi yayi jin numfashin na ƙara matsowa.
A hankali yace.
"Ba cewa nayi ki fitoba, nazo in roƙeki ne kamar yadda Manzon Allah ya sanar mana, dukkan halitta tanaji.
Kuma ina kaga wani abun cutarwa a gidanka ka haÉ—ashi da Allah da Manzonsa kace ya fita.
Manzon Allah ya bamu tabbacin.
Muddin ba mai cutarwa bane zai fita.
In yaƙi fita kuwa ka kasheshi".
ÆŠan zagaitawa yayi jin kukansu ya kuma tsananta, cikin sanyi yace.
"Ni bazan roƙeku kan ku fita ku bar muhallin zamanku da ban san tsawon shekara nawa kuke rayuwa a wurinba.
Kuma bansan dalilin zamanku a wurinba.
Shiyasa bazance ku bar Masarautar JoÉ—a ba.
Kuma bazan kasheku ba,
Sai dai roƙana garemu.
Munada baƙi a Masarautar Joɗa kuma yau zasu shigo, dan Allah da Manzonsa, kada ku fito ku baiyana kanku ga baƙinmu kada ku razana mana baƙi kada ku cutar mana da mutanenmu.
Kuyi zamanku a muhallin ku".

Shiru sukayi tsit alamun sun jishi kuma sun gamsu".
Fahimtar hakane yasashi cewa.
"Na barku lfy".
Yana faÉ—in haka ya juya, LamiÉ—o da Galadima ya gani tsaye a bayanshi.
Murmushi sukayi tare da matsowa inda suke.
Galadima ne yace.
"Kada ka damu da fitarshi da zamanshi da yaranshi
Domin kai ke ganinshi a nan, amman duk in da wani mugu ya shigo masarautar JoÉ—a da nufin yiwa LamiÉ—o wani abun zai ganta da yaranta a gabanshi.

Amman wanda yake jinin wannan gidan bazai ganshiba.
In kaga mutun ya ganshi saida sahalewar LamiÉ—o".
Shiru yayi yana kallonsu.
Shi kuwa LamiÉ—o a hankali yace.
"A ƙalla yafi shekaru ɗari biyu da arba'in a cikin wannan curi a wannan Masarautar tun zamanin baban kakana Joɗo yake nan, ba kuma tsafi bane, ba sihiri bane, kamar yadda kowa ya sani shi maciji curi gidan zamansa ne, to bulalin caɗin masarautar Joɗa kuwa suma asali nan suke da zama curin ne ya binnesu, kana macijiyar ta shiga ciki, shine ma dalilin hana shaɗi to sai dai lokaci zuwa lokaci in an sarki maici yazo wurin yayi sallama macijiyar kan fito, in zata fito takan fito da balalin a binɗinta. Sai daga baya ta fara fita ita da ƴaƴanta suna yawo cikin masarautar Joɗa ne, muka gane yunwa ke sata fitowa, sai ta shiga cikin kaji tasha kwayaye ta haɗi ƙananan kaji.
Lokacin da muka fuskanci haka sai muka fara kawo mata kwai a matsayin abincinta.
Daga baya muka fahimci in mutun ya shigo da mugun nufi tana razanashi".
Taɓa bakinshi yayi cikin rashin yarda bare gamsuwa yace.
"Ni dai ban tambayeka ba, inma tsafine kaidashi Ni nan Muhammad Jabeer bani dalaifi a ciki nayi-iya yina in rabaku da wannan tsarabe-tsaraben na masarauta kun ƙiya".
Ya ƙarishe mgnar yana juyawa ya nufi wurin da tsuntsayen wurin suke.
Gefenda aku yake ya nufa.
Tana ganinshi ta kaÉ—an fiffigenta tare da cewa.
"Sheykh Jabeer ya dawo".
Murmushi yayi tare da shafa kan akun yace.
"Ya dai tsuntsuwa mai daraja ya gida".
Cikin irin mgnarsu na Ali tace.
"Lfy Sheykh ya madina garin Manzon Allah".
Ta ƙarishe mgnar tana kaɗa kanta da jelarta alamun yiwa sauran tsuntsaye rigimar ance mata tsuntsuwa mai daraja.
Murmushi mai faÉ—in Sheykh yayi ganin.
ÆŠawisun nan tazo gabanshi ta tsaya ta buÉ—e dogon jelanta ta kaÉ—ashi tayi sama dashi.
har yana taɓa gemunshi cikin sanyi yace.
"A a kekyawar tsuntsuwa mai kyan ado da tafiya".
A hankali ta karkaÉ—a jelan kana ta fara zagayashi.
Tana nuna mishi kyan tafiyar.
Su kuwa sauran tsuntsaye kuka suka farayi.
Murmushi mai faÉ—i ya kumayi tare da cewa.
"Tsuntsaye masu zaƙin murya da sauƙin firewa".
Aifa nan suka tashi sama suna shawagi a wurin.
A hankali ya juyo ya kalli tarin tattabarun dake gabanshi mazan ciki suna ƙotowa wa matansu.
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Iyayen soyayya duk cikin tsuntsaye bayaku a soyayya".
Ai sai suka fara irin kukansu nan guggdu-gudduu guuu".
A hankali ya fita yankin tsuntsayen bakin ƙoramar dake gudana a tsakiyar Garden ɗin ya nufa.
Inda agwagin ruwa keta shawagi a bakin wurin.

Zama yayi yana nazartan lamuran halittun É—an adam.
Ko wanne halitta akwai mace akwai na miji.
Kuma ko wanne halitta namiji baya iya rayuwa saida macce.
To shi menene matsalarsa da duk manyan likitocin duniya suka kasa ganowa, kowa sai yace mishi lafiyarshi lau.
Shi kuma yasan baida lfyar maza, tunda bai taɓa jin wani abu ya motsa a zuciyarshi bare yasa wani sashi na jikinsa motsawa ba yana dai jin shi wasu lokutan a namiji jim kadan lbri zai sauya.
Gefenshi LamiÉ—o da Galadima sukazo suka zauna.
Bisa wani carpet da hadimin da ya shigo yanzu ya shimfiÉ—a musu.
Yana fita wani ya shigo da kayan abinci.
Cikin kula LamiÉ—o yace.
"Taho nan muci abinci Ustazu".
Hannunshi yasa ya shafa cikinsa.
Sosai yakejin yunwa hakane ya sashi gyara zama nan sukaci abinci su ukum su.

Gani. Ƙarfe ɗaya tayine, lokacin salla ya ƙara to.
Ga ɓaki nata shigowa masarautar Joɗa.
Yasa suka tafi.

Shi yana shigowa bathroom ya wuce. Wonka ya fesa mai rai da lfy kana yayi al'wala.
Kana ya fito ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da gajeren wondo 3 qtr yasaka kana yasa tattausar rigar mai guntun hannun. Duk kalarsu Royal blue ne, sai ya É—auka farar jallabiya. Fara mai É—an karen kyau.
Kana yasa baƙar al'kyabbar jikinshi tare, dasa hirami mai fari da ja, yayinda hakama takalmanshi fari da ja.

Wasu sabbin turaran da ya seyo ya fesa a kan sabbin kayan da ya saka masu É—an karen kyau.

Wani irin ƙamshi yakeyi mai daɗin shaƙa.

A hankali ya fito falonshi, kallon abinci dake jere kan Dinnin yayi kana ya wuce ya fita.
A falon ya samu su Jalal da alamun da al'wala a jikinsu.
Can falon Shatu yajiyo muryarta tana kiran Hibba dake É—akin Mama.
Sai yanzu da yaji muryarta ne ma shi ya tuno da ita a gidan.
Kai ya kaɗa yasa ƙannenshi a gaba suka tafi.
Suna isa masallacin akayi sallan azahar.

Ƙarfe ɗaya da mintu arba'in suka firfito masallacin da ya cika yayi maƙil mafi akasarin matasa suna cikin shigar sukuwane.
Chapter 99 · 0% Book details