← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 183

Sashe 151

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tukunyar kwan nan ta buɗe ganin sun dafu ne yasa ta sauƙesu, ta tsanesu kana ta sasu a plate.
É—an motsa taliyar da dankalin tayi kai ta gyaÉ—a ganin yayi yadda takeso naman ya wadaci girkin sosai,
Kwan ta fara ɓarewa, saida ta baresu fes kana, ta rufesu gefe, buɗe tukunyar taliyar tayi ganin yayi dai-dai da Dan ruwa-ruwane yasa ta ɗauki caras da al'basan da ta yanka tare da dafaffan kwai ɗin ta sasu ciki.
sannan ta rufe ɓol-ɓol yake wani kekkyawan ɓararraka.
Wata kekkyawar Foodflaks mai marfin glass ta ɗauko ta fara ɗiban taliyar gefe-gefe tana sawa a wani kekkyawan kwano gudun kada garin sawa a Foodflaks ɗin ya ɗan ɓata kular, daga cikin kwanon ne ta juye a kular sannan ta dawo ta yaɗe al'basa da caras da kwan da namomin ta jerasu saman kular kana tasa marfin ta rufe.
Sosai tsarin yadda tasa abincin yayi masifar kyau.
Sauran na tukunyar ta sawa Sara a plate da kwai É—aya da Nama dasu karas É—in sauran kuma ta sawa Ummi shi a wata Æ´ar kula.
Cikin Murmushin Ummi tace.
"Gsky kam Aysha koda a ƙoshe nake zanci girkin nan".
Murmushi tayi tare da ɗauko lfaks ɗinshi da Ummi tasa mishi tea, kasan cewar ɗan ƙaramine yasa ta jerashi kan tray kusa da kular,
ferfesun da Ummi tayi ta ɗan ɗuma tasa mishi a ƙaramar kula, kana tasa plate, cup, tea spoon and fork. ta kimtsa komai, kana ta tura tray'n can gefe, sannan ta matso kusa da Ummi tana cewa.
"Ummi miyan me zakiyi mana".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ɗanyar ƙuɓewa".
Da sauri tace.
"Ummi yaushe zamuyi miyar kase".
Cikin dariya tace.
"In sha Allah gobe zamuyi".
Allah ya kaimu tace cikin jin daÉ—i.

A hankali yayi parking gab da bakin ƙofar falon nasu, Allah ya sani ya gaji ga yunwa.
A hankali ya fito, dai-dai lokacin kuma Jamil da Affan suka iso wurin.
Affan ne yasa hannun ya amsar mishi jakar system É—inshi.
Tare da ce mishi.
"Sannu da dawowa Malam".
Kai ya gyaÉ—a musu, yayi gaba kana suka bishi a baya.
Da sallama a bakinshi ya shiga.
Suna shiga kai tsaye Side É—insa ya wuce, Affan na biye dashi a baya.
Jamil kuwa kitchin ya nufa yana cewa.
"Salamu alaikum Ummi".
Da sauri ya iso kusa da Ummi.
"Ummi me kuke dafawa haka naketa jin ƙamshi ya ƙare zancen yana jan kular dake kusa da Ummi.
Yana buÉ—e wa yace.
"Kai badon a ƙoshe nakeba da nayi tafiyar ruwa da kular nan".
Dariya Ummi tayi shi kuwa cewa yayi.
"Dan Allah wa akawa wannan girkin?".
Da sauri Ummi tace.
"Hammanku".
Juyowa yayi ya kalli Aysha tare da cewa.
"Uhum son kai. To ya dawo sai a kai mishi tare muka shigo".
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
"Ba ni naiba Ummi ce ta mishi".
Dariya sukayi duka, ita kuwa Ummi kallon Aysha tayi tare da cewa.
"To É—auki ki kai mishi, kinga fa É—aya tayi".

To tace tare da É—aukan tray'n ta nufi Side É—insa.

Ummi da Sara kuma sukaci gaba da aiki Jamil na zuba musu surutu.

A hankali tayi sallama tare da kutsa kai ciki jin muryar Affan a ciki yana surutu shi É—aya kai kace zarerrene shi kuwa Sheykh bakace yana falon bama sai dai kaji yana cewa.
"Uhmm, uhum, ehh, ko?".
Iya amsar kenan.
Ganin suna tsakiyar falon ne yasa ta iso tsakiyar falon, a hankali ta sunkuyo ta ajiye tray'n bisa santa table dake tsakiyar falon.
A hankali ya ɗago idonshi ya zubasu kanta, da sauri ya juyo ya kalli Affan ajiyan zuciya ya sauƙe ganin Affan ba ita yake kalloba duk da ita yakewa mgn, amman wayarshi yake latsawa.
wuyan rigarta da yake mai faɗine ya samu nasarar baiyana raɓin ƙirjinta a woje sabida sulewar da gyalenta yayi.
murmushi ta É—anyi jin Affan na cewa.
"Ƙaro plate da spoon Aunty Aysha nima nan yunwa nakeji".
Cikin tsokana tace.
"Ina Maman Amal".
cikin kwaɓe fuska yace.
"Uhum ita kuwa yar zuriya tana can wai suna auren Æ´ar autarsu Zeenart".
miƙewa tayi kana ta ɗan kalli Ya Sheykh haɗe fuska yayi tare dasa yatsarshi kan ƙirjinshi yaja kana ya nuna mata ƙirjinta da idonshi sannan ya nuna mata Affan da babbar yatsarshi wanda yayi alamun kamar gashin girarsa yake kwantawa.
Da sauri ta janye idonta kanshi kana ta gyara gyalenta.
Sannan ta juya ta É—auko plate sannan tazo ta zuba musu.

Kana ta juya ta fita sabida wani irin mayataccen kallo da Ya Sheykh ke cilla mata.

A hankali Sheykh ya lumshe idonshi lokacin da yasa abincin a bakinsa taunawar da yayi yaji É—an-danon ya sashi jin kunnenshi na amsa amo.
Affan kuma haÉ—iye lomar dake bakinshi yayi tare da cewa.
"Kai abincin yayi daÉ—i Malam jolof É—in kwai ne ko na dankali ko na taliya ko daima jolof É—in nama ne?".
Murmushi Sheykh yayi tare da kurban tea kana yace.
"Ko zan riƙe maka takalminka kaje kayi tambaya ne?".
Dariya Affan yayi tare da cewa.
"Wallahi ba santi bane".
hannusa yasa ya ɗan make ƙeyan Affan kana yace.
"Kai ana zafi a garin nan ƙara gudun A/C'n nan ɗazu da zan fita na rage."
Mikewa yayi tare da cewa.
"Gsky ana zafi koda yake naji ɗazu Gimbiya Aminatu na cewa yauwa kwana goma kenan ba'ayi ruwan samaba jiya har roƙon ruwa aka fita".
Ya ƙare zancen yana dawowa ya zauna kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Har kwana goma, to Allah ya bamu mai Al'barka mai cike da ni'imomi".
Amin Amin Affan yace kana sukaci gaba da cin abinci.

Ita kuwa Aysha kitchin ta koma, nan suka ƙarashe aikin kana suka shirya komai a Dinning table, sannan Sara ta tafi.
Ummi kuwa da Jamil suka zauna a falo.
Ita kuwa Aysha bedroom É—inta ta, shiga.
Bathroom ta shige sabida, wani shegen fitinenne fitsarin da takeji.

Bisa toilet É—in ta zauna tare da lumshe idanunta, sabida jin daÉ—in juye nauyin mararta da takeyi.
Bayan ta gamane, tayi amfani ruwan É—umi.
Sai kuma ta kwabe dan zafin da takeji tace bari ta ɗan watsa ruwan sanyi lumshe idonta tayi lokacin da ruwan sanyin ya sauƙo jikinta, kana dai-dai lokacin ta tuno mafarkin da tayi da safiyar yau, da sauri ta rumtse idanunta gam sabida a fili take ganin yadda Sheykh yayi ta murzata a mafarkin da kuma irin kukan da tayi sabida azabar da ya azabar da ita da sauri ta ware idon da kyau sabida sai takega kamar zai shigo yanzune ya ritsa da ita haka yasa taci gaba da wonkon da sauri-sauri.

Cikin tsananin isa da izza da tsaurin ido, take taku har zuwa tsakiyar falon kana hadimanta na Binta a baya.
Tsakiyar falon ta tsaya tare da watsawa Ummi da Jamil ido dogon tsaki taja tare da cewa.
"Ina yake É—an masu fiffigen!?".
Da sauri Jamil ya miƙa tsaye tare da watsa mata wani irin mugun kallo mai cike da tsana yace.
"Baya buƙatar ganin irinku da ko sallama baku iyaba".
Cikin tsawa da É—aga murya tace.
"Rufe min baki ƙaramin kwaro, ka bari inyi da shi jan wuyan naku".

Da sauri Sheykh ya miƙe tsaye jiyo muryar Gimbiya Saudatu a tsakiyar falonshi.
Affan ma miƙewa yayi da sauri kana yabi bayan Sheykh daya nufi falon da sassarfa.

Yana fitowa Gimbiya Saudatu ta gyara tsayuwarta tare da buÉ—e al'kyabbar jikinta kana tace.
"Yauwa al'huda-huda sarkin karatu.
Zo nan zo ka gayawa wannan ɗan tayin ƙanin naka cewa.
Duk lalacin mutun ya iya sallama amman banda tsuntsaye su sai dai su gani anayi, gwarama tsuntsun da ba zunibi ne ya maidashi tsuntsuwar ba dama haka Allah ya halicc...".
Cikin wani irin tsananin tafasan zuciya da tuƙuki da ciwo a rai.
Sheykh yayi mata wani razanenne tsawan da saida tayi tsalle ta koma baya kaÉ—an.
Tsawar daya danna matane yasa Aysha fito da sauri tana mai gyara É—aurin É—an kwalin doguwar abayar da tasa yanzu.
Cikin rawan jiki yake taku har gabanta.
Ummi da Affan da Jamil kansu jikinsu kerma yakeyi.

Jalal dake Side É—in su ma yajiyo sautin muryarsa hakane yasa ya nufo falon da sauri.

Cikin azabar fushi ya nunata da Æ´ar yatsarshi manuniya murya na rawa yace.
"Duk tsuntsuwar da kika gani Allah yasan da zamanta, ki kuma sanni wannan tsuntsuwar ta fiki daraja har gaban Allah".
Cikin jajir cewa da ƙarfin hali ta ɗan ja da baya tare da cewa.
"Eh lallai kam ta fini har gaban Allah mana tunda girman zunubanta da jafa'inta yasa Allah ya nuna mana ikonsa da aya a kanta ya sauya mata halitta daga mutun zuwa tsu..".
Wani irin zabura Ummi, Affan, Jamil, da hadiman Gimbiya Saudatu
Sukayi sabida wani irin azabebben ihu da ta kurma da karfi sabida wasu irin gigitattun tagwayen maruka da Sheykh ya yarfa mata da hannunshi.
Wanda sukayi nasarar tafiya da jinta da ganinta.
Kanta ya sake nufa da azama alamun zai tabketa da iyakar iyawarsa
Cikin rawan jiki Ummi tace.
"Sheykh kayi haƙuri barta kasan hannunka".
Ina wani marin ya kuma yarfa mata wanda saida taji wani fitsari ya tsarto mata.
Ihun data kurma yayi dai-dai da kife kanta da tayi da jikin kujera.

Cikin wani irin azama da sauri haÉ—i da kiÉ—ima Aysha tayi sauri ta nufi gaban Sheykh sabida ganin baya cikin hayyacina.
Affan da Jamil da sukayi nufin riƙeshi ne ya yarfawa maruka wanda yasa suka ja da baya.

Cikin azama tasha gabanshi tare dasa hannunta ta riƙo hannunshi da ya ɗago zai mari Gimbiya Saudatu, cikin azaban fushi ya juyo ya kalleta da rinannun idanunshi.
Da sauri ta kuma ƙara riƙe hannunshi tare da matsoshi kana murya na rawa tace.
"Yan Sheykh! Kayi haƙuri".
Fusge hannunshi yayi da ƙarfi ya nufi kan Gimbiya Saudatu domin idonshi ya rufe rib baya ji baya gani kamar yadda itama Gimbiya Saudatu idonta da kunnenta suka dena aiki kana fitsari ke tsiyayo mata.
Da sauri Aysha ta kuma shan gabansa, kawai sai ta faÉ—a jikinshi ta ruggumeshi gam-gam a jikinta,
cikin rauni take cewa.
"Yah Sheykh ka bari, kada ka kulata Please Yah Sheykhhhh kada ka sake barin hannunka mai daraja da kullum yake cikin taɓa al'ƙur'ani mai girma ya taɓa fuskarta kada ka bari fuskarta ta samu darajar da hannunka zai taɓata.
Chapter 151 · 0% Book details