Sashe 37
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna.
Kana ya fuskanci ƙannen nashi da kyau.
Jalal ne ya É—an sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya É—an rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci É—an uwan nasu,
Cikin yin fiki-fiki da idanu yace.
"Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?".
Alhamdulillah, yace mushi a taƙaice, kana ya ɗan gyara, hiramin dake bisa kafaɗunshi.
Jalal ne ya É—anyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata,
Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake.
Cikin sanyi yace.
"Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t
yasu Sitti?".
Ido ya É—an kauda kana yace .
"Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?".
Kanshi ya É—an jujjuya kana a hankali yace.
"Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sauƙi ya zame mana ɗa'a muce, da sauƙin, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sauƙin, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita".
Ya ƙarishe mgnar tamkar zaiyi kuka,
ganin hakane yasa Jabeer ɗan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ƙunci ko baƙinci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya ɗauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya miƙe cikin kula ya kallesu, murya a ɗan macce yace.
"Kuzu kuci abinci".
To sukace baki É—ayansu, kana duk suka nufi, dinning table É—in.
Wanda yake cike da abinci kala-kala.
Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake buƙatar ci,
Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici.
Ya dai zauna yana kallonsu,
Ummi kuwa, tana gefenshi.
Kanshi ya É—an juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart,
É—an gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa.
"Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?".
hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya.
Cikin haÉ—e fuska Haroon yace.
"Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an liƙa maka jaraba".
Jamil ne yayi Æ´ar dariya tare da cewa.
"Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi".
Jalal ne ya É—an tsuke fuskarsa tare da cewa.
"Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin Æ´a mace bane, jikanshi nefa ta wurin É—a namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?".
Ummi ce taja wani dogon ajiyan zuciya tare da cewa.
"Uhummm ta yaro kyau take bata ƙarko, to kai Jalaluddin, yanzu Jafar da aka bashi Galadima, wani hali yake ciki? Tun randa aka naɗa masa sarautar me mutane suke kallon ya zama? Dukfa duniya kallon majanun akeyiwa Jafar".
Juwairiyya ce ta É—an rumtse idonta tare da cewa.
"Ni banyi fataba, banso a sake bawa Kowa wani mulkin da nasan baza'a barku lfy ba, shi LamiÉ—o, meyasa ko Æ´aÆ´an nashi babu wanda ya bawa mulkin komai?".
Da sauri Ummi tace.
"Sabida muddin yace zai basu sarautu, to wasu zasu hallaka wasu".
Cikin daƙilewa Jalal yace.
"Ok shine sai ya zaɓi ƴan ɗakinmu a matakan zakarorin gwajin dafi? Ya bawa Ya Jafar Galadima, yaga yadda aka medashi dare ɗaya, da rashi da bazamu samu madadinshiba a duniya, an cire hankalin mahaifinmu a kanmu, sannan ya kuma bawa Hamma Jabeer wani mulkin, salon a sabautashi kenan, nest target nasu kuna, wato a kanshi ne?".
Shiru sukayi jin Jabeer na cewa.
"Azzannu zambu walau kana haƙƙun, na haneku da irin waɗanan zantukan, babu wanda ya isa, ya cutar da wani sai Allah, domin shine mai rayawa, kuma mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, mai cuta mai waraka. Ummi har kema, ya zakiyi ki zauna kina gaya musu hakan, to waye zai cutar damu, acikin ahlinmu, daga ƙannen mahaifinmu fa, sai ƙannen kakanmu, sai matasansu da jikokinsu, sai kuma ƴan uwanmu, dan Allah ku bar munanawa mutane zato."
Juwairiyya ce ta É—an girgiza kai.
Shi kuwa Jabeer, cikin bada umarni yace.
"Juwairiyya jeki duba Ya Jafar, nasan zuwa yanzu ya tashi daga baccin."
To tace, kana ta miƙe ta nufi tsakiyar falon. da sauri ta tsaya tare da ɗan raɓawa gefe, sabida ganin Gimbiya Saudatu, na tsakiyar falon.
Da sauri ta É—an rusuna tare da cewa,
"Barka da fitowa Gimbiya Saudatu".
Zama tayi bisa kujerar da Jabeer ke zama, É—aura kafarta tayi É—aya kan É—aya.
Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta.
Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ƙasaita tace.
"Kai Jabeer!."
Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi,
cikin rawan jiki da tsoro tayi ƙasa da murya tare da cewa.
"Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta."
Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu.
"Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka".
Still bai buɗe idanunshi bama, bare ya amsa ko yunƙurin tashi,
sai dai laɓɓan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.
Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ƙasaita tace.
"Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun Fulɓe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi".
Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba'in.
Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen.
Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsabura.
Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken.
da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an riƙe mishi, hannunshi.
ganin Hamma Jabeer ɗinsune ya damƙi hannunshi ne ya sashi, taune lips ɗinshi da masifan karfi.
Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzuƙa Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.
Ummi kuwa cikin rawan murya da tsoro da firgici ta kallesu murya na rawa, tace.
"Dan Allah Jabeer, kaje, tashi muje ka amsa kiranta dan Allah badon niba, dan darajar Manzon Allah".
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin zubewa kan guiwowinta,
Jin kalaman da tayi mishi da gane nufinta na rusuna mushine ya sashi saurin miƙewa tsaye.
da sauri suma duk suka miƙe tsaye.
Gyara kekyawar al'kyabbar jikinshi yayi wacce take ta limamaice bawai ta sarautaba, jam hiraminshi yayi ya rufe sajenshi da kyau ya rage iya shatin fuskarshi dan yasan dole tazo da hadimanta mata.
Jalal ne ya tsaya gefen damanshi, kana Jamil a gefen hagunshi, Haroon kuwa na bayanshi, Jakadiyarsu kuwa tana gaba tanayi musu jagora.
A haka suka fara taki kan stpes ɗin sauƙowa daga kan dinning area ɗin, wani irin taku sukeyi mai cike da ƙasaita da kwarjini. Yana tsakiyarsu tamkar sarki da fadawanshi.
A haka suka nufo tsakiyar babban falon da ya kai wasu faluka huÉ—u.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu, wani irin hushi da numfarfashi takeyi tamkar wacce tayi gudun fanfalaƙi,
cikin izaya da isa, take zaune bisa mazauninshi.
Tare da cewa.
"Ina karen Larabawan yakene, Dan kan uwark?".
Bata ƙarishe mgnar tataba, sabida ganinsu sun nufota gadan-gadan, wani irin kwarjini yayi mata,
wanda yasa ta haÉ—iye ragowar mgnar tata,
shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin wani irin taku naƙasaita suka karaso tsakiyar falon.
Ido ta zuba musu kana cikin tijara tace.
"Me zaka zo ka tsaya min a ka, ka zauna inada mgna da kai".
Cikin wata iriyar dakekkiyar murya mai cike da ƙasaita yace.
"Ai ba sai kince na zaunaba, dama dole in zauna, tunda ni ba bawanki bane, bazan tsaya a kankiba, sabida Ni ba dogari bane".
Ido ta zazzaro woje alamun tarin mamaki, ajiyan zuciya ta sauke a ranta tace.
"Ehe mai jajayen kunnuwa, uwarka zanci".
Shi kuwa Jabeer, wani irin taku yayi mai cike da izza, bisa kujerar dake fuskantar wacce take zaune a kai ya zauna, da sauri ta tsareshi da ido tare da cewa.
"Kai ina sama kana sama, haka aka koya maka irin tasu tarbiyar ta larabawan kenan".
Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura ya ɗaurs kan ɗaya, kana ya gyara zamanshi da kyau,
cikin muryar ƙasaita yace.
"Ki dena yimin ihu a kai, nan ba fadar masarautar waÉ—ancan surutattun bane, nan fadace mai daraja masarautar JoÉ—a ce, kiyi hattara da lafuzanki, na baki mituna biyar daga cikin wunin yau gaya min damuwarki in baki mgninta".
Jakadiya dai gaba É—aya jikinta rawa yakeyi.
Haroon kuwa, bayan kujerar da Jabeer ke zaune ya tsaya,
Jalal kuma yana gefenshi hakama Jamil.
Juwairiyya kuwa, tana inda take tun É—azu.