← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 183

Sashe 62

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laminu kuwa tuni yayi gaba yana É—aukar shigowarsu.
Sabida aikinshi na jarida dama neman rohotone aikinshi.

Sanadin saurin da suke ɗanyi ne yakesa al'kyabbar jikinshi ɗan buɗewa tana bazuwa hakan sai ya zama kamar ƙasaitace tasa yake wannan abun a wurin mai kallonshi.

Gaba daya duk ta inda suka zo wucewa, sai ya É—aga hannunshi duka biyu, yayi musu sallama tare da cewa.
"Ya mai jiki?".
In sunce da sauƙi. Sai yace.
"Laah Ba'as É—uhhuru in sha Allah".
Duk inda suka gilma sai an bisu da ido. Especially Jabeer da babu wanda zai kalleshi bai ƙaraba

Tuni labari ya kai ga kunnen Dim din asibitin.

Lokaci É—aya ya kikkira DOCTOR'S É—in ta wayar salulu ya sanar musu su kimtsa komai su kula da kowa yadda ya dace.
Mai martaba LamiÉ—o na cikin asibitin.

Ita kuwa Shatu tana haurawa sama.
Ido take É—agawa ta duba sunan Office da mai Office É—in Office na forko taga musulmine haka yasa ta kutsa kai ciki.
Zaune yake babu kowa sabida duk majinyatan sun tafi.
Wasu an duba su, wasu kuma korarsu akayi da cewa yau half day ne, sabida haka su tafi.
Da mamaki ya É—ago kanshi jin an shigo mishi Office babu sallama. Da sauri yace.
"Waye?".
Sabida cikin shigar yan matan larabawa take.
Arabian gawd ne mai masifar kyau da taushi a jikinta wanda samanshi yake a dai-dai jikinta ƙasa shi kuma yake a buɗe, wasu irin duwatsune a jikin rigar tun daga sama har ƙasa sai wal-wali sukeyi suna ɗaukar ido.
Tayi rolling kanta da É—an kwalin rigar fuskarta ta fito ras a ciki.
Wasu takalmi Golding color ne masu ɗan tudu dai-dai misali sai Ƴar ma dai-daiciyar hand bang mai masifar kyau shima Golding color ne, sai wayarta ƙirar iPhone 11.
Fuskarta babu kolliya sai dai duk da haka bai hanata yin kyau ba gashin girarta ya konta lib-lib. Sai dai kuma ta rufe fuskar da tattausan Niƙab sai dai bashi da duhu sosai.
To wannane ya hana Dr Salim ganin fuskanta, ita kuwa Shatu cikin tsananin ɓacin rai da zafin tozarcin da akayi wa yan uwanta tace.
"Dr Salim".
Cikin Mamaki yace.
"Na'am". Yatsarta tasa tana nuna mishi maraba da baƙi ta wondon shi, cikin rauni tace.
"Dr Salim na tabbatar kai musulmine, kuma nasan kasan cew manzon Allah yace shi musulmi ɗan uwan musulmine! Shin ko ka mance hakane, da ka kasa taimakawa yan uwanka musulmai da kafurai sukayi musu rauni akazo aka watsar dasu a nan kuma kuka ƙi dubasu meyasa, ko dan kawai sun kasance fulanin dajine laifinsu?".
Cikin sanyi Dr Salim yace.
"Wallahi umarni ne ba'a bamuba daga sama".
Cikin tafasar zuciya tace.
"Umarni wanne irin umarni kuma zaku jira bayan Allah da Manzonsa sun baku dukkan dama da umarnin taimakawa É—an uwanku musulmi muddin kunada dama".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Dim É—inmu ne ya hanamu dubasu".
Cikin kufula tace.
"Kan kafurar uwarshi! wato a cikin asibitima sai an mana ƙabilan ci, dan Allah Dr kuje ku taimakawa bayin Allancan".

Cikin jin ƙarfin guiwa ya juya, ya fita, ya nufi can.
Ita kuma haka ta rinƙa bin duk Office ɗin da taga na musulmi ne tana shiga.

Tawagar Lamiɗo kuwa suna isa baƙin wani tamfatsetsen Office Sheykh Jabeer, ya ɗan kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Ni bari in shiga office na, ko mutun biyar in duba kafin ku gama zagayawa".
Cikin gamsuwa da hakan LamiÉ—o yace.
"To bisimilla".
Nan ya nufi babban barandar da Nurses suke tare a wurin maza da mata.
Jamil kuma na biye dashi da System É—inshi a hannunshi. Hakama Haroon ya biyoshi.

Nurses ɗin kuwa suna hangoshi duk suka mimmiƙe tare da cewa.
"Sir barka da zuwa".
Barka dai yake ce musu tare da ratsawa yana wucewa.
Su kuwa sun taru a wurin ne dan tawagar Lamiɗo na wucewa su sauƙa ƙasa su duba Fulanin nan kamar yadda Dim ɗinsu ya basu umarni sabida kada Lamiɗo ya gansu a yashe a ƙasa yasan abun bazai mishi daɗi ba.
Suna ganin ya shiga Office É—in suka juya da nufin zasu tafin sai kuma suka tsaya jiyo muryar Shatu na cewa.
"Ku tsaya ina kuma zakuje? Baku da aikin yi ko? Amman da yake ba taimako ne a zuƙatankuba kun bar bayin Allah a wulaƙance ko?".
Cikin masifar Nurses da su ba komaiba sai iya ciwa mutane zarafi a hatsale tace.
"Ke kuma waye".
Kallonta Shatu tayi sama da ƙasa tare da kallon rubutun dake saman aljihun rigarta ganin sunan arniyace ga kai da gashin doki ga uban faratu kamar na jaki yasa taja tsaki tare da cewa.
"Banyi da keba, da masu hijabi nake mgn".
Yadda tayi mgnar da ƙarfi ne yasa, su Jabeer ma jiyo muryarta,
wanda shi kuwa zuwa yanzu yana jin zuciyarshi zata iya faɗowa ƙasa dan bugawar da takeyi.
Jin muryar wata nurse É—in tana cewa.
"Wannan ma ai iskanci ne".
Cikin taɓe fuska ya nunawa Jalal yatsa alamun ya buɗe mushi ƙofar yaga meke faruwa da suka cika mishi kunne da hayaniya.
Da sauri Haroon yabiyo bayan Jalal suka fito.

Shi kuma Sheykh Jabeer komawa yayi ya jingina da jikin kujerar shi.
Tare da rage girman idonshi ya zubawa bayan Shatu ido.

Ita kuwa Shatu cikin zafi ta kalli arniyar nan da tace mata wannan ma ai iskanci ne tace.
"A kul kada ki kuskura ki sake kira min iskanci a gabana, ke kika sanshi ba niba, ke kika taso cikinsa".
Sai kuma ta juya harce cikin fillanci tace.
"Shegu masu wari".
Sai kuma ta juyo ta fuskancesu da kyau, Haroon kuwa da Jalal ido suka zuba mata cikin mamaki.
Shima Jabeer idon ya zuba mata so yake yaji meyasata ihun nan.
Ita kuwa Shatu cikin sanyi ta fuskanci musulman ciki murya a É—an tashe tace.
"Kada dai ku manta nace daku nakeyi masu hijabi sabida nasan kun san ma'anar Al'muslim akul muslim. Kun kuma san girma da daraja da kuma wanda ya faÉ—i hakan".
Cikin gamsuwa duk suka ɗaga mata kai, rai a ƙuntace tace.
"To meyasa kuka bar waɗanan can bayin Allah'n a tozarce a yashe a maraba da baƙi koda dreesing na raunuka su bakuyi musuba, menene laifinsu, kawai dan sun kasance fulanin daji, shiyasa DOCTOR'S da Nurse's kab bazaku jiƙansu ba".
Cikin sanyi É—aya daga cikinsu tace.
"Ayyah yanzuma can zamu tafi. Sabida sai yanzu Dim ya bamu umarni".
Wani dogon tsaki taja tare da cewa.
"Daga baya kenan yau kwanansu goma cib babu wanda daya dubasu, sai da suka gama jigata".
Tsaki arnan ciki sukaja tare da juyawa suka tafi.

A hankali Jalal ya juyo ya kalli Hammanshi da yake cewa.
"Rufe min ƙofa wannan ta cika min kunne da ihu".
Da sauri yace to.
Haroon kuwa murmushi yayi tare da juyowa zai shiga ciki kafin Jalal ya rufe ƙofar.
Da sauri ta juyo jin takun mutun a bayanta,
Cikin muryar umarni tace wa Jalal.
"Kai mai kamar larabawa tsaya kada ka rufe ƙofar, Office ɗin na arne ne ko musulmi?".
Cikin dariya Haroon yace.
"Na musulmi ne".
Taku ta fara tare da nufo cikin Office É—in.
Wani irin sunkuyawa Jabeer yayi ya kifa ƙirjinshi kan babban Glass table dake gabanshi, sabida ji yakeyi tamkar kan zuciyarshi take taku. Ji yakeyi zuciyarshi zata fashe tsabar yadda take bugawa da azaban ƙarfi yadda take ƙara matsoshi haka bugawa zuciyarshi ke ƙara tsananta.
Cikin mamaki ta zubawa Office É—in ido. Office ne mai matukar girma da kyau da tsaruwa, kai bakace Dr Office bane in ba É—an wannan gadon da labulanshi da sauran kayan aiyukansu ka ganiba.
Duk da sai sati-sati yake zuwa nan Office ɗin tsab-tsab sai wani irin sanyi da ƙamshi yakeyi, cikin taɓe fuska tace.
"Me hakan shima DOCTOR baida lfy ne? Kodai tsabar wulaƙanci ne?".
Murmushi mai kama da dariya Haroon yayi sabida yasan babu abinda Jabeer ya tsana yake kuma tsoro kamar a tsaya a kanshi ana mgna da ƙarfi, yo shi ko a hankali kake mgna sai yace kana mishi ihu a kai bare kuma wannan da take tsaye a kusa dashi kuma tana mgna da ƙarfi cewa zaiyi haushi takeyi."
Shi kuwa Sheykh Jabeer hannunshi yasa yana dafe ƙahon zuciyarshi da yakejin yana tsalle.

Rafi'a kuwa tsaye tayi a bakin ƙofar tana kallon ikon Allah.

Sauran Nurses ɗin kuwa suma, tuni sun tafi, maraba da baƙin.

Ita ko Shatu a hankali ta ƙara motsowa gaban table ɗin hannunta tasa ta bug...

😂😂😂😂tsawon shekaru labarin littafin GARKUWA yana kimtse a kaina da zuciyata. Ni kaina in na tunoshi sai nayi murmushi nayi shauƙi sarƙaƙiyarsa kan hanani baccin dare inyi ta nazartan lmrin lbrin GARKUWA, nakanji murmushi da daɗi in na tuna lbrin nakan zubda hawaye wasu lokutan wasu lokutan nakanji jikina yayi sanyi da rayuwar duniya, labarin Garkuwa bazaka ganeshi ba, sai in ka karantashi duk iya lbrin mai labartawa bazai labarta maka yadda komai yakeba, Uhummm Allah ya nuna mana ƙarshensa, salon soyayyar Sheykh ta musamman ce..

Masoyan Parvina kuna sani dariya.

Masoyan Shatu kuna burgeni.
Ina masoyan Boleru jinjinan girma gareku.

Masoyan Sheykh ina sonku,
Sheykh yana gaidaku.

Masoyan Jalal yace ku dena kallonshi.

Masoyan Umaymah tace ku tayata da addu'a Allah ya yaye musu matsalarsu.

Wai Ya Ba'ana baida masoya ne?
Allah sarki Ba'ana ina sonshi dan al'khairin da yayiwa Aysha a baya. To wai wane al'khairi yayi mata ne?

Littafin GARKUWA na kuɗine in kina buƙatan Normal group turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276. In kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin dubu ɗaya rak ta asusun na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276. Masu turo katin mtn numbers ɗin zaki turo ba hotonba.
Chapter 62 · 0% Book details