Sashe 135
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shiga ta zauna bakin gadon Hibba tare da cewa.
"Iye ashe dai my Hibba ba dama wurin tsabta".
Murmushi Hibba tayi cike da jin daÉ—in yaba mata da Aysha tayi.
Ita ko Aysha numfashin gajiya ta sauƙe tare da cewa.
"Yanzu bari inyi wonka wlh na gaji".
Azeema da yanzu ta shigo ne riƙe da ƙaramin yaron Aunty Safiyya wacce itace ƴar farin Aunty Hafsat kuma itace matar Ibrahim.
Yaron bai wuce shekara Uku bane.
Tace.
"My Aunty kamar tafiyar mota kikayi".
Hannu tasa ta amshi yaron tare da cewa.
"Masha Allah yaron waye wannan mai kama da Jalal".
Hibba ce ta É—an shafo kansa tare da cewa.
"Aunty Aysha kice kawai mai kama da Hamma Jabeer ko".
Yi tayi kamar bataji Hibba ba.
Azeema kuwa cewa tayi.
"Yaron Aunty Safiyya ce, kin santa ko".
Kai ta jujjuya alamar a a.
Da sauri Hibba tace.
"Itace matar Ya Ibrahim ƙanin Aunty Juwairiyya".
Murmushi ta É—an yi tare da cewa.
"Ok na gane masha ALLAH".
Tace tana sumbatar goshin yaron.
juyowa suka ɗanyi jin motsin buɗe ƙofa da kukan yaro.
Safiyya ce ta shigo mai kama da Azeema sak.
murmushi Safiyya tayi tare da cewa.
"Iye Aunty Aysha kice kin gane Angon naki kenan".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Angona kuma".
Azeema ce tace.
"Eh ai mai sunan Hamma Jabeer ne."
Kai ta É—an sunkuyar ta kalli yaron tare da cewa.
"Eyeh kai mun gode kuwa".
Kallonta Safiyya tayi cikin sakin fuska.
gyara riƙon da tayiwa ƙaramin ɗanta, Salim tana bashi nono tace.
"Yanzu muka dawo kasuwa akace min kun iso ko ruwa ban shaba.
Azeema kawo min abinci tun safe muna kasuwa".
Da sauri Azeema ta miƙa taje ta kawo musu abinci.
Bayan ta zubane tace.
"Aunty Aysha sauƙa kuci kema bakici komaiba tunda kukazo".
Zatace a a .
Safiyya tace.
"A a dan Allah kada muyi haka dake sauƙo muci, Ni fa yar uwarkice kuma matar abokin wasanku kinsan ɗan kawuna aka auramin, ni matar abokin mijinki ne kuma Aminiyarki sannan ƙawar mijinki".
Dole Aysha ta sauƙo sukaci abinci tare.
Sannan ta miƙa taje tayi wonka.
Tana fitowa Hibba na shigowa da jakar data amso a wurin Ummi a can É—akin dasu Aunty Kubra suke.
Fita sukayi Safiyya kuma ta shiga Bathroom É—in.
Nan ta samu ta kimtsa.
Wani Shadda lace red color sai ratsin white blue a jiki wanda kamar zanen bakan gizo ta saka doguwar rigace
Ta zauna a jikinta ras, tayi masifar kyau, bata wani yi kolliyar azo a ganiba.
Gyalen shi farine ta yafa, bayan ta murza É—aurin É—an kwalinta.
Turarenta mai ƙamshi ta fesa.
Kana ta ninke kayan data ciren.
Da sauri Hibba da yanzu ta shigo ta amshisu tace.
"Yauwa bari in kai a wonkesu agoge kadama su tarun miki."
"To". tace, kana ta maida marfin jakarta ta rufe.
Safiyyah na fitowa ta kimtsa itama nan suka zauna suna hira har dai aka kira sallan magriba.
Bayan anyi magriba anyi ishane.
Duk suka fito babban falon.
Sai Umaymah dake can cikin ƙawayenta da matan abokan Abbansu HAROON.
ita kuwa Aunty Hafsat ta Tara zuriyarsu kab sunata hira.
Suna tsara tafiyarsu da za'ayi gobe jumma'a da hantsi, zuwa Leddi julɓe.
Da yamma ayi kamu jibi a asabar É—aura aure da hantsi sannan su dawo da amarya da daren ranar kuwa ayi walimar washe gari Lahadi kuma ranar wuni ce ayi fansan ido da yamma, da dare kuma ayi shagalin mother's day.
Duk yadda sukaso ayi bidi'a da yawa, Sheykh ya karya musu logo daya samu Ibrahim da Abbansu Haroon da kawunshi Baban Aunty Juwairiyya dasu Ibrahim da amarya Jannart É—in.
Ya dai tsara yadda yaga dama a bikin.
Haroon kamar ya rinka ihu.
In ya kufula sai Sheykh ya koma gefe yana kallonsa yana taɓe mishi baki.
Shi da Ibrahim dama su sunce sai jibi zasuje asabar zasu sammaka da tawagarsu zuwa É—aurin aure da É—aukan amarya.
Washe gari ranar Jumma'a da hantsi jirginsu Safiyya, Hibba, Aysha, Azeema, Aunty Kubra, da wasu ƙawayen Umaymah da ƙannen baban Haroon jirgisun ya isa birnin Jalaluddin.
Sheykh kuwa shi tunda sukazo idonshi ma bai sake ganin Aysha, duk da tana É—an faÉ—o mishi a rai lokaci zuwa lokaci sai dai baya bin ta kanta.
Dan hidimomin sun sha kansu.
Suna isa masarautar Jalaluddin.
Kai tsaye suka wuce Side É—in kakarsu.
Sitti kenan wacce taketa dakon zuwansu dan ganin Aysha matar jikanta mafi soyuwa a ranta.
Suna Shuga babban falonta Safiyya ta fara kiranta.
"Sitti! Sitti!! Sittin Jadda ko dai kina can wurin tsohon zumanki ne".
Dariya tayi ganin Sitti ta fito da sauri.
hannu ta buÉ—e wa Aysha irin dai al'adar su ta larabawa.
Cike daso tace.
"Iye masha ALLAH Jazlaan ya samu kekyawar mace mai nagarta".
A kunyace fuska É—auke da murmushi Aysha ta isa jikinta.
Ruggume ta tayi tare da cewa.
"Sannu da zuwa masarautar julɓe, jikata".
Cikin sakin jiki da ita Aysha tace.
"Yauwa Sitti na sameku lfy?".
Alhamdulillah tace.
Tana kallon tsohuwar da kyau tana gani wasu kamannin Ummey a fuskarta.
Jansu tayi har cikin Bedroom É—in ta.
Duk jikokinta ne.
Safiyya ce ta zaro wayarta ta kira Aunty Rahama tace mata sun isofa.
Aunty Rahma kuwa dake tsuma Jannart da kayan gyara na al'farma Juwairiyya da Jazrah da Saddiƙa na gefenta.
Da sauri tace.
"Gani nan zuwa yanzu kuwa, Safiyya".
Tana katse kiran tace.
"Muje Side É—in Sittiina.
Su Safiyyah sun iso."
A tare suka miƙa suka nufi ƙofar Sitti.
Tafiyar a kwai yar tazara tsakaninsu.
A can Side É—in Sitti kuwa, Bayan sun zauna Sitti tasa hadimanta sun kawo musu abin ci dana sha.
Sunaci suna hira.
Ita kuwa Aysha Ishma Æ´ar Aunty Rahma dake bacci kan gadon Sitti ta zubawa ido.
Duk da bata ganin fuskar yarinyar gaba É—aya amman ta hango wani irin masifeffen kama da takeyi mata da Junainah.
Shiyasa gaba É—aya hankalinta na kan yarinyar.
Hibba ce ta É—an kalleta tare da cewa.
"Aunty Aysha kici mana, kin tsaya kallon Ishma".
da sauri ta É—an rusuna ta fara cin Couscous da miyar hanta da Sitti tayi musu da kanta.
Suna shigowa Aunty Rahma ta tsaya tana kallonsu cikin sakin fuska tace.
"To yau duk kamar takuma ta zama É—aya ina surkar tawa".
Sitti ce ta kalleta cikin son yar autar tata tace.
"Gata nan a gabanki".
Ta ƙarashe mgnar tana nuna mata Aysha dake zaune tana fuskantar gado.
ÆŠan juyowa Aysha tayi da murmushi a fuskarta.
Da sauri ta juyo gaba É—ayanta tana kallon Aunty Rahma cike da mamakin tsananin kamarta da Ummeynta, hatta muryarsu iri É—aya.
Da sauri tayi ƙasa da kanta, jin ta zauna kusa da ita.
Cike da Muryar mamaki tace.
"Aunty Rahama ina kwana".
"Lfy lau Alhamdulillah my surka ya É—ana, Jazlaan".
"Alhamdulillah yana lfy". tace fuska a sake tare da alamun kunya da kuma al'hinin abin da take gani da ji na kamanceceniyar fuska da murya.
Sitti ce tayi dariya tare da cewa.
"Tab lallai kuwa da yana kusa da kinsha tsuka, kin san baya son kina ce masa É—anki dan yace ya fiki".
Safiyya ce tace.
"Tab ai Hamma Jabeer baya son ace ta fishi, sai yace.
"Dan wata biyun ne wani abun".
Dariya dai sukayi ita kam Aysha.
Ta shiga ruÉ—ani kamannin.
Ƴarinyar da aka kira da Ishma da Junainah sun bata mamaki, sai kuma ga kamannin da yafi bata tsoro ma yanzu kam ko murya da dariyar Ummey nata irin na Aunty Rahma ne.
Ya ilahi ya mujibadda'awati".
Ta faÉ—a cikin ranta.
Lokacin da Ishma ta taso zaune daga baccin da takeyi, har kamar zata faÉ—i.
Da sauri tasa hannu ta tare yar yarinyar da bazata gaza shekara biyar ba.
Da sauri Æ´arinyar ta manna kanta a jikinta tare da cewa.
"Mommy zansha ruwa".
Da sauri ta sunkuyo kan yarinyar hannunta tasa ta dafa goshinta, cikin sanyi tace.
"To ga ruwan buɗe baki". Ta ƙareshe mgnar tare da ɗaukan bottle water mai ɗan sanyi dai-dai misali, tana buɗe marfinshi.
Juyowa Ishma tayi jin baƙuwar murya.
Cikin sauri ta kalli Azeema tare da cewa.
"Laa Aunty Azeema kalli Aunty Ayshan Hamma Jabeer tazo".
Tayi mgnar da alamun tasan Aysha a hoto.
Murmushi tayi tare da sa mata bakin gorar ruwan a baki.
Cikin mussuke ido ta buÉ—e baki ta fara shan ruwan.
Aunty Rahma kuwa, kallon Aysha take cike da ƙauna.
Aunty Juwairiyya ce ta É—an kalli Aysha cikin yanayin da bazaka gane manufarshi ba tace.
"Sannuku da zuwa yau kam gaki a masarautarmu tushenmu, gaki ga Sitti kakarmu data haifi babana ta kuma haifi Mamansu Sheykh da Ya Jafar dasu Jamil jininmu É—aya".
Ta ƙareshe mgnar cikin nuna kusanci da dangatakar dasu Sheykh na jinine.
Kai Aysha ta É—an juyo ta kalleta,
murmushin gefen baki tayi,
dan ta gane manufar Aunty Juwairiyya tana nuna mata cewa su jini É—aya ne, itace bare a tsakaninsu.
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh yau kam gani ga Sitti ga Aunty Rahma".
Ta ƙareshe mgnar tana wata mgnar a zuciyarta.
"Uhumm Aunty Juwairiyya kenan, ai dama saida ɗan gari akanci gari da yaƙi, kina matsayin yar uwarsu kuma kike cutar dasu, in da zasu sani da bazasu aminta da keba".
Muryar Ishma ce ta katse mata mgnar zuci da takeyi.
"Aunty Aysha ina Hamma Jabeer".
Kanta ta É—an shafa tare da cewa.
"Yana Tsinako".
Da sauri tace.
"To shi bazai zo bane?".
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
"Zai zo".
"Yaushe?". Ta kuma tambayarta a gajarce.
murmushi ta É—an yi tare da cewa.
"In Sha Allah gobe zasu zo".
Allah ya kaimu ta tafaÉ—a tana wasa da jelan gashin Aysha dake bisa kafaÉ—arta.