← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 183

Sashe 92

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai bayan sallan isha'i sun gama aikin sahur É—in ne.
Suka dawo falo, nan Ummi ta nuna mata É—inkunanta da aka bada tun Umaymah bata tafiba.
Sosai taji daÉ—in kayan da É—inkunan, lallai tana son dogayen riguna Amman tana son surkawa da Shadda, atampa, leshi, musamman WaÉ—an nan É—inkunan sunyi masifar kyau. Ko wanne dai-dai jikinta kamar an gwada ta.
Daga nan kuma suka nuna mata gellulluka da hibai da takalma da saraƙunan da suka zaɓo mata bayan sun zaɓawa kansu.
Sun nuna mata nasun ma.
Ummi ta ƙara da cewa.
"Duk zannuwan da abun É—inkawan kuma an bawa Kabir telen suma duk cikin KMC suke.
Nanda salla dai komai zaizo dai-dai.
Cikin jin daÉ—i tace.
"Ngd matuƙa Ummi Allah ya saka da al'khairi".
Amin Amin tace. Kana tace.
"Sheykh zakiyiwa godiya".
Shiru tayi kamar bataji ba.
Hibba kuwa cikin jin daÉ—i tace.
Aunty Shatu na zaɓa mana wani Shadda lace mai masifar kyau iri ɗaya na ɗauka mana Royal blue and white Golding color. Nace a tsantsara mana dogayen riguna".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kai kinko kyauta mana".
Daga nan suka tattara tarkacen suka nufi makoncin baccin su.

Zaune take gefen Ummi tana riƙe da waya cikin murmushi tace.
"Allah ko Umaymah munyi kewarki".
Cikin jin daÉ—i Umaymah tace.
"To ko zaku zomin Barka da sallane".
Da sauri tace.
"Eh Umaymah Allah in ya yarda zamuzo ki tambayan mana shi".
Cikin dariya Umaymah tace.
"Yoh mace da mijinta sai wani ne zai tambayar miki".
Cikin sanyi tace.
"Uhummm".
Ita kuwa Umaymah cewa tayi.
"Ina Umminku?".
Da sauri tace.
"Gata ta ƙarishe mgnar da miƙawa Ummi wayar.
Cikin fara'a suka gaisa kana Umaymah ta tambayeta ya yaran nata, tace duk suna lfy.
Nan take ce musu ta cewa Shatu ai a saudia zasuyi salla.
Sosai Shatu ta tayasu Murna.

Suna cikin hirar Hadimai guda uku suka shigo da jakukkunan guda uku.
Rusunawa sukayi bayan sun gaidasu ne,
suka ajiye jakukkunan tare da cewa.
"Gashi biyun inji LamiÉ—o É—aya kuma Gimbiya Aminatu ce tace mu kawo miki".
Sukarishe mgnar suna kallon Shatu.
Godiya tayi musu kana ta kalli Hibba data miƙo mata kuɗi sun kai dubu biyar.
Ta gane manufar Hibba shiyasa ta amsa ta basu.
Godiya sukayi kana suka tafi.

Jim kaɗan Hadiman Hajia Mama sukazo da saƙon Hajia Maman.
Sosai Shatu tayi godiya ta mashi kuÉ—i a hannun Hibba ta basu.

Nan Hibba ta tattara kayan ta shigar dasu, zata shigar dana HAJIA MAMA tace
"A Hibba barsu zan shiga dasu."
Gefe ta nuna mata tace ajiyesu anan.

Bayan sunyi sallan azahar sun fito zasu Fara aiki ne ta kalli Ummi tace.
"Ummi bari inje inyi godiya wurin Hajia Mama".
Cikin tsareta da ido tace.
"Ki bari mana sai ansha ruwa sai in rakaki daga nan kiyiwa LamiÉ—o ma godiya.
Duk dai wannan kyauta da yakeyiwa duk ahlin masarautar JoÉ—a in lokacin salla ya gabato amman muje kiyi godiyar."
Da sauri tace.
"No Ummi ba sai an rakani ba, zanje ni É—aya ma, kinga nasa al'kyabba".
Daga nan ta fice, cike da mamaki suka bita da ido.

Bayan kamar 37 minute ta dawo cike da fara'a sukaci gaba da aikinsu.

Can da suka fito dan yin sallan la'asar,
Ba kayan ba dalilinshi. Da sauri Hibba tace.
"Aunty Shatu kin shigar da kayan ne?".
Ci gaba da tafiya tayi tare da cewa.
"Maisu ta aiko an kwashe mata abunta dai".
cikin mamaki sukabi bayanta.

Yau azumi goma sha huÉ—u gobe 15 in Allah ya kaimu.

Bayan yaci abinci ne ya kira Umaymah nan yake ce mata.
"In Allah ya kaimu gobe iwar haka ƙarfe goma na dare zuwa sha ɗaya jirginmu zai tashi Umaymah".

"Kai da waye zaku tafi ne?".

"Nida Dr Aliyu, da Barrister Kamal, sai kuma Ya Hashim da Galadima, da Wambai da Abba na da cimgan É—in shi".

Da sauri tace.
"To wai kana nufin kai bazaka je da taka cingam É—in bane?".

Cikin sanyi yace.
"Kiyi haƙuri Umaymah dan Allah na roƙeki kada kice inje da kowa, dan Allah a barni mana in huta in na bar ƙasar kam".

Shiru Umaymah tayi saida taji ya kai ayane tace.
"Shi kenan Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, kuma muna nan tafe".

Amin Amin yace kana sukayi sallama.

Washe gari kab mutanen masarautar JoÉ—a masu zuwa Umrah sun gama shirin su.

Bayan ansha ruwa anyi sallan isha'i ne suka shiga kitchen dan aikin sahur, koda ta É—auko Foodflaks É—in da akasa mishi abin buÉ—a baki ko buÉ—e su baiba.
Hakane yasa Ummi tace to maza ta dafa mishi wani abun.

To tace kana ta juya ta É—auko, kaza, kwai, dankalin turawa kaÉ—an, maggi, gishiri, tattasai, attaruhu al'basa mai Curry,
Duk ta matso dasu kusa.
Sai kuma ta É—ebo Kabeji karas.
Ta miƙawa Saratu tace.
"Yauwa Sara goga min su ƙananan, kada ki haɗasu wuri ɗaya, kana ki yayyaka min al'basa sannan ki jajjaga min wata."
Ta faÉ—in tana tura mata Attaruhu da al'basan.
Cikin nitsuwa Saratu tace.
"To Aunty ba matsala".
Ita kuwa Ummi meda hankali tayi kan girkin sahur É—in.

Wanke rabin kazar tayi, tare da sata a tukunya ta watsa al'basa da maggi da tafarnuwa da citta da kanamfari kaÉ—an.
Sannan ta rufeshi. Tasa wuta yadda ya kamata.
Kana ta jawo robar dankalin ta fara ferewa tare da cewa.
"Allah aikin nan yana yawa Ummi, kusan wuni muke a kitchen mu kuma kusan kwana shima wai bazaici abuba sai sa mutane aiki".
Tayi mgnar cikin gajiya da kuma iya gskyar ta, dan muddin kasha ruwa tafa burinka ka samu ka huta.
Juyowa Ummi tayi ta É—an kalleta tare da cewa.
"A'a ai bakya son hutun tunda kikaje kika samu Juwairiyya kikace ta huta taji da aikin gidanta, nan zaki rinƙa yi, sannan in Hajia Maman ta aiko ki kora Hadiman dashi, ko kisa Hibba ta kaiwa bayi shi.
Kinga duk sun gaji sun daina kawowa, sai Na Gimbiya Aminatu, shi kuma Sheykh yace a dena kawowa tunda kice zaki iya da aikin.
Yanzu da kin bari suna kawowa dai da wata ranama sai munga dama mushiga madafa".
Sunkuyar da kanta tayi tare da yin shiru kamar bata nan.
Yes ta san duk abinda Ummi ta faÉ—a hakane.
Ƙarisa feree dankalin tayi kana ta wonƙeshi fes ta ɗaurashi a wuta, ya dafu sosai kana ta sauƙeshi a gefe.
Zuwa lokacin kazar ma tayi lugub, haka yasa ta sauƙeshi ta juyeshi a plate, zare ƙasusuwan tayi duka, sannan ta ajiyeta gefe kusa da dankalin.
Jajjageggen Attaruhu da al'basan da Saratu ke miƙa mata ta amsa.
Cikin plate É—in dafeffen dankalin ta juyeshi kana tasa kazarma a ciki.
Sannan ta jujjuyasu ta caƙuɗasu da kyau, kana tasa Maggi gishiri ɗan ƙanƙani, sai kuma Curry.
Kwan dake gefe cikin É—an wani kwanon tangaran ta jawo, ta fasa kwan ta juye cikin haÉ—in kaza da dankali da jajjagen ta É—an gwarayasu.
Hibba data shigo yanzu ne tace.
"Yauwa My Aunty dama kwaÉ—ayi ne ya koroni nazo in shiga kitchen."
Murmushi tayi tare da cewa.
"To matso ki tayani aikin É—an zuba min ruwan zafi kan Karas É—incan.
In yayi ɗumi ki juye ruwan cikin kwandon kabejin nan ruwan zafin ya ɗan razana ganyen, sai ki miƙo min shi nan".
To tace tare da fara aikin.
Ita kuwa Shatu ɗiban haɗin ta rinƙayi tana mul-mulawa kamar Yan boll,
saida ta gama sannan, ta É—aura man gyaÉ—a.
yayi zafi ta fara suyasu,
saida ta soyasu duka tasa a Foodflaks kudun kada yayi sanyi ta matsar dashi gefe.

Kana ta matso ta ta amshi Kabeji da Karas É—in.
Mai tasa kaɗan a tare da al'basa, kana tasa jajjagen kaɗan, ta soyasu, sannan ta ɗauki sauran murmusheshen kazar tasa a ciki kana ta juye Kabeji ta Karas ɗin, sanna tasa Maggi, mintuna biyu zuwa uku ta sauƙesu.
Ta zubawa Hibba da Ummi kana tasawa Sara.
Sanin ya dawone yasa ta shirya mishi komai a tray'n.
Kana ta nufi Side É—inshi.

Ummi kuwa da Hibba a falon suka zauna suka fara ci suna santi.
Ita kuwa Saratu tattare wurin tayi ta kimtsa komai ta goge sauran kwanuka kana ta tafi.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, tuni ya gama kimtsa komai da zai buƙata in yayi tafiyar.
Bai wani É—auki abu da yawa ba.
Komai na É—auki shi ya kimtsashi bisa tsari.
A hankali ya taso daga bakin gadon hannu yasa ya shafa cikinsa,
Yunwa yakeji kuma ya gaji da masan shiyasa yau bai kulaba.
Folon ya nufo tare dasa kuÉ—in dake hannunshi a al'jihun jallabiyarsa.
A hankali ya tura ƙofar ya fito.
A dai-dai lokacin itama ta turo ƙofar shigowa falon .
A hankali ta shiga

Tsakiyar falon ya nufa,
bisa kujera ya zauna, ita kuma kanta a sunkuye ta iso inda yaken.
ÆŠan sunkuyowa tayi ta ajiye tray'n kan santa table É—in, gabanshi.
Kana a hankali ta fara miƙewa zata tashi.
Kanshi ya É—an juyo ya kalleta, da yatsarshi ya nuna mata ta zauna.
Cikin kwaɓe fuska tace.
"In zauna?". Kanshi ya gyaÉ—a mata alamar eh.
Chapter 92 · 0% Book details