← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 183

Sashe 24

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kallon sukeyiwa juna shida Ya Salmanu, cikin wani irin mugun kallo mai cike da mugunta yayi kwaffa tare da cewa.
"Uhummm Salmanu manyan gari, wato har an samu wani mai yar guntuwar jarumtar da zai iya haɗa so dani a kan Shatu, to bazan ce maka komaiba, amman ka shirya ranar litinin zamuyi shaɗi muddin ka cini na bar maka ita duniya da lahira, zan kuma bar garin Bani, da ƙasar nan gaba ɗaya zan koma ƙasar Cameroon, in kuwa na cika zaka bar duniya baki ɗayanta!".
Cikin tsananin tsoro da kaÉ—uwa Shatu tace.
"A a fa Ya Ba'ana wlh ba sona yakeyiba, karatu yake koya min".
Da sauri Salmanu ya katseta da cewa.
"Sonta nakeyi Ba'ana so kuma na aure, na kuma yarda zan shiga gasar ShaÉ—i da kai a ranar Litinin na amince".
Wata irin muguwar dariya yayi wacce har tasa Aysha kowa cikin gida da gudu, shi kuwa saida yayi dariyar mai isarshi kana yace.
"Lallai gidan ArÉ—o Yabani na gab da rasa motsin É—ana miji".
Yana faɗin haka ya murza layar zananshi, sai gashi ya ɓaci.

Cikin ƙarfin hali Salmanu ya nufi gida.

Shi kuwa Ba'ana yana ɓacewa a tsakiyar dottawan Fadan Arɗo Yabani ya baiyana,.
Wanda badon tsoffin makiyayene sun saba ganin abinda yafi haka ba tabbas watsawa zasuyi.

So amman suka dake, cikin kamala Bappa ya kalleshi tare da cewa.
"A a Ba'ana lfy kuwa?".
Sunkuyar da kanshi yayi kamar mutumin kirki, cikin danne fushinsa yace.
"Ku gafarceni Bappa nazone da batun neman al'farma fagen shaÉ—i, nida Salmanu É—an ArÉ—o zamuyi gasa kan Shatu, na kuma yarda, muddin yayi nasara akaina na bar mishi Shatu zan kuma bar Rugar Bani baki É—aya".
Da sauri Bappa yace.
"A a".
Da sauri ArÉ—o Yabani yace.
"A a Malam Liman ba komai, na amince na basu damar yin gasar ShaÉ—i mai nasara yaci gasar".
Jin haka yasa dattawan nan duk sukayi shiru.

Shi kuwa Ba'ana cikin tarin ƙeta jikinshi har tsuma yakeyi yana maganar zuci.
"Uhumm zan kashe Salmanu kuwa kisa mafi muni zaku gane kurenku hegun fulani kunzo garin daba nakuba kun fisu dukiya zan kashe Salmanu irin kisar da ban taɓa yiwa waniba kisan da zaisa har abadan babu wanda zai sake cewa yana son Shatu".
A zahiri kuwa, godiya yayi musu kana ya juya ya tafi.
Nan dattawan kuma sukaci gaba da tattaunawa yadda ShaÉ—in zai kasance.

Washe gari ranar asabar da sanyin safiya akayi shelar sanar da gasar ShaÉ—i da za'ayi jibi litinin, da kuma, waÉ—anda zasuyi gasar da sunan wacce za'ayi dan ita.

Gaba É—aya magarna ta cika Rugar Banin da kewayenta, duk wanda yaji yana firgici,
Maman Salmanu kuwa tuni taketa kuka tana cewa ita kam so ake a ƙarar mata da yaranta an kashe mata Hashimu yanzu kuma ace da Salmanu za'ayi gasar Shaɗi da mutun da sun san ba'a taɓa nasara a kansa a.,
Mutanen sauran rugogin Fulani dake mutunci da ArÉ—o Yabani kab sai gudumowar magunguna suke kawo na dauri dan a tsuma jikin Salmanu.

Sosai kuwa babanshi da yayunshi mata da maza da abokanshi keta tsumashi.

Shi kuwa Ba'ana tun ranar ya ɗauki tunƙur ƙasar da yake tsuma bulalinshi, ya kaishi Ƙauyen Bonon, gaban dodon tsafinsu,
Anan tukunyar ta kwana bulali tamanin dake cikin tunkuyar nan aketa tsumawa da tsafi.
Kana an jikasu da ruwan gishiri sannan an juye kunamai sama da ɗari a ciki, irin baƙaƙen kunamun nanne masu mugun dafi, an sasu ciki sunata harbin bulalin nan suna sa dafinsu a jiki. ranar lahadi da yamma ya amso tukunyar,
Har zauren gidansu Shatu yaje yasa aka kira mishi ita bayan ta fitone yace ta leƙa cikin tukunyar, a hankali tace.
"Me zan gani a ciki?".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Nazo in nuna miki bulalin shaÉ—i nane, ki gansu da kyau, dan ki cewa wancan koÉ—eÉ—den ya shirya shan zabga".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni ba sai na ganiba".
Murmushi yayi tare da buÉ—e tukunyar kana ya karkatar mata shi gabanta.
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"In......

Littafina na kuÉ—ine turo katin mtn na É—ari uku kacal ko karanta a nitse.

By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 10

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

LITTAFIN GARKUWA NA KUÆŠINE, TURO KATIN MTN NA ÆŠARI UKU KACAL ta number 09097853276 domin samun cikekken labarin, ko kiyi min transfer É—in 1k É—an samun SP GROUP ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276

FREE PAGE

Cikin tashin hankali tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ya Ba'ana me wannan, abu kamar macizai". Da sauri ya meda ya rufe kana ya miƙe cikin yin ƙasa da murya yace.
"Kinga ni kada ki tayarmin da hankali kinsan bana son ganinki cikin tashin hankali, in sha Allah nine da nasara ko dai bakya so nane".
Da sauri ta girgiza kanta tare dasa tafin hannunta ta rufe bakinta.
Ganin haka ya kwashi abinshi ya tafi.

Ita kuwa koda ta shiga gida, gefen Inna ta zauna tare da cewa.
"Inna ku cewa Bappa ya cewa ArÉ—o ya hana gasar nan, kada a cutar da Ya Salmanu".
Cikin sanyin jikin da duk kwanan haka inna ta zama, a hankali tace.
"Uhumm ba komai Shatu in sha Allah duk abinda zai faru da sanin Allah.
Yanzu ke yaushe nema zaki koma hutunmu?".
Kanta ta gyaÉ—a a hankali tace.
"Rana ita yau zan koma kimga saura mako É—aya kenan".
Ummey ce dake gefe ta É—anyi ajiyan zuciya gami da cewa.
"Alhamdulillah ni in kin komama hankalinmu zaifi konci, domin muddin kinanen sai Ba'ana yayi ta kalato fitina".

Shiru sukayi baki É—ayansu, jin an fara kiran sallane tasa, duk kowa yayi al'wala haraman salla.

A daren ranar kuwa Ya Salmanu da abokinshi Sale suka zo, wurinta, nan take ce musu ita kam bata son wannan gasar da za'ayi kuma tunda an kafe sai anyi sam ita bazata jeba.
Haka dai sukayi ta hira daga bisani suka tafi.

Washe gari ranar Monday kuwa, tun da sanyin asuba aketa gangamin.
HaÉ—uwa a filin da za'ayi shaÉ—i.
Mutanen sun cika maƙil dan anfi yawan yin gasar da safe, sabida da rana duk makiyaya sun tafi kiwo manoma sun tafi daji.
Tuni matasan Fulani na rugogin nesa da Bani ma sun zo.

Bukar kuwa tunda aka fito sallan asuba yaje. Gidan ArÉ—o Yabani, yaso ace an janye gasar tun randa aka shelanta amman ArÉ—o yaki,
still yanzuma da yazo, bayan sun gaisane ya É—anyi gyaran murya tare da cewa.
"Haƙiƙa naso a janye wannan shaɗi, domin nasan abun bazaiyi daɗin ganiba ace Ba'ana na zane Salmanu ɗan Arɗo ga wannan rugar, amman kaƙi ka saurari zancena,
Dan haka ni ba kada wani abu ya faru ku kuskura kuyi kuka dani, duk abinda ɗana yayiwa ɗanku kune kuka saya mishi da yawun bakinku kun rigada kun san bazaku taɓa samun wanda zaifi ƙarfin ɗanaba".
Shiru ArÉ—o Yabani yayi yana nazartan kalaman Bukar,
ganin yayi shirune alamun ya gama magarsa cikin sanyi ArÉ—o Yabani yace.
"Duniya da faɗi take, Bukar Mai kanwa a kwana a tashi watan-wata-rana zakaji zaka gani da idanunka za'a samu wanda zaifi ƙarfin ɗan ka, Allah zai bijiro da wanda zai iya jure bulalin ɗan ka".
Cikin wani irin yanayi Bukar yace.
"Babu mamakin a samu mai iya, jure bulalin, tabbas babu mamaki. Sai daifa abun da bazai taɓa yiwuwa bane har illa masha ALLAH ace an samu wanda zai iya nasara a kanshi babushi babu namijin da zai iya sashi jin zafin bulala bare ya zubda hawayen da zaisa ya rasa Shatu".
Wani dogon numfashi ArÉ—o Yabani yaja tare da cewa.
"Uhummmmmm". Daga nan bai kuma cewa komaiba,
Shi kuwa Bukar tashi yayi ya kakkaɓe rigarsa ya juya ya tafi yana faɗin.
"In dai kunne yaji gangan jiki ya tsira".
Da ido Arɗo Yabani ya rakashi, yana maiji a cikin ransa inma ace yanada dama, inama ace zai samo wannan bulalin da Malam Chuɓaɗo ya gaya musu, da tabbas ya samu hanyar da zai cire mugun iri a garinshi.

A haka Salmanu da abokinshi, sukazo suka sameshi zaune. Bayan sun gaisane Sule ya É—an matso kusa da ArÉ—o a hankali yace.
"Allah rene, duk wuri an taru mu ake jira, shi Ba'ana tun da asuba yana can, yanzu Iro yazo yake ce mana gacan fili ya cika, mu kaÉ—ai ake jira, har wasu nata maganganun wai Salmanu ya ji tsoron Ba'ana ya gudu".
Murmushin da yafi kuka ciwo ArÉ—o Bani yayi dafa tsakiyar kan Salmanun yayi kana yace.
"Kuje Salmanu, Allah ya bada sa'a Ubangiji yaga niyarmu na son tseretar da wannan yarinyar daga fadawa auren wannan mushurkin, taƙadiri in Shatu matarkace Allah ya baka sa'a in kuwa ba matarka bace, Allah ya baiyono mata wanda zai zame mata GARKUWA daga faɗawa auren wannan azzalumin".
Amin Amin sukace baki É—ayansu kana su sukayi gaba.
Shi kuwa ArÉ—o, saida ya jira su Malam Liman Bappa kenan dasu Ahaji Horu, da Ahaji Umaru da Garbati.
Koda sukazo ba ɓata lokaci suka nufi, farfajiyar wurin da aka tanada dan shaɗi.

Filin ya cika ya batse tako ina mutane zuwa sukeyi arna da musulmai fulani da hausawa da ƙabulun, Ɓachamawa, domin duk yankin nahiyarsu an san babu taƙadiri sama da Ba'ana sabida tunda ake gasar Shaɗi da kuma gasar kokuwa yayin nunan sabon gero ba'a taɓa cin nasara kanshiba, muddin ya shiga gasa tofa shine da nasara.
Har ta kai da in dai ya É—aga hannun to babu mai É—agawa.
To sanadinshi aka hana ShaÉ—i a Rugar Bani, tsawon shekaru biyu sai gashi yau an dawo dashi.

Wannan dalilin ne yasa gaba ɗaya Rugar Bani ta cika maƙil da mutane maza da mata manya da yara,
Ga mai busar sarewa kuma yana tsakiyar taro inda akabar filin da za'a gobza yanata rere kirari wa Ba'ana.
Chapter 24 · 0% Book details