← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 183

Sashe 124

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zamanshi yayi ya fuskanci ArÉ—on araÉ—abe cikin tattausan lafazi yayi É—an murmushi tare da cewa.
"Kuna lfy ko? ba wata matsalar ko?".
Murmushi ArÉ—on araÉ—abe yayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah".
Kanshi ya É—an É—ago ya kallesu baki É—ayansu kana yace.
"Masha Allah. To Allah ya taimaka".

Amin Amin sukace cike da jin daÉ—i, shi kuwa fuskantarsu yayi dukansu tare da cewa.
"Na kawo wannan ziyarar ne dan samar da Kekkyawar alaƙa da kauda fitina tsakanin makiyaya da manoma da sauran al',lummar gari.
Ina al'fahari da dukanku biyu uku makiyaya manoma jama'ar gari.
Bana son wani sashin ya cutar da wani sashin.
Ina neman al'farma daku zauna lfy da manoma banda yi musu ɓarna akan haƙinsu.
su wahala su noma kusa dabobbin ku suci su taka kunsa ya tabbata baku da gskya duniya zata É—aukemu masu tada zaune tsaye.
Amman ina kuka bari manoma suka tattara kayan amfaninsu sai ku nemi izinisu ku shiga kuyi kiwo a gona kinsu".

Cikin gamsuwa da bayaninshi suka haÉ—a baki wurin cewa.
"In Sha Allahu zamu kiyaye,
bazaka samemu a layin masu tsokana ba mu nan Jafuna".
Kanshi ya gyaÉ—a cikin gamsuwa kana yace.
"Muddin manomi ya neme ku da fitina ko wasu sauran gama gari kada ku tanka musu.
Ga number wayata zan baku koda yaushe kuka kira zata shiga.
Zan sanar da ƙungiyar *MI YETTI ALLAH* itace ƙungiyar dake kula da matsalolin makiyaya da manoma.
Sannan duk inda kuke akwai mambobinmu a garuruwan dake kusa daku zasu shiga lamarin.
Duk wanda aka samu da rashin gsky zai fuskaci Hukunci.
Kana Ƙungiyar *TABITAL POOLAKU* tana tare daku a cikin dukkan al'amuran ku.
Kiyaye shigar banza kamar dai yadda na ganku yanzu cikin manyan suturu shine abinda yafi dacewa damu a matsayinmu na musulmai".

Cikin murmushin ArÉ—on araÉ—abe yace.
"Zamu kiyaye, kuma dama mu Jafunawa bamu ɗaya daga cikin ƙabilun dake yawo a daji da kiwo masu yaɗa barna.
Mu Jafunawa ko suturarmu ta banbanta data sauran makiyaya".

Hannu ya bashi bayan ya basu number miƙewa sukayi tare.
Da musu godiya
Kana suka rakasu har wurin motocinsu, nan Galadima ya miƙa musu kyautan kuɗin taimakon da Sheykh ya ware musu.
Nan suka shiga suka tafi a jere kamar dai yadda sukazo.

Tafiya mai É—an nisa sukayi kana suka dawo kan hanya.

Jihar Jigawa suka nufa,

Dan yana so a ƙalla dai a yau ya zauna da Arɗaɓen jihohi uku

Kamar yadda ya tattauna da Rugar forko hakama ta biyu.
Sun amshesu a mutunce.
Daga nan suka nufi jihar (Tsinako) Katsina.

Daji suka nausa karfe biyar dai-dai suka isa Rugar da ArÉ—on araÉ—abe nasu yake.

Dai-dai lokacin kuma gaba É—aya makiyayan sunata dawowa kiwo.
Bayan sun fitone, suka nufi inda suke.

Cike da mamaki Sheykh da tawagarsa duk ke kallon mutanen wannan Rugar.
Gaba É—ayansu maza garin kitsone a kawunansu reras har kafaÉ—unsu.
Ga wasu irin guntayen wondunan yadin atampa na mata,
kana rigunan tashi kabi shanu a jikinsu.
Kowa ka gani da sanda a wuyanshi.

Ba yabo ba Fallasa suka marab cesu.
Bayan sun gaisa ne yayi musu jawabin abinda ya kawosu.
ÆŠaya daga cikin ArÉ—o's É—in ne yace.
"To wannan shiga dai itace muka samu wurin iyaye da kakanni babu kuma abinda take mana mu ba a takure mikeba kamar yadda kace.
Sannan batun manoma kuma infa suka tsokanemu mu bazamu jira wata hukumar.
MI YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU ba.
Zamu rama".
Murmushi Jalal yayi tare da cewa.
"In kunfi ƙarfin kungiyar ku ta mi YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU.
Tabbas bazakufi ƙarfi mu mu rundunar tawagar sojojin ƙasar ba.
Ku iye harshenku tabbatar da zaman lfy ne ya kawomu nan ba musuba kuma umarnine."
Cike da mamaki Ya Hashim da Laminu da Sulaiman harma da Jamil suka zubawa Jalal ido.
Mgnarshi ta nuna cewa, shi sojane mai ƙarfin iko kenan.
Rigar dake jikinshi ta sama ya cire.
Sai ga rigar sojojin ƙasar Nigeria ta baiyana a jikinshi a saman kafaɗunshi.
Taurari biyu da kuma alamar Shaho colonel ne kenan.

Suma sauran abokanshi biyu rigunansu na sama suka cire.
Ganin hakane yasa waɗannan makiyayan sukayi ƙasa da kawunansu.

Shi kuwa Sheykh.
Gyara zamanshi tare da cewa.
"Zama lfy yafi zama É—an sarki, inji bahaushe to, tabbas mu zauna lfy shine ci gabanmu."
Sai kuma ya kalli Galadima dake gefenshi yace.
"WaÉ—annan mutanen a dasawa Rugarsu ayar tambaya.
Ku tashi mu tafi, in naji wani kuskure ko tsokana daga gareku tabbas zaku fuskanci fushin ƙungiyar mu, zamu kuma miƙaku hannun hukumar ƙasa.
In kuwa wasune suka tsokaneku ga number ta ku gaya min haƙiƙa zamubi kadunku bazan lamunci a cutar daku ba."

Da sauri Arɗon Arɗaɓen ya biyo bayansu da sauran wasu dattawansu.
Haƙuri suka bashi tare da al'warin zaman lfy.
Kana bazasu bari ayi husumaba.

Da haka dai sukayi sallama suka tafi.
Madadin su kwana cikin jihar Tsinako indama sukeda cikekken ikon a masarautarsu Haroon ga uwa mai daraja Umaymah sai suka wuce jihar Noka bayan sunyi sallan mangriba da isha'i.

Suka É—au Hanya.
Gajiya iya gajiya sunyishi.
Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi nuƙui sabida ba ƙaramar tafiya sukayi ba.
Wuni a zaune tun karfe bakwai na safe har yanzu takwas na dare kan tafiya suke kuma babu alamun sun kusa jihar Nokan.

A cikin motarsu Jalal da abokanshi sunata hirarsu.

Laminu kuwa tuni ya sanarwa Gimbiya Saudatu ashe Jalal sojane.

Ta girgiza da jin lbrin sosai.

A motarsu Galadima kuwa shiru duk sukayi dan gajiya ga jikin tsufa.

Ita kuwa Aysha dama tunda aka hanata fita, ta kumbura ta cika tayi tib bata sake kulashiba, shima ko inda take bai kuma kallonba.

Bare yanzu aikin tura rahoton tsarin Rugar da suka fito yake turawa Haroon.
Ta E-mail address É—in shi sabida shi baya whatsapp.
Bayani yake mishi ya isar da saƙon ga masarautarsu dan a sawa mutanen wannan yankin ido sosai, ya lura basu da nitsuwa.

Haroon kuwa Umaymah ya kalla cike da mamaki yace.
"Kinaji Umaymah Sheykh fa yau jihar nan ya wuni.
Wai yanzu madadin ya kwana a nan shine ya wuce Nokan a daren nan".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na sani ai munyi mgna da Aysha.
Tare da ita suke shiyasa bazai iso nanba".
Murmushi Haroon yayi kana sukaci gaba da hirarsu.

Sai ƙarfe Goma da rabi suka isa Nokan state.

Wani tamfatsetsen hotel mai zaman kanshi suka nufa.
A cikin motar ya rufeta.

Kana ya fita.
Su Jamil duk na biye dasu a baya.

ÆŠakuna ya kama musu gaba É—ayansu sannan ya juyo ya dawo shi É—aya.

Motar yazo ya buÉ—e tare da cewa.
"Bismillah".
Tura baki tayi tare da cewa.
"A barni zan kwana cikin motar".
Kanshi ya sunkuyar tare da kaurara muryarshi yace.
"Ki fito".
A hankali ta zuro ƙafafuwan ta woje,
sun É—an kumbura alamun dadewa a zaune.

Sabida ko abinci saya sukeyi a cikin mota sukeci.

Sai dai shi wunin duka dabino yakeci.

Miƙewa tayi ta fito.
Hannunshi yasa ya É—auki jakar kayanshi.

A hankali yayi gaba tana biye dashi a baya.

Hotel ɗin babbane mai matuƙar kyau.

Wani Side shi wai VIP can suka nufa.

Suna shiga cikin falon, ta zauna bisa kujera.

Shi kuwa ajiye jakar yayi kana, ya miƙe tsaye,
Jikin ƙofar ɗakin ya koma ya rufe kana ya zubawa ƙofor ido.
Tsawon mituna biyar, kana ya dawo wurin abun kunna fankan
daga nan kuma ya dawo tsakiyar falon saman jikin fanka ya tsurawa ido.
Ita kuma tana binshi da ido, ne ganin kamar wani abu yake nema.

Bedroom ya wuce.
Ya fara bincikar É—akin.
A jikin masaƙalin Rimot ɗin AC yaga wani ɗan ƙaramin abu.
Hannunshi yasa ya cire abun.
Kana ya fito jakar ya É—auka tare da cewa.
"Mu tafi".
Cikin gajiya da wani irin nannauyan masifeffen baccin daya cika mata ido ya kashe mata jiki da gajiya tace.
"Ina kuma zamu je? ni bacci nakeji! Ni na gaji".
Hannunshi yasa ya kamo nata hannun.
Wani ɗakin suka kuma komawa aka basu key tare da bashi haƙurin da ita dai bata san kanme suketa bashi haƙurinba sunata rantsawar basu sani bane.
Ma'aikatan hotel É—in da kansune suka bi bincika É—akin kana suka fita,
suna cewa.
"In sha Allah zamu kula zamu kuma kiyaye gaba".

Rufe ƙofar yayi kana ya wuce bedroom.
Ita kuwa bisa kujerar ta kwanta tana sauƙe numfashin gajiya da bacci a take bacci ya saceta.
Shi kuwa Sheykh wonka yayi kana ya fito yayi shirin baccinsa.
Leƙowa falon yayi.

Tuni tayi bacci bisa kujera sai numfashin gajiya take sauƙewa a hankali baccin kuma mai nauyi takeyi.
A hankali ya iso inda take,
"Ke Tashi kije kiyi wonka".
Yace yana kallonta.
Shiru kamar bata da rai ko motsi batayi ba.
Karo na uku ya kuma cewa.
"Ke tashi kije kiyi wonka ki kwanta".
Still ko mitsin batayi ba.
A hankali ya É—an sunkuyo kanta.
Hannunshi yasa ya É—an kamo hannun ta tare da cewa.
"Tashi kije kiyi wonka zakiji sauƙin gajiyar".
Cikin bacci tace.
"Uhum-Uhum.
Ni na gaji ka barni bazanyi wonka bacci zanyi".
Kanshi ya juya tare da cewa.
"Uhummm yanzuma tsami kikeyi, Ni in bakiyi wonkaba bazan kwana dake É—aki É—aya ba".
Cikin baccin ta É—an kalleshi tare da lumshe ido tace.
"Ni Ko sati nayi banyi wonkaba bana tsami, kuma ni zan kwana a nan kaje can É—akin".
Da sauri yace.
"Rufe baki yarinya ko yaushe bakinki baya shiru.
Muje kiyi wonka".
Komawa tayi ta konta, tare da lumshe idanunta, da suke cike da bacci mai nauyi da gajiya tuni ta meda baccinta".
Juyawa yayi ya koma Bathroom ruwan É—umi mai É—an zafi sosai ya cika baf É—in kana, ya fito.

Gefenta ya zauna.
A hankali yasa hannunshin ya fara zuge zip É—in rigarta,
shiru tayi tana baccinta.
Ƙarasa zuge zip ɗin rigar yayi tare da cewa.
"Tashi! Tashi!! Zan tuɓeki fa".
Shiru kakeji kamar bata da rai".
Kanshi ya jingina da kujerar.
Kana ya fara yin ƙasa dashi tare da ɗan ɗagota ya jinginata da jikinshi.

Still tana baccinta.
Ƙasa yayi da rigar ya cire mata hannayen ya rage bra ne a ƙirjinta, ɗan jawota yayi ya kifeta kan cinyarshi ya ɓalle masaƙalin yayi kana ya ɗan ɗagota ya cireshi a hankali.
Yana cewa.
"Tashi to! Tashi kinji!".
Shiru abinta, É—an gajeren tsaki yayi tare da.
Manna bayanta da ƙirjinshi.
Chapter 124 · 0% Book details