← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 183

Sashe 121

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da kunya tace.
"Hijabin ya sarƙafe min ɗan kunne".

Bai tanka mata ba, sai hannunshi yasa ya buÉ—a hijabin.
Ya maidashi a hankali yasa yatsunshi biyu, yana cire É—an kunnen.

Matsota ya kumayi, kana ya samu ya warware garkuwan É—an kunnen daga jikin yadin hijabin.
Sai kuma yasa hannunshi ya cire mata hijabin duka.

Ya zama daga ita sai wondon dake manne a jikinta.

A hankali ya sunkuyo ya ɗauki rigar tata, sannan ya juyo ya zama tanata cikin falon shi yanata baƙin ƙofar shiga,
Yayi mata ƙawanya da jikinshi.

Idonta a sunkuye, hannunta na saman caɓɓullenta.
Zura mata rigar yayi a wuyanta.
Cikin nitsuwa ya buÉ—e hannun rigar na dama ya sakamata cike da takatsantsan.
Sannan a hankali yasa hannunshi ya kamo hannunta na hagun ya saka mata hannun rigar.

Cikin hikima ya sake rigar tayi ƙasa, sannan a hankali ya juyo bayanta, dai-dai ta wuyan rigar yayi kana yaja mata zip ɗin.
ÆŠan sunkuyowa yayi ta kafaÉ—anta, ganin gaban rigar bai dai-dai-ta yadda ya kamata bane yasa a hankali yasa hannunshin cikin wuyan rigar.
ciki da mamaki da tsoro ta rumtse idanunta.
Shi kuwa hannunshi yasa ya dai-dai-ta caɓɓullenta cikin breastcub ɗin.
Kana ya dauki É—an kwalin ya É—aura mata a kanta kamar mayafi kana ya juya ya nufi.
Dinning area yana maijin wani irin yam-yam da tafin hannunshi ke mishi tun sanda ya taɓa caɓɓullenta, hannunshi yasa ya ɗauki goran zam-zam ɗin da ya mata addu'o'in karya sammu.
Gabanta ya dawo, ita kuma tana ta son É—aura É—an kwalinta.
Goran ya miƙa mata tare da cewa.
"Gashi wannan shi zakisha duk sanda kikaji ƙishi.
In kinsha kuma ki É—an shafawa hannun ki mai ciwon".
Cikin yin ƙasa da idonta ta amshi goran tare da cewa.
"Ngd".
Bai tanka mata ita kuma ta juya ta tafi.

A falo ta samu Ummi da Umaymah da Hajia Mama,
suna zaune.
Cikin wani irin yanayi ta kalli Hajia Mama kana tace.
"Ina kwana".
Fuska cike da fara'a tace.
"Lfy lau. Alhamdulillah yau jiki da sauƙi ko?".
A taƙaice tace.
"E".
Daga nan ta wuce.
Hajia Mama kuwa Umaymah ta kalla tare da cewa.
"Khadijah ya lbrin Auren Haroon ne Kam?".
Ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"To aure kam yazo ga mai nisan kwana".
Bayan sallan layya da kwana goma za'a fara bikin".

"A lallai aure kam yazo ga mai nisan kwana".
Hajia Mama ta faÉ—a.

Ita kuwa Ummi murmushi tayi tare da cewa.
"Lallai jihar tsinako zata kwashi baƙi".

Nan dai sukayi ta hira.

Sheykh Jabeer kuwa. A hautsune ya koma bedroom, kan gado ya kwanta tare da yin rubd ciki.
Idonshi ya rumtse da ƙarfi wai ko zasu dena harsasho mishi hoton abinda ya gani.

Kiran da akewa wayarshi ne ya sashi jan tsaki
Karo na uku yanajin kiran yana shiga.
Ya sani babu mai mishi wannan kiran mafarautan sai mutun biyu.
Haroon ko Ahmad wani babban abokinshi É—an kasar Cameroon.

Hannunshi yasa ya amsa kiran tare da danna amsa kuwa.
Tsaki yaja jin Haroon na cewa.
"Kai kace baka son yawan kira, in an kiraka sau ɗaya kuma baka ɗagawa dan wulaƙanci.
Ni kuma gani Sitti ce ta buwayeni da in Kira mata kai taji lbrin jikin amarya."
Cikin sanyi yace.
"Yaushe kaje lamorde julɓe?".

"Yau kwana biyar".

A hankali yace.
"Anya kuwa Haroon in kayi aure bazaka dena aiki ba".

Taɓe fuska yayi tare da cewa.
"Babu mamaki in bar aikin ma inji da amaryata".

ÆŠan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
"Bawa Sitti wayar".

Miƙa wa Sitti wayar yayi.
Cike da kulawa da so tace.
"Muhammad".

"Na'am Sitti ya gida".

Cikin kulawa tace.
"Gida lfy lau. Ya jikin iyalin naka?".

A hankali yace.
"Alhamdulillah".

Da sauri tace.
"Muhammad yaushe zaka kawo min itane?".

"Nima ban sani ba". Ya bata amsa a gyatsine.

Murmushi tayi kana tace.
"Shike nan zan zo ai".

Da sauri yace.
"A a bance ba, ki bari in ta samu lfy zata zo".
To tace tana murmushi tasan yasan in tazo tofa.
sa'idonta yafi na akowa.
Duk motsinshi zata gayawa LamiÉ—o.
Nan dai suka ɗan yi hira kana suka ƙatse kiran.

Da daren ranar kuwa koda suka zo konciya Umaymah tace.
"Aysha tafi É—akin mijinki kar hannun ya tashi dare-dare ya zama kina fita."
A hankali tace.
"Umaymah yau hannun da sauƙi tunda nasha ruwan addu'o'in nan bana jin zogin sosai".

Cikin jin daÉ—i tace.
"To Allah yasa mu kwana lfy ba tashi".
Amin Amin tace kana suka kwanta.

Allah cikin ikonsa da buwayarsa da al'farmar Annabi da al'ƙur'ani a daren sau biyu kawai ta ɗan tashi.
Shima in Umaymah ta shafa mata ruwan dai sai ta koma bacci a take.

Washe gari da safe kuwa,
Cikin mamaki ta kalli Umaymah dake shafa mata ruwan tace.
"Umaymah bakiga kamar kumburin ya raguba".

Siyayan ruwan tayi a tafin hannunta tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Aysha hannufa Alhamdulillah da sauƙi sosai.
Ga mgni kusa dake a bakin mijinki muje anyi ta wahala".
Uhumm tace tare da sunkuyar da kanta.

Ummi kuwa Murmushi tayi.

Koda aka gama breakfast.

Ranar a haka a kaikacen ta daure taci.
Kafin azahar sosai hannun ya lafa.

Yau kuma tunda safe ko inda hanyar Side É—insa yake bata kallaba, in taji zogin ta É—auko ruwan tasha a shafa mata.

Shi kuwa Sheykh ranar tunda safe ya fita bai dawoba sai tara da rabi na dare.

Still yauma an kwana hannun da sauƙin.

Washe gari da safe.

Sheykh ya kuma É—auko wani zam-zam É—in da ganyen magarya guda bakwai,
Yazo yana mata tofin cikin ruwan.
Yana mgnar zuci.
"Uhum jiki yayi sauƙi zamu huta da koken masifa da shogoɓar tsiya".

Koda ya gama yaje ya ajiye a Fridge kana yazo.
Ya shiga wonka kasan cewar yau Monday ne tushen aiki ko nasara na tsoronta.

Ya fara kimtsawa.

Ita kuwa a falon bayan sunyi breakfast,
suka dawo nan cikin falon, juyowa tayi ta É—an kalli Umaymah dake shigowa falon tace.
"Uhum Umaymah ruwan fa ya ƙare".

Shigowa tayi ta zauna gefenta kana ta kalli hannun ya saɓe sosai.
"To kije ki gaya mishi mana, ai bai fitaba, tashi kije da sauri kada ya fita baki gaya mishi ba".

To tace kana ta miƙe ta nufi can.

Tana shiga yana fitowa.
A hankali ta koma gefe ta tsaya.
"Ina kwana". Tace mishi ido a ƙasa

Ta gefen idonshi ya kalleta tare da cewa
"Lfy ya jikin?."

"Da sauki". Tace kana ta É—an kalleshi tare da cewa.
"Yah Sheykh!".
Ido ya É—an zuba mata kana yace.
"Na'am!".

hannunta ta É—an sa ta shafi fuskarta kana tace.
"Uhum dama maganin nawa ya ƙarene shiyasa nace bari in gaya maka".

Hannunshi ya miƙo tare da cewa.
"Inga hannun".

Ɗago hannun tayi ta miƙa mishi.
Amsar hannun yayi kana ya juyo ya nufi tsakiyar falon.
Tana biye dashi abaya.
Bisa kujera ya zauna tare da nuna mata gefenshi.
Zama tayi, duk yana riƙe da hannun,
É—an sunkuyowa yayi ya fara karanta Suratul Baqra yana tofa mata, yana sa yatsunshi biyu yana É—an murza hannun a hankali-hankali, ido ta É—an rumtse tare da motsoshi jin yana É—an jan hannun.

Wash tace a hankali.
Ɗan ƙara murza hannun yakeyi yana tofa mata.
Hannun hagunta tasa ta damƙi damtsen hannunshi na dama.
bai kulata ba yaci gaba da jujjuya mata hannun dan ya lura tana barin hannun a ƙage wuri ɗaya ko yaushe tana naɗe dashi.
Murza hannun yakeyi da ɗan janshi yana miƙar dashi da ɗan ƙarfi.
Wani irin bubbuga sawunta tayi tare motsoshi da kyau.
Tsakanin sawunshi tasa cinyarta ta dama.
kana tasa hannun hagun nata ta maƙaleshi.

duk ta kanainayeshi tako ina.
zuface ta fara keto mata tako ina na jikinta,
Ajiyan zuciya ta fara sauƙewa jin ya sake mata hannun.

Kanta ta manna a damtsen hannunshi tana maida numfashi.

Shi kuwa shiru yayi yana jin yadda take maida numfashi.
Kusa 6 minute kana a hankali yace.
"To É—an sakeni in kin gama hutawa ko".
A kunyace ta É—an zame jikinta ta janye cinyarta.

Miƙewa tsaye yayi yana gyara al'kyabbar jikinshi.
goran ya ɗauko a Fridge ɗinsa kana ya miƙa mata.
Amsa tayi kana suka fito a tare.

Affan suka samu da matarsa Mami.

Suna fitowa Affan ya miƙa tare da miƙa wa Hamman nashi hannu bayan sun gaisane yace.
"Ya mai jikin dai?".

"Alhamdulillah jiki da sauƙi".
ya bashi amsa

Mami kuwa a hankali ta zame ta É—an rusuna cikin girmamawa tace.
"Barka da safiya Hamma ya mai jiki".

Hannunshi ya kai ya É—an shafi kan É—ansu Karami Aliyu tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah jiki da sauƙi. ya yaran?".

Suna lfy tace tare da kallon Aysha dake murmushi jin Affan na cewa.
"Aunty Aysha ya jikin dai yanzu kam hannun bazai faÉ—i bako".

Murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah da sauƙi".

Sallaman su Umaymah Sheykh yayi ya tafi.

Murmushi Mami tayi cikin son matar Hamman nasu tace.
"Ina kwana Aunty Aysha".

"Lfy lau".

"Ya jikin naki". Tace tana kallon hannunta.

"Alhamdulillah jiki da sauƙi sosai ma".
Ta bata amsa.
Tana zama kusa da ita, tasa hannun hagun ta amshi Aliyu wanda Dr Aliyu sukayiwa mai suna.

Affan ne ya É—an kalleta tare da cewa.
"My Aunty ga iyalin nawa.
Ƙanwar Yusuf aboki nane yayar matarshi Zahra ce kuma."

Cikin fara'a da son Mami tace.
"Ayyah yayi kyau Allah ya ƙara zaman lfy da zuriya mai Al'barka".

Murmushi yayi tare da cewa.
"Amin tare daku, mu yanzu wannan na uku fa, ai munyi ƙoƙari ko Umaymah".
Cikin dariya Hibba tace.
"Kai Ya Affan abinma ƙoƙari ne kenan".
Dariya sukayi duka kana sukaci gaba da hira.
Aysha tana jin gamsuwa da gskyar Mami fiye data Aunty Juwairiyya.
Ranan dai anan Mami ta wuni.

Haka dai taci gaba da amfanin da ayatul shifa da zam-zam da ganyen magarya.

Cikin ikon Allah da izininshi.
Cikin kwanaki goma sha biyar hannun nan ya warke ya koma garau.
Har tana shiga kitchen ayi aiki da ita.

Hakane yasa Umaymah ta fara shirye-shiryen komawa tana mai jin sanyi kaÉ—an a ranta.

Yau kwananta ashirin da zuwa, kuma yaune zata koma.
To fa batun ƙomar da zatayi da Hibba ne yasa.
Aysha taji babu daÉ—i.
Chapter 121 · 0% Book details