Sashe 100
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fitowa gida ya nufa sabida bai son yawan hayaniya, kuma zaiyi baccinsa da ya saba dashi, baccin tsakanin azahar da la'asar.
Su Jalal kuma cikin abokansu suka nufa.
Yana dawowa Falon Hibba kaÉ—ai ya samu ta kunna tv tana kallon Film É—in India kamar zai hanata kuma dai sai ya wuce.
Bayan tayi mishi sannu da dawowa.
Yana shiga ɗakin ya tura ƙofar ɗakin ya rufe ba tare dasa key ba.
Kana yasa hannunshi ya kashe fankar, tare da kashe wutan É—akin.
A hankali ya iso bakin gadon. Zare Al'kyabbar ajikinshi yayi ya ajiyeshi bisa gadon.
Kana ya zare jallabiyar jikinshi itama ya ajeta kan gadon ya rage dagashi sai 3 qtr da ƙaramar rigar.
Dan sosai yake jin bacci, sanadin ɗan zafin hadarin dake haɗuwa yayi yawane yasa ya ƙara gudun AC kana.
A hankali yayi taku zuwa, gefen gadon agogon hannunshi ya cire ya ajiye a kan Bedside drower'n dake kusa dashi.
Konciya yayi a nan a ƙasa bisa tayis babu shimfiɗan komai bare pillow.
Wannan tsarinshi ne da yakeyi, wanda yanayin hakane dan tuna konciyar ƙabarin da wata rana zai riskeshi.
Wani lokacin ma, harda AC'n yake kashewa.
Yana konciya ya fara tasbihi yanayi a hankali idonshi na rufuwa, wannene yasa yakeyin bacci a lokacin da yaso.
A can cikin masarautar JoÉ—a kuwa.
Cikin wani irin farin ciki Jalal Jamil suka nufi Side É—in Hajia Mama jin labarin Ya Affan ya dawo daren jiya karfe biyun dare, a bakin Imran
A falo suka samu Hajia Mama cikin tarin bege da kewar É—an uwan nasu Jalal yace.
"Mama wai Yah Affan ya dawo?".
Cikin murmushin tace.
"Eh ya dawo".
Da sauri Jamil yace.
"Yesss Jalal zomu tafi tafi Side É—inshi Aunty Mami an shawo turai an dawo".
Da sauri suka tsaya jin Mama na ce musu.
"Basa nan tunda safe Aunty Mamin naku ta matsa ya kaita gida wai Abban Yusuf ba lfy, to sun tafi can, Aryan ma yazo bai sameshi ba shima ya tafi can duk sun haÉ—e a can".
Da sauri Jalal yace.
"Muje mu É—auko shi dan wlh su Hamma Yusuf da Ya Aryan bazasu barshi ya dawo da wuriba".
Cikin murmushin Jin yadda yaran ke son Juna tace.
"Yanzu kuwa zasu dawo, dan kunsansu duka uku da son daba, sun girmama su basu bar hawa doki da tsereba kuma kasan Yusuf zaice suzo wurin uban gidansa Malam Jabeer".
To da hakane suka É—an gamsu suka nitsu.
A can Dou Gire kuwa samun jikin Abban Yusuf da sauƙine yasa.
Suka shirya suka nufo Masarautar JoÉ—a.
Ummi ma tayi kolliyar sallanta tayi kyau ta fito falon, inda Hibba take.
Shatu kuwa tana ɗakinta lokacin ta gama yin kolliya tasa wani damdatsen Shadda lace mai masifar kyau, Royal blue ne mai kyau da ɗaukar hankali sai zaren lace-lace ɗin da akayi da red and pink guava mai masifar kyau, sai wani irin sheƙin shaddar takeyi tana fidda maiƙon kyau.
Doguwar rigace inrin fitet ɗin nan na zamani mai ɗan karen kai duk inda sirin yanken fisis ɗin yake an bishi da jerin duwasun shuwa riski masu sheƙin Daimond, cib-cib rigar tayi a jikinta.
Murza É—auri É—an kwali tayi irin mai stpes É—in nan
Kana ta tura É—an kwalin kaÉ—an wannan tattausan saje da suman dake konce a goshinta ya fito ras.
Sai ta baya kuma ta tsakiyar É—an kwalin ta bar rami ta fito da jelan gashinta ya konto har kafaÉ—anta ba tare da ta kitseshi ba.
Wasu Æ´an kunne da sarka na azurfa ta saka a wuyanta,
sai wani kekyawan agogon fata rea ƙirar Gucci ta manna a tsintsiyar farin hannunta da yake, ɗanɗase da zanen jan lalle mai kyau.
Gyale rea color mai masifar kyau ta É—an yafa a kafaÉ—unta.
Wasu turaruka kala biyu ta fesa, kana ta kalli muskarta da jikinta a madubin.
Wayarta ta É—auka ta É—an kaikaice ta É—auki kanta hoto ta cikin madubin tayi kyau sosai.
Wasu takalma marasa tudu tasa suma rea color ne.
Tana riƙe da wayarta ta fito falon.
Da sauri Hibba ta miƙe tare da cewa.
"Wow! Wow!! Wow!!! masha Allah Aunty Shatu kin ganki kuwa masha Allah."
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kai gsky amaryar Sheykh ta fito da madarar kyau masha ALLAH".
Ita dai sai murmushi takeyi dace musu.
"Ngd".
Cikin jin kunya.
Hibba kuwa duk takun da motsin da zatayi sai ta É—auke ta hoto.
Daga ƙarshe ta rinƙa yi musu selfi su duka huɗu.
Saida suka gajine kana suka zauna suna hira.
Nan suka kira Umaymah suka sha hira.
Suna cikin hira Ummi ta juyo da sauri jin muryar Affan yana sallama tare da cewa.
"Assalamu alaikum. Ina Umminmu ina amaryar Hamma tuzuru".
Miƙewa da sauri Ummi da Aunty Juwairiyya sukayi tare da cewa.
"La Affan yaushe ka dawo".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Jiya da tsakiyar dare, ina Auntyn nawa".
Ya ƙarishe mgnar yana shigowa cikin tsakiyar falon.
Tafa hannu Ummi tayi tare da cewa.
"Suwa nake gani kamar Yusuf da Aryan".
Cikin dariya sukace.
"MuÉ—in ne dai Ummi".
Cike da jin daÉ—i Ummi da Aunty Juwairiyya ke cewa.
"Kai maraba lale lallai yau munada manyan baƙi , oh duniya Yusuf da Aryan kamar ba kuba".
Dariya sukayi tare da zama a kujeru.
Hibba kuwa tuni ta isa gaban Affan lakace hancinta yayi tare da cewa.
"Sakaliyar Umaymah ashe kina nan bana zakiga shagalin sallan Masarautar JoÉ—a".
Cikin sauri ya kalli Shatu dake ce musu.
"Sannunku da zuwa".
Da sauri ya juyo ya kalli Ummi kana ya kalli Aunty Juwairiyya tare da cewa.
"Wannan ce Auntyn nawa amaryar Sheykh Ustaz Malam Dr Jabeer akarmakallu".
Murmushi Ummi tai tare da cewa.
"Eh itace".
Cikin dariya ya kalli Yusuf da Aryan da suke gaisawa da ita yace.
"Kan bala'i ashe dama Sheykh Hamma Jabeer yana kallon mata kalli yadda ya zaƙulo zankaɗediyar sarauniya".
Yusuf ne ya daki kafaÉ—arshi tare da cewa.
"Kaifa Affan É—an iskane baka da mutunci, baiyi aureba kace mishi. Shugaban tuzuran Afirka.
Yanzu yayi auren kuma zakace yana kallon to dama ce maka akayi shi makaho ne?".
Dariya sukayi baki É—ayansu,
Aryan ne yace.
"Bar Affan da shegiyar surutu".
Dariya suka kumayi kana duk suka zauna.
Suka gaisa cikin tsokana Affan ya kalli Shatu dake danna wayarta tana kallon hotunan da sukayi yanzu yace.
"Aunty Amarya Hamman namu yana nan ne, ayi mana iso wurin shi mu kwashi gaisuwa".
Shiru ta É—anyi tare da kallon Ummi.
Da sauri Hibba tace.
"Eh yana nan yanzu ya shiga".
Kai ya gyaÉ—a tare da cewa.
"To Aunty Sayyada ayi mana sallama dashi ace É—aliban shi ne, Affan, Yusuf, Arya,".
Cikin tsoron kada Shatu ta kuma zuwa É—akin abun da ya faru jiya ya sake faruwa Ummi tace.
"Ai yana bacci ne yanzu ko".
Da sauri Affan yace.
"No ba matsala in ance masa Yusuf ne, tashi kice muna sallama dashi."
Cikin murmushin jin Yusuf da Aryan sunce.
"Eh gsky gwara mu gaidashi kada ya gammu a wurin sukuwa yace bamu nemi izininshi ba".
A hankali tace.
"To bari a gaya mishi".
Ta yunƙura zata tashine Ummi ta riƙe hannunta tare da cewa.
"Shatu kadafa".
A hankali tacewa Ummi.
"Ba komai fa Ummi".
Ganin hakane yasa Ummi ta sake mata hannun tare da cewa.
"To Allah yasa".
Amin Amin Juwairiyya da Hibba sukace.
Shi kuwa Affan cewa yayi.
"Allah bazaiyi faÉ—aba in yaji mune".
Kai Ummi ta gyaÉ—a sabida basu san me take tsoron ba.
Ita kuwa Shatu a hankali ta nufi Side É—insa.
Su kuwa hirarnsu sukaci gaba dayi a falon.
A hankali ta tura ƙofar falon nashi ta shiga.
Shiru babu kowa babu komai sai sautin ac dake tashi fuuuhhh.
A hankali ta lumshe idonta kana cikin sanyi ta nufi ƙofar ɗakin nashi.
Tare da cewa.
"Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Salamu alaikum!!!".
Shiru babu motsin komai, hakane yasa a hankali tasa hannun hagun ta dafa ƙirjinta dake bugawa.
Kana tasa hannun damanta ta tura ƙofar Bedroom ɗin.
Sai kuma gashi ta buɗu ƙofar.
Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sauƙe jin wani irin masifeffen ƙamshi da sanyi daya ratsa mata jiki da zuciya.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
A hankali ta cusa kanta cikin É—akinta da yake duhu.
Wani irin bugawa ƙirjinta keyi kana.
Kanta na sarawa da masifan ƙarfi.
A hankali ta juya gefen mashigar É—akin hannun tasa ta lalubi abin kuna wutan É—akin danna É—aya daga ciki tayi,
hakan yasa ƙoyin wutan ɗaya mai kalar Sky blue ya kawo wuta.
Sanadin hakane ɗakin ya kawo wani irin haske mai ƙayatarwa.
Yanayin wutan É—akin labulayen da kayan jikinta dana jikinshi sukazo iri É—aya.
Juye- juye tayi tare da cewa.
"To ina yak".
Shiru tayi bata ƙarisa rogowar mgnar ba hangoshi can ƙasa yana konce rigingine yayi pillow'n da tafukan hannunshin.
A hankali tayi taku uku zuwa biyar ta matso kusa dashi cikin sanyin da ya fara yimata yawa ga cikinta dake tsuma a hankali tace.
"Salamu alaikum".
Ko motsi baiyiba bare tayi zaton zai amsa.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
Ganin hakane ta matso a hankali take takun saÉ—ab-saÉ—ab take taka sawunta a hankali har ta isa kusa dashi.
Da sauri ta zubawa ƙafar damanshi ido.
Ajiyan zuciya tayi mai sanyi tare da mgnar zuciya.
"Uhumm ashe dama yana komciya a ƙasa haka babu shimfiɗan komai ba pillow, da kuma ƙaramar riga da wondo iya guiwa."
A hankali ta iso gab da kanshi,
Cikin yin numfashi a hankali wai karya jita, ta rusuna ta zauna bisa sawunta irin zaman yin tahiyan salla.
Cikin ƙurawa babbar yatsar ƙafar damanshi inda ta rinƙa biyo wannan zanen macijin dake kwance lib a ƙafarshi.
Da ido tabi zanen har kan guiwarshi inda iya nan wondon 3 qtr ya rufe.
A hankali ta ƙara sunkuyowa ta kurawa wurin ido, tare da mgnar zuciya.
"To iya ina wannan zanen tafiyar macijin ya tsaya ne a jikinshi?".
Jim kaÉ—an tayi kana a hankali.
Ta miƙa hannunta, cikin sanɗa a hankali hankali tasa yatsunta biyu ta kamo bakin ƙafan wonɗon ta ɗan jawoshi a hankali tayi sama das...!