Sashe 4
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
...Bayan shekaru Goma sha biyu...
Cikin Ƙasar Kautal A Jihar Æadamaya state.
A wani yanki na Æadamaya state, cikin Shikan local Government area a wata rugar FULANI mai suna.
*RUGAR BANI*
Garin Shikan wani yankine daga yankunan Æadamaya yankine mai tarin Æ™abilu ma banbanta addinai da al'adu wanda duk yankun Æadamaya shida Bimu sune sukafi tarin Æ™abilun sai dai babbancin mafiya yawan kabilun Bimu musulmaine saÉ“anin mafiya yawan Æ™abilun Shikan kafurine maÆ™iya Allah da Manzonsa.
Shikan shine sashin da yafi tara ƙabilu mafiya yawa, masu baƙaƙen zuciya ƙabulun da hasken addini bai cimmusuba.
Ƙabila mafi rinjaye a yankin Shikan itace Æ™abilar É“achama. Mafi akasari Æachamawa mutanene kafurai ne marasa É—igon imani a zuÆ™atansu marasa son zaman lfya, mugunta da kisa shine abinda ke sasu farin ciki, abinda kawo ya sanine duk sanda akaji jihar Æadamaya cikin wani tashin hankali to daga Æ™abilar É“achama ne.
Duda yawan ƙabilu na garin Shikan hakan baisa fulani sun sakar musu garinba, domin tushen garin na fulanine, sabida kowa yasan makiyayi basa nesa da wurin damshi da ruwa, domin rayar da ababen kiwonsu.
Haka yasa akwai musulmai Hausawanmu da tarin yawa cikin garin Shikan, wanda duk rintsi da wahala sunƙi barin garin, koda yake hakan baya rasa nasaba da irin al'barkatu da ni'imomin da Allah yayiwa garin.
Daga gefen. Garin Shikan akwai babban kogin da yakeda ruwa biyu wanda ko wucewa zakayi ta kan babban gadan da titin da zai kaika cikin Æadamaya zaka hangi ruwane kala biyu a kogi É—aya basu kuma taÉ“a haÉ—ewa wuri É—aya ba da izinin ubangiji.
Gefen kogin ta dama wata babbar *Rugar fulani mai suna Rugar Bani* ce mai tarin tarihi, rugace mai girma wacce Ubangiji ya Æ™awatata da ababen buÆ™atar yau da kullum, wannan Ruga itace yanki mafi sanyi a yanki Æadamaya state rugace damu fulani muke ce musu *JOTTAN MA'EN* Bi ma'ana fuli mazauna wuri É—aya, ba ire-iren fulani makiyaya masu tafiye-tafiye bin rugageba, fulanin Rugar Bani fulanine makiyaya masu tarin dabobi masu tarin yawa, Rugar Bani Rugace da aÆ™alla fulaninmu sunyi sama da shekaru dari da ashirin awannan Rugar, shiyasa harda gini zamani da kyawawan gidaje fulanin sukayi, yayinda kuma akwai bokkokinma a cikin Rugar tasu wanda kuma suka sayi filin da kuÉ—insu zufansu a hannun sarkin Shikan na wancan zamanin ya sayar musu yankin wurin gaba É—aya sun biya kuÉ—insu ya kuma basu takardu su, suna zaune a nan suna noma suna kiwo.
Rugar Bani na zagaye da Æ™auyukan Æ™abilun Æachamawa da tarin yawa, wanda nan gefensu Æ™auyen Bonon yake wanda nanne dodon tsafin Æ™abilar É“achamawan take wanda sunan dodon tsafin nasune suka sawa suna Æ™auyen suna Bonon. Kauyen Bonon shine zuciya da karfin kafuran nan, sunyi imani dashi, fiye da zaton mai zato, koda laifi wani yayi bonon ake kaiwa Æ™ara kuma muddin bonon ya tsinewa mai laifinsun to zai lalace ya É—ai-É—aice dashi da zuriyarsa baki É—aya, da yake sunyi imani da hakan kuma yana faruwa suna gani shiyasa bonon yake tamkar zuÆ™atansu, kamar dai yadda in jikin É—an adam idan zuciya ta É“aci gagganji na É“aci to haka bonon take a wurinsu... Wannan kenan
Rugar fulanin Bani yafi ko wani yanki na Æadamaya sanyi mai É—an karen daÉ—i.
Koda yake hakan ya samune sanadin ƙawanya da wani babban dutse mai fesar da numfashin sanyi yayi musu, wanda ya kasance musu tamkar rufar garin.
Gefen hagun Rugar Bani kuwa wani babban fadama ne mai cike da lamɓu mai ɗauke da ababen more rayuwa wanda ya kasance mallakinmu Fulanin Rugar Bani, lambun yana da duk wasu kayan marmari kamarsu.
Lemu, mangoro, gwaiba, ayaba, dabino,kwakwa, kashu, kankana, abarba, da jefi-jefin tuppa da inabi.
Wanda wannan fili yake mallakin Fulanin Rugar Bini'nne, kana bayan filin kuma akwai wani rafin da ya kasance masarrafin noman shinkafawa ne wanda suke yinshi noman rani da damina, kuma shina mallakin Fulanin Rugar Bani ne, wanda komawa yasan iya filinshi,
Daga gaban Rugar Bani kuwa kogin Shikan ne malale a gabansu iya ganin mai hange da ido biyu gefen hagunsu kuwa nan garken shanunsu ke shimfiÉ—e bila adadin.
Rayuwar Fulanin wannan Rugar rayuwace mai cike da aminci da amana da hakuri da kauda kai duk da tarin zalunci da kafurai Æ™abulun Æachamawa keyi musu.
"Kamar yadda duk kowa ya sani duk duniya anyi ittifaƙin ba fulatani ko ba fulatana basa neman tsokana ko tada husuma bare tada zaune tsaye. Akan cutar da bafulatani yayi kamar bai san an cutar dashi ba ko bai ganeba, wannan dalilin yasa duk ƙabilun ƙasar Afirka sukeyiwa ƙabilarmu kallon wawaye ne ko basu san abinda sukeyiba ko sokayene, masu ƙarancin wayewa Gidadawa.
Mu kuwa a namu sashin fulani mun kasance masu kauda ido kan cutarwar forko data biyu, sai dai a haƙiƙinin gsky bama lamunta ko jurar cutarwa ta uku! Domin rama cuta ga macuci ibadace. Kuma Ba'a sarar mumini a rami ɗaya sau uku".
Wannan shine jawabin da wani farin dottijon bafulatanin dake zaune tsakiyar al'ummar wannan rugar bayan sun dawo daga jana'izar mutun ɗaya da ƙabilun ɓachama suka kashe musu cikin sunkuru, a daren jiya wanda ya kasance ɗane ga Arɗon Yabani shugaban Rugar tasu kenan.
Hannu yasa ya share zafafan hawayenshi dake kwaranya daga ida nunshi cikin É—aga sauti yaci gaba da cewa.
"Fulani basa ɗaukar mataki domin yaƙi ko zalumci sai dai dan kare kawunansu. Kuma kun sani duniya duk ta sani FULANI BA ƳAN TA'ADDA BANE! Ba ƴan bindiga daɗi bane, makiyayene masu ƙare rayuwarsu dan samawa mazauna cikin birane jin daɗin rayuwa, muyi kiwo mu kai musu suci naman susha madarar shanu kana muyi noma mu ciyar dasu.
Meyasa su mutanen birane basa É—aukar matsalarmu tasu matsalar ana kashemu tamkar kiyashi kuma babu masu kulawa".
Tsagaitawa ya ɗanyi tare da shashsheƙa cikin bada umarni a matsayinsa na shugaban Rugar uban wanda aka kashe kuma yace.
"Na roƙeku da Allah kada wanda ya ɗauki makami domin ramuwa duk da munga yankan rago akayiwa Hashimu amman bamu san wayeba kuma bamu da hujja, dan haka kada wanda yace zai ɗauki makami.
Muyi rubutu mu aikawa maimartaba sarkin Æadamaya, domin Al'Æ™alami yafi tokobi, mu kai kukanmu gareshi, tunda shi sarkin wannan yanki na Shikan mun kai mishi kukanmu a karo na barka tai bai kulaba, kuyi hakuri mu miÆ™a lamarinmu ga sarakuna mu, inada yaÆ™inin zasuyi mana adalci".
Shiru mutanen da aƙala sun kai ɗari da ashirin sukayi.
Yayinda kowa ya keta zubda hawaye.
Sai É—aya daga cikine da ya kasance baÆ™in jakada Æachama ruwa biyu uwarshi Æ™abilar É“achama, wacce ubanshi bakura babarbaren borno wanda shike saida kanwa a rugartasu ya auro Uwar Ba'ana. yana naÉ—a komai a wayarshi,
domin miƙawa shugaban mayaƙan ƙabilar ɓachama, komai ya gani, domin shi ɗin ya kasance, makashinsu ne kuma taburmarsu ne, domin dama bahaushe yace sai da ɗan gari akanci gari da yaƙi!...
A cikin babban birnin Æadamaya kuwa. *Land of beauty* Garin Modibbo JoÉ—a,
Mai tutar fulɓe garinda duk arawacin ƙasar Kautal mune kaɗai muka rage da tutar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo.
Wanda ya dasashi ya kafashi da hannunshi masarautar fulbe mai ƙarfi Masarautar Joɗa...
Cikin birnin matsarautar JoÉ—a.
A cikin babban birnin Æadamaya.
Wasu irin tsala-tsalan motocine wanda a Æ™alla sun kai Goma suke jere suna fitowa daga harabar shaharerriyar makarantar Jami'a ta dake cikin babban birnin Æadamaya wato J.U.B JoÉ—a University Æadamaya
Yayinda suke tafiya a jere a jere cikin tsananin gudu tamkar zasu tashi sama kana ga jiniya daya karaÉ—e illahirin sashin wurin wanda dole yaja hankali duk wanda ke wurin gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama da titin.
Motoci huÉ—une a gaba, wanda suka kasance masu kyau.
Sai wata Rolls Royce, mai kuɗi kimanin naira million 4, 959,630. Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai sheƙi da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine ƙal sai glass ɗinta daya kasance tin tek mai duhu.
Wani kekyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa.
Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin Super Nour a jikinsa wanda a ƙalla zai kai tamanin ɗ kuɗinshi, ya ɗaura baƙar al'kebbarsa ta jinin larabawan saudia Al'kebbar baƙace mai faɗi, kana yasa farin hirami a kanshi da zagayen baƙin saman hiramin.
Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido, wani irin tsabtaceccen gemune da bazai wuce kamu ɗaya ba ne yayi lib a haɓarsa.
Zaune yake cikin motar ya jingina bayanshi da sit É—in, ya lumshe fararen idanunshi,
A hankali yake motsa tattausan jajayen laɓɓansa yana tasbihi.
"Subahanallahi wal'hamdulillah wa la'ilahaillah Allah Akbar, Astagafillaha wa'atubu ilaik".
Yanaji a jikinshi kudun da akeyi yayi yawa, to amman dolene ayi irin wannan gudun domin lokaci na gab da ƙurewa, dan sosai sallan jumma'ar ya gabato, yasan yanzu masallacin ya fara cika, wannan dalilin yasa bai hana drevernshi gudunba, kuma bai hana fadawanshi sakin jiniyarba, dan ta hanyar jiniyarce zaisa a basu hanya su samu su isa kan lokacin daya dace.
Bawai ya bari ayi jiniyar da gudun dan nuna isa da ɗagawa bane, sai dan son isa masallacin Masarautar Joɗa da yake limanci kuma yake gabatar da Hudubar jummar matuƙar yana ƙasar tiyatar da yayiwa watace ya sa lokaci yaso ƙure mishi.
Motoci, biyar kuma na bayanshi wanda uku daga ciki na É—aliban J U B da ya fitone, wanda yana aiki cikin Hospital É—in makarantar, bayan kuma asibitinshi da kuma Genaral Hospital Æadawaya da yake zuwa sau É—aya cikin ko wanne sati.
motoci biyun bayanshin kuma, Jalal ne da abokanshi.
Shiyasa motocin suka taho a jere-a jere dan shi bai fiye yarda ya fita da mota sama da biyarba, suma ba kullum ba, wani lokacinma yakan fita shi É—aya.
A haka dai har suka fara ratsowa cikin Æadamaya, a dai-dai mashigar laleko ne,
Cunkoson ababen hawan ya yawaita, yayinda suka danno kai wurin yasa da yawa suka fara komawa gefen titi suna kauce musu dan basu hanya dan jiniyar dake musu nunin akwai uzurin gaggawa ga kuma fadawa a motocin.