← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 183

Sashe 56

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan falonshi suka zauna, shida Haroon.
Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace.
"Yauwa Gimbiyar LamiÉ—o kizo kiyiwa wannan jikan naki faÉ—a".
Murmushi tayi mai ƙayatarwa,
a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi.
A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna,
cikin sanyi ya kalleta.
Ita kuwa cikin kulawa tace.
"Jabeer, ya jikin naka".
Cikin harshen fillanci yace.
"Da sauƙi".
Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace.
"Yaci wani abu kuwa?".
Da sauri yace mata ehh.
Cikin kula tace.
"Me yaci!?."
Murmushi yayi cikin tsokana yace.
"To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa".
Dariya ta É—an yi tare da cewa.
"Taso kuzo kaci abinci".
Kanshi ya girgiza mata tare da cewa.
"Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina.
In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka".
Murmushi tayi tare da cewa
"To naji taso muje kaci wani abun".
Dai-dai lokacin LamiÉ—o da Galadima suka shigo.
Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.

Bayan sun zauna ne LamiÉ—o yace.
"Ya ƙarfin jikin?".
Rai a ɓace yace.
"Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani".
Murmushi LamiÉ—o yayi cikin tsokana yace.
"To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?".
A hatsale yace.
"Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin."
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama".
Da sauri ya É—ago kanshi daga kallon Tab É—inshi ya zuba musu tare da nuna kanshi.
Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace.
"Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin.
Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba."
Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaÉ—arshi tare da cewa.
"A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah".
Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru.
Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.

Bayan sun tafine.
Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya É—anci abinci.

Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.

A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa.
Saida akayi sallan la'asar kafin suka isa sashin, Jabeer.
Sosai suka nuna mishi kulawa da gata,
Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole.
Hajia Mama kuwa daÉ—i kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.

Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.

Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.

Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.

A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.

Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu
Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.

Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin É—an Æ´ar uwar tata É—a mafi soyuwa a gareta sama da Æ´aÆ´an data haifa a cikinta ma.

Yau kwana biyar da faruwan abun.
Sosai jikinshi yayi ras.

Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.

Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba'ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.

Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani.
Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.

Yakanji kamar ya faÉ—i ya mutu in ya tuna garin.

Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.

Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer,
A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al'kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al'kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina.
Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara,
Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi.
Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki.
A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya,
Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace.
"Masha Allah, ÆŠan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka".
Kanshi ya É—an kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace.
"Sun isoma".
Cikin jin daÉ—i tace.
"Eh haka dai Jamil ya gaya min".
Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace.
"Ya Jabeer ya jikin?".
Cikin jan gajeren tsaki yace.
"Lfyata lau".
Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi.

A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya.

Suna fitowa harabar Side É—in shi.
Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne,
sai yau ya bawa Haroon key É—in ta yace a É—auko mishi Umaymahnshi, shi bazai je É—aukotaba sabida.
LamiÉ—o yace bazai fitaba.
A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars.

Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi.
Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buÉ—e marfin motar.
Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace.
"Marhababuki ya Umaymah, ta faddal".
Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito.
Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daÉ—i ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi.
Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje,
kanshi ta shafa tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani".
Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah.
suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito.
Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa.
"Ta É—anki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye".
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi".
Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa.
"Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata".
Hannunta tasa ta É—an zunguri Haroon tare da cewa.
"Kishi".
Jamil ne ya É—an kallesu lokacin da suka É—unguma suka nufi Sade É—in Jabeer cikin tura baki yace.
"Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi.
Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin".
Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa.
"To Jamil harda kai, wato kaima É—an team É—in Haroon ne ko?
To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da É—aba, ko Hajia Mama?".
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace.
"Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba,
Gaba É—aya Jabeer ya kwace mana ke".
Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba É—ayansu lokacin da suka shiga cikin falon.

Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi.
Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya É—anyi murmushi.
Aunty Juwairiyya ce ta É—an kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace.
"Matar ƙani yau tun safe ban jikiba".
Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi.
Cikin happy tace.
"Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa".
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata".
Kanta ta É—an juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci.
A ranta take addu'o'in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi.
Tattausan Lips É—in shi masu kama da kunnen fure ta kalla.
sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai.
Allah ya sani randa ta samu lips É—in nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haÉ—iyesu.
Chapter 56 · 0% Book details