← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 183

Sashe 67

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Shatu cikin rawan jikin jin idanun mutane na yawo a jikinta dan ma Allah yasa akwai niƙab a fuskarta.
Take bin bayanshi. Shi kuwa Sheykh Jabeer yadda suke ƙara matso inda yake haka bugun zuciyarshin keta tsananta.
Suna isa gaban Lamiɗo Bappa ya miƙawa Lamiɗo hannunta cikin sanyi da nitsuwa da taushin lafazi yace.
"Allah rene, ga Aishatu matar Muhammad Jabeer.
Gata amana bisa jagoranci ka, nasabarka da yardarka.
Da kamala da nitsuwa da na gani a fuskar yaron yasa naji ƙarfin guiwar baku aurenta.
Ba tare da fargaba ba, yanzu kaine kaka kuma jagora a gareta".
Sai ya kuma nuna Barrister Kamal da shima yana cikin wakilai, shi a zatonsa ma shine mahaifin Jabeer cikin sanyi yace.
"Kai kuma kaine matsayin mahaifi a gareta ku zame mata dangin ta data rasa, naso ace da mata a masu ɗaukanta, dan in danƙa amanarta a hannun macce yar uwarta.
Amman ba komai, na baku amanarta dan Allah kada a cutar da ita, domin nima ta kasance amanace a uwurina, domin Æ´aÆ´an mu da muka haifama amanace Allah ya bamu kuma abun kiyayewa, bare kuma É—iya irin Shatu É—iyace da take da nasabobi masu yawa a gareni".
Cikin gamsuwa Lamiɗo yasa hannunshi ya amshi hannunta daketa karkarwa, tuni niƙab ɗin fuskarta ya jiƙe jilak da ruwan hawaye.

Cikin Dattaku LamiÉ—o yace.
"In sha Allah zan kula da dukkan lamuranta tamkar yadda nake kula dashi Jabeer, kuma kada ka damu akwai masu meye mata gurbin uwa ƙanwa yaya dama duk danginta a cikin masarauta Joɗo, baƙoma baya kukan maraici bare kuma, matar sashin jinina".
Cikin sanyi da wasu hawaye Bappa yace.
"To Ngd matuƙa".
ArÉ—o Bani ne ya dafashi tare da cewa.
"Ka sanya mata al'barka a cikin aurenta ba zubda hawaye ba."
Sosai Haroon ya zuba mata ido.
Shi kuwa Sheykh Jabeer da mamaki yake kallon Bappa dake zubda hawaye.

A hankali su Bappa suka É—an ja da baya.

Shi kuwa Lamiɗo ya juya ya nufi motar riƙe da hannunta.
Haroon ne yayi saurin buÉ—e musu marfin motar, suka nufoshi gadan-gadan.
Jalal kuwa ido ya zubawa yatsun hannunta da Lamiɗo ke riƙe dashi.

Shi kuwa Jabeer idonshi ya rufe da ƙarfi. Sai kuma ya buɗesu, dai-dai lokacin Lamiɗo ya kawota bakin ƙofar motar tare da cewa.
"Mamana kiyi bismillah ki shiga da ƙafar dama".
Cikin shessheƙan kuka ta gyaɗa kai tare da yin bisimilla kana ta ɗan sunkuyo, sai kuma kukan ya kubce mata.
Shi kuwa Jabeer da sauri ya buɗe marfin motar ta gefen hagunshi. Kamar gilmawar walƙiya ya fita cikin motar.
Dai-dai lokacin da Shatu tasa ƙafarta ciki.
da sauri yasa hannunshi ya buɗe motar Jadda tare da shigewa ciki yaja marfin ya rufe sabida ji yayi zuciyarshi zatayi bindiga, wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi.

Ita kuwa Shatu, a hankali ta shiga ta zauna, don batama lura da shi bane tabbas dai taga mutun ya fita cikin motar.
Tana shiga Haroon ya maida marfin ya rufe
Shida LamiÉ—o suka koma sit É—in bayan wannan sabida su a zatonsu Jabeer na ciki.

Ganin LamiÉ—o ya shigane yasa duk kowa ya shiga motarshi.
Hakama Jadda ya shiga ya zauna hankalinshi na woje.

Sai da akaja motocin suka fara tafiya ne, ya juyo da sauri jin Jabeer na jan wani ja'irin tsaki mai tare da ajiyan zuciya.
Cikin mamaki Jadda yace.
"Haaahh kai kuma Meya kawoka nan? Yaushe ka shigo min mota!?".
Bai kula Jadda ba, asalima yi yayi tamkar bai jishiba.

Haroon kuwa cikin dariya ya É—an bugi sit É—in da yake zaton yana wurin cikin juya harcen Larabci yace.
"Masha ALLAH, gasar ShaÉ—i tayi mana rana mun rabaka da gwauranci".
Murmushi LamiÉ—o yayi tare da kallon Haroon yace.
"Saura kai". Murmushi yayi tare da cewa.
"Ni ai nan kusa za'ayi".
Jin shirune, yasa Haroon yayi shiru,
Azotonshi ya ƙin mgna da shariyar ne suka zowa Jabeer bare, yasan yanzu a cike yake.

Su Jalal kuwa kab da al'hini suke tafeyi.

Jadda kuwa yayi iya mgnarshi yayi shiru ganin bai kulashi ba.

A haka suka isa cikin Masarauta JoÉ—o.

Suna isa kuwa Jabeer ya fito ya nufi Side ɗinsa, fitowarsa cikin motar Jadda ne yayi matuƙar bawa Haroon da Lamiɗo mamaki.

Haroon kuwa bayanshi yabi da sauri.

Suna shiga Side É—insa kuwa suka samu babu kowa.

Suna gama tsayuwa Sallama ya nufi Side É—in Gimbiya Aminatu bisa umarni LamiÉ—o.

Yana shiga a babban Falon ya samu. Umaymah, Ummi, Aunty Juwairiyya, Hibba, Adda Rumana wacce take yayarsu Jabeer yar farin Abba kenan, sai mai bin mata Rumaisa.
Kana sai Gimbiya Aminatu dake tsakiyarsu, sai hadimanta.

Koda ya sanar musu, sun iso.
Kusan duk a tare suka miƙe sai Gimbiya Aminatu ce bata tashiba da hadimanta.

Su kuwa da sauri suka nufi woje, Umaymah ce gaba sai Aunty Juwairiyya dake biye da ita a baya riƙe da wani tire wanda samanshi ke ɗauke da al'kyabbar irin tasu ta matan masarauta da kuma wasu sauran tarkace.
Suna fitowa motar na isowa har bakin wurin. Da sauri suka nufi jikin motar.
Ita kuwa Zuwa yanzu ta tsagaita da kukanta, sabida ababen da take gani a cikin masarautar ya shallake tunanin mai tunani,
gaba É—aya jikinta tsuma yakeyi, sabida idonta na gane mata ababe na ban tsoro.
Cikin ranta take mgnar zuci.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, wannan wanne irin gidane? Me yake faruwa da mutanen masarautar? Sunko san gskyar junansu?".
Da sauri ta rumtse idanunta sabida wasu irin hayaƙi da take gani yana tashi tako ina na gidan yayiwa gidan rumfa gaba ɗayansa.

A da sauri ta buÉ—e idonta jin an kamo tafin hannunta,
Umaymah kuwa cikin tsantsar jin daÉ—in da farin ciki maras misaltuwa tace.
"Marhababiki ya binti". Wani irin azabebben tsinkewar zuciya da firgici da razanine ya daki zuciyar Shatu a lokaci É—aya.
Da sauri ta ƙara ware idanunta, dan son kallon matar da take jawota tare da cewa.
"Kiyi bismillah ki fito da ƙafar dama, ki riƙe hannuna da kyau ɗiyata, ki kalleni nan nice jagorarki ki taka ƙafarki a inda zakiga na taka tawa".
Ido ta zuba mata, tare da fitowa a hankali.
Tana fitowa bakin ƙofar Umaymah tasa hannu ta amshi al'kyabbar da Aunty Juwairiyya take miƙa mata.
Kangeta tayi kana tasa mata al'kyabbar, sannan ta gyara mata rufuwarshi da kyau ta rufa mata hularshi. Yadda sam mutun bazai samu damar ganinta ba.

Ga niƙab ga kuma hular al'kyabbar da lu'ulu'u danke reto a fuskarta.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta matso tare da cewa.
"Marhabin yar uwarta, Alhamdulillah yau kam na samu yar uwa".
Adda Rumana ce ta matso kusa da ita tare da yin mgna da fillanci tace.
"Sannu da zuwa Masarautar Joɗa ƙanwata".
Adda Rumaisa kuwa murmushi yaketayi tare da matsowa, haka suka sata a tsakiya.
Jakadiyarsu kuwa sai bin takun ƙafar Shatu takeyin da ido.

A haka suka zagayeta, kana hadimai suka mara musu baya.

A haka suka isa babban falon Gimbiya Aminatu.
Suna isa Umaymah ta kaita har gabanta ta ajiyeta,
Cikin tsantsar jin daÉ—i tace.
"Alhamdulillah Gimbiya yau dai ga sabuwar Gimbiya dan yanzu itace amarya ba keba".
Cikin dariyar jin daɗi Gimbiya Aminatu tasa hannu ta kamo hannun Shatu da Umaymah ke miƙa mata tare da cewa.
"Kishiya ban haushi, ta isa ta zama Gimbiya zakisa yanzu in korata woje".
Dariya sukayi baki É—ayansu.

Yayinda tuni hadimai mata suketa jere ababen maƙulashe a gaban Shatu.
Danginsu, Zuma, Madarar shanu, Da Æ´aÆ´an itatuwa masu sanyi.
Ita dai Shatu ƙasa tayi da kanta,
tana jin fargaba da kuma tsoron wannan bahagon gidan data shigo.

Su kuwa nan sukayi ta mata hidima da nuna mata so.

Ganin magriba ta ƙara to ne yasa,
Umaymah ta jawo hannunta ta kaita wani É—aki dake nan kusa dana Gimbiya Aminatu.

Tare da cewa.
"Yauwa É—iyata kiyi salla. Za'a kawo miki abinci, kada kici komai sai nazo".
Cikin sanyi ta gyaÉ—a mata kai.
Ita kuwa Umaymah hannu tasa ta fara zare mata al'kyabbar, koda ta cire mata shi, cikin kula tace.
"Cire niƙab ɗin, babu mai shigowa nan yanzu sai nida Gimbiya Aminatu da Juwairiyya sai Jakadiyarsu".
A hankali tace.
"To".
Haka nan taji duk wani yarda na duniya ta sauƙeshi kan wannan kekyawar mata mai fara'ar nan.

A hankali tasa yatsunta ta kamo niƙab ɗin ta ɗin ta yayeshi.

Wasu irin tagwayen numfarfashi Umaymah ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!".
Da sauri ta juyo ta ruggume Jakadiyarsu a hankali tace.
"Alhamdulillah Ummin Jabeer itace. Wlh itace".
Cikin wani irin tarin jin daÉ—i Jakadiyarsu ta É—an kalli Shatu, tare da yin murmushi mai cike da ma'anoni.

Jakukkunan dake hannunta ta ajiye, kana ta iso kusa da ita ido ta zubawa fuskarta kana tace.
"ÆŠiyata menene sunanki?".
Cikin yin ƙasa da ido Shatu tace.
"Aysha".
Kusan a tare sukace masha ALLAH.
Nan Umaymah kam ta juya da sauri ta fita.

Ita kuwa Jakadiyarsu Jabeer shirya mata kayan data shigo dasu takeyi a drower'n.
Tare da bata umurnin taje tayi al'wala.

Umaymah kuwa tana fita kai tsaye Side É—in Jabeer ta nufa.

Shiru ba kowa, da kamar duk sun tafi masallaci ne.

Aunty Juwairiyya da Hibba kuwa suna sashin Juwairiyyan.
Ummi kuwa na can wurin Shatu.

Kai tsaye É—akin da nanne masaukin ta, ta nufa.
Bathroom ta faÉ—a ruwa ta É—an watsa tare da yin al'wala kana tafito tazo ta kabbarta sallah.

Ita kuwa Shatu zaune take bisa sallayan.
Tunda ta idar da sallan bata tashiba.
Sai kanta data jingina jikin gadon da take gefenshi.
A hankali ta rumtse idanunta tare da motsa laɓɓanta tana karatun al'ƙur'ani cikin sanyin murya, Ummey da Junainah ne suka faɗo mata a rai shine ya sata zubda hawaye wasu na korar wasu.
Kewarsu da begensu, ya tuno mata su Ya Gaini da marigayi ya Lado.
Ummi kuwa itama bisa sallayan take tana lazumi.

A haka har lokacin sallan isha'i yayi.

Jin wata zazzaƙar murya mai matsifar daɗi na karatun.
Hannun tasa ta share hawayenta dan jin karatun takeyi yana ratsa mata zuciya ya tsananta zubar hawayenta.

A hankali ta miƙe itama ta kabbarta sallan isha'i.
Hakama Ummi.
Chapter 67 · 0% Book details