← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 183

Sashe 70

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Murmushi Umaymah tayi cikin jin daÉ—in ganin su, da wal-wala hatta Jalal fuskarshi a sake take.
Jamil ne ya kalleta lokacin data ƙara so kusa dasu, cikin murmushi yace.
"Umaymah mu sai yaushe za'a nuna mana Amaryar a gabatar mata damu, ta sanmu da kyau".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ai ku tun daren jiya nagabatar da sunayenku da matsayinku gareta".
Haroon ne ya ɗan kurɓi tea tare da cewa.
"Yo ai Ni dai ba sai an gabatar daniba, domin nasanta tun safiyar jiya kafinma a É—aura auren ko Jalal?".
Taɓe baki Jalal yayi tare da cewa.
"To ni mamaki nakeyi, ko dai dama ita tazone dan taga wanda za'a aura mata".
Umaymah ce ta É—an zauna kusa da Jafar tare da kallonsu kana tace.
"Babu sam ita kanta bata saniba bata zata ba bata tsammaci aurenta a jiyaba.
Sai dai arashi kukayi, Ni tun jiya da kuka gayamin nasan arashi ne kawai ya haɗaku a asibitin. Bata san komaiba akan auren nan hakama iyayenta, basu da zaɓine kawai dan sun san ƙa'idar gasar Shaɗi ne hakan yasa sukayi haƙuri."
Kai Jalal ya jinjina tare da cewa.
"Uhummm mu dai yanzu yan kallone. Dan na sani tabbas yanzu za'a fara buga Game É—in yanzu wasan zai soma".
Cikin yin ƙasa da murya Jamil yace.
"Sosai ma, dan kuwa akwai kitimurmurar da za'ayi a masarautar Joɗa, wannan Ustaz Sheykh Malam akarmakallahu Hamma Jabeer ɗin, salonshi na dabanne a dukkan lamuran yauda kullum wannan auren dai zamuga ya zai kasance!". Ya ƙarishe mgnar da yin ƙasa da murya sosai, yanayi kuma yana kallon hanyar falon Sheykh Jabeer.
Cikin haÉ—e fuska na wasa Umaymah tace.
"Al'khairi shine zai wanzu".
Murmushi Haroon yayi tare da cewa.
"Inafa al'khairi a wannan abun da bashi da tushe, ni kaina naji baƙin cikin wannan al'amari, auren Muhammad Jabeer ya zama kamar a munafuce a ɓoye babu wani shiri bare kimtsi kun bari an auro mishi mace kamar auren ƴar tsana".
Jafar kam abincinsa yakeci, ba tare da ya kulasuba.
Jamil kuwa sai murmushi yakeyi.
Jalal kuwa shiru yayi alamun nazari.

Ummi kuwa ware wasu kyawawan Foodflaks takeyi gefe.
Tare da abinci a cikinsu.

Bayan ta gamane ta ajiyesu gefe.
Tare da cewa Umaymah.
"Ga breakfast É—in Sheykh".
Kai Umaymah ta gyaÉ—a mata.

Nan sukaci gaba da hira.

A can Side É—in Mama kuwa,
Tunda batun auren Jabeer ya basu ya riski kunnuwan ahlin masarautar JoÉ—a,
kowa da abinda ke ransa.

Batool kuwa hankalin Mama in yayi dubu ya tashi, bisa irin kukan da Batool ketayi har cewa takeyi ta gane ai dama Mama bata son ya aureta.
Da kyar ta samu tasha kanta,

Gimbiya Saudatu kuwa, da Baba Nasiru da Baba Basiru da Laminu.
Zaman gaggawa suka tanada.

Suna tattauwana wannan baƙin lbrin da bai musu daɗi ba.

Zaune yake gaban wani ƙasurƙumin boka matsafi.
Cikin tsantsar tashin hankali da kiÉ—ima yace.
"Boka Tsitaka haka mukayi da kai? Yaushe ka fara min ƙarya kan aiyukan da nake baka? Ya za'ayi kwatsam rana tsaka ace wannan shegen yaron da nakeji tamkar in kasheshi yayi aure? Da kai mukayi mgna a nan tsawon shekaru kace min ka, kashe min wutsiyar ɗan iska mai jajayen kunnuwa, babushi ba mace har yaumal ta ƙunun nadi.
Ka bani tabbacin. Har gobe sihirin na bibiyarshi, kace min duk sanda zanen kan macijin ya isa kan tsaitin ƙahon zuciyarshi zai mutu kowama ya huta. Sai kuma jiya kamar sauƙan aradu ace yayi aure!".
Wata iriyar razanenniyar dariya mara daÉ—in amo boka Tsitaka ya kece da ita, wanda har saida tsaunuka da kwazazzaban dake wurin suka amsa amonta.
Dariyar mugunta yakeyi babu ƙaƙƙautawa, har saida baƙon nashi ya fara hatsala cikin tashin hankali yace.
"Wannan ai insakanci ne, in bazaka iyaba ina nemo wasu matsafan. Ya zan zo da matsalata da sanyin safiyar nan kai kuma ka kama min dariya, Ni mahaukacin gidanku ne?".
Cikin dariyar boka Tsitaka yace.
"To ai tashin hankali na banzane, kana kokonto kan aikin da shekaru goma sha biyu yana cinsa yana bin jikinshi. Kana zaton ya karye ne? To bari kaji wannan sihiri yana nan a jikinshi, har kwanan gobe wutsiyarsa bata harbawa, baya jin kanshi a namiji.
Ba kuma zaiji yadda maza kejiba har abadan.
Iya bincikena banga mai mgnin da zai gani aikin da mukayi mushiba.
Auren da akayi mishi, da ya sani tabbas da zai watsa abun. In kuwa kana zaton sihirin yana sauƙa kaje ka dubu, zanen bindin maciciyar da yake tun daga kan ƴar babbar ƴatsar ƙafarshi ta dama, zaka samu kan macijiyar ya ƙetare ƙugunshi.
Na kuma gaya maka duk sanda kan macijiyar ya isa kan ƙirjinshi, saman nononshi, zai mutu, kuma yadda zai bar duniya haka ƙannenshi da wanshi zasubar masarautar Joɗa har abada yadda ba'a tambayi yaushe matacce zai dawo duniyaba haka suma baza'a tambaya ba."
Cikin ɗan jin daɗi baƙon bokan yace.
"To ai dole hankalina ya tashi, kaida kace min bazai wuce shekaru biyar ba zai rasu gashi yanzu shekaru goma sha biyu bai mutuba".
Cikin zare ido boka Tsitaka yace.
"Kai ai mun ma yi dacen yin asirin da wurine, tun kafin ya gama girma da yanzune sam bazai kamashiba, mutumin da baya rabuwa da sunan Allah a bakinshi. Yaronda ko yaushe da al'wala yake zama, ai badan hakaba da tuni mun hallakashi".
Cikin ɗan samun nitsuwa baƙon ya direwa Boka Tsitaka kuɗi kana ya miƙa ya fice.

A can wurinsu Umaymah kuwa.
Suna cikin hira, Umaymah ta ɗan juyo a hankali ta kalli hanyar fitowa falon Sheykh Jabeer, sabida jin ƙamshin turaren shi.
Murmushi mai cike da jin daÉ—i tayi ganinsa cikin shiga ta al'farma, kamar yadda ya saba.
Wata jallabiya blue color ce mai taushi a jikinshi.
Sai al'kyabbar da ya ɗauka samanta shi kuma peach brawn mai ɗan karen kyau sai sheƙi yakeyi,
kana sai hira minshi shima Peach brown da É—igo-É—igon white.
Sai takalmansa sau ciki masu kyau, baƙaƙe kana sai ɗan abun saman hiramin shima baƙi.
Taku yakeyi cikin nitsuwa da haiba da kamala, fuskarshi cike da kwarjini da ƙasaita.
Hannunshi na riƙe da Tab ɗinshi.
Idonshi na kanta yana sarrafata da hannun damanshi yayinda hagunshi ke riƙe da ita.
Sai wani irin ƙamshi yake bazawa a duk inda ya wulga.
A hankali yake taku amman da alamun sauri yakeyi.
A tsakiyar falon ya tsaya, tare da kallon inda suke zaune.
Ganin Umaymah ta nufoshi ne yasashi gyara tsayuwarshi.
Tare da É—an kallon ta, kana yana mai amsa gaisuwar su. Jalal da Jamil.
Tana isowa inda yake ya É—an kalleta, cikin yanayin rauninshi dake baiyana in yana gabata, a hankali yace.
"Umaymah ina kwana".
Cikin kula tace.
"Lfy lau Alhamdulillah Jazlaan ya gajiya da jikin!".
A taƙaice yace.
"Alhamdulillah". Sai kuma ya É—an juya yayi taku uku zuwa biyar ya isa Dinning area, kana Umaymah na biye dashi.
Dafa kujerar da ya Jafar yake a kanshi yayi tare da sunkuyowa ya kalli fuskarshi da kyau, sai kuma ya É—an kalli Aunty Juwairiyya cikin kauda kanshi a kanta yace.
"Ya jikin nashi?". Cikin sanyi tace.
"Alhamdulillah jiki kam da sauƙi sosai, dan tunda ka dawo zaiyi baccinsa lfy ba tashin hankali in lokacin tashinsa yayi kuwa ba hargowa zai tashi yayi al'wala yayi ta nafilfilinshi".
Cikin yanayin jin daÉ—in zance yace.
"Alhamdulillah. In sha Allah komai zai dai-dai-ta domin babu cutar da bata da waraka sai dai ina ba'a gano mgninshi ba".
Hannunshi ya gyara da kyau yadda Jafar zaiji daɗin riƙon da yayi mishi.
Chapter 70 · 0% Book details