← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 183

Sashe 28

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Su Sule, Iro, Ado, Junaidu, Madu, Ari, Sani, Ibi, ja'eh, Ori, Binbi, dama sauran samari majiya karfi kuma kab sun cikin daji.

Haka suka kwana a can. Suna tafiya suna nema, kafin gari ya waye, wasu sun isa har jihar taraba, wasu Gombe, wasu har bauchi, wasu har cikin iware da mutun biyu na taraba,
Wasu sun nausa da nisa, sabida in dai tafiyace bata taɓa bawa bafulatani tsoroba domin anyi ittifaƙin duk ƙabilun duniya babu ƙabilar da takai ƙabilar fulani saurin tafiya da jumurin doguwar tafiyar ƙafaba, bayan laraban da.

Washe gari Litinin.
É—in, sauran dattawan garin suka sallaci Ya Lado, kana suka zauna amsar gaisuwa.
Suna kuma jin labarin inda yaransuke.
Ganin sunata wahalar tafiya ba lbrine yasa.
Bappa yace su dowo. Domin wanna abu addu'ace mgninshi.
Sannan kuma wannan karon bazasu saurari masarautar Numan ba , gangami zasuyi su kai kukansu, ga masarautar Joɗa, wanda a cikinta ne GARKUWAN FULANIN ƙasar Nigeria gaba ɗaya yake.
Da fari ArÉ—o Yabani bai gamsu da hakanba saida Bappa yayi mishi bayanin.
Dolefa suna da buƙatar hukama mai tsarki ta shiga tsakaninsu da ƙabilun Ɓachamawa nan, kana dole mgnar ta isa ga babbar masarautarsu, wacce za'a miƙa mgnar ga Ƙungiyar *TABITAL POOLAKU, DA KUMA ƘUNGIYAR.*
*MIYETTI ALLAHA*
Wannan dalilin ne yasa Ardo Yabani ya umarci gaba É—aya matasan da suka bazama neman su Gaini su juyo su dawo gida.
Haka kuwa akayi kafin yamma sai gasu duk sun daddawo domin.
Wasu da yawa motoci suka shigo.

Bayan sallan ishane suka zauna zaman mitin domin sun gama shirya komai gobe dai kai tsaye masarautar JoÉ—a zasu wuce.

Bayan sun gama tattauna yadda abun yake suka tsaida zance kan cewa dattawansune zasuje.
Daga nan Duk suka tashi taron kowa ya koma gidanshi da tarin al'hini a zuƙatansu.

A can cikin birnin Ɓadamaya kuwa cikin makarantar su Aysha.

Zaune take bisa salla hannunta riƙe da carbi tana ja.
Kana hannunta É—aya kuma rike da wayarta, wacce taketa kiran yayunta kab baya shiga tun jiya da yamma.
Cikin kula Rafi'a ta kalleta a hankali tace.
"Aysha ba komaifa, kinsan garin naku kunada matsalar Network, wasu lokutan kuma kinsan basu da cajine".
Kanta ta jingina da jikin gini, murya can ƙasa tace.
"Gaba ɗaya fa, woyoyinsu basa, shiga, na maƙotanmu kuma ko sun shiga basa ɗagawa, Rafi'a hankalina ya tashi."
Da sauri Rafi'a tace.
"No kada ki damu tunda kikaga basa É—agawa alamun kenan woyoyinsu na wurin cajine ko?".
Idonta ta lumshe tare da cewa.
"Zuciyata na yawan sinkewa Rafi'a, fargaba nakeji".
Cikin sanyi Rafi'a tace.
"Yauwa to ki kira Ba'ana mana".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh hakane fa".
Ta karishe mgnar tana dannawa wayarshi kira.
Bugu É—aya ana biyu ya É—aga,
Da sauri tace mishi.
"Ina wuni ya Ba'ana".
Ba'ana dake zaune tsakiyar ƙabilun Ɓachamawa suna mitin yadda zasu farma garin Rugar Bani da yaƙin sunƙuru gobe, murmushi yayi cikin sonta yace.
"Lfy lau Mata, ya karatu?".
Alhamdulillah tace tare da cewa.
"Ya Ba'ana ya garinmu ya lbrin gidanmu duk suna lfy?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Duk suna lfy garinmu duk anata kewarki É—azuma na wuce ya Ladonkin a kwance yanata shan baccinsa babu ruwanshi da damuwar duniya".
sam bata kawo komai a rantaba kan mgnarshi ta ƙarshe, saima sanyi da ta ɗanji daya bata tabbacin, suna lfy, sabida iya tsawon zamanta da Ba'ana bai taɓa yi mata ƙaryaba, koda zaiyiwa duk mutanen duniya ƙarya to ita baya mata ƙarya, kuma duk zafin gskyar mugun abunda yakeyi zai gaya mata. Abu biyu ya ɓoye mata a rayuwarshi sata da kisan da yakeyi, sai dai yana gaya mata in dai a kantane zai iya kashe kowa ma.
So cikin sanyi tace.
"To yasu Ya Gaini kuma".
Murmushin mugunta yayi tare da cewa.
"Shima na wuceshi wurin Binto sunata hirarsu har tanata raira masa waƙoƙin soyayya".
Murmushi ta É—anyi tare da cewa.
"To ka gaida min su bari in É—anyi wonka".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To Mata kiyi wonkanki anjima zan kiraki muyi hira".
To tace mishi kana ta katse kira, tare da cewa Rafi'a.
"Alhamdulillah duk lfyarsu lau ashe".
Itama Rafi'a murmushi tayi kana sukaci gaba da hirarsu sai dai still fa tsoro da fargaba da bugawar da zuciyar Aysha keyi bai bariba, ganin hakane yasa Rafi'a, kallonta kasancewar Rafi'a ƙwararriyar mai koyar da girgirkene, a zahiri cikin makarantar tasu, da kuma social media. Cikin kula da son samawa aminiyar tata nitsuwa tace.
"Yauwa GARKUWA, zomu shiga kitchin, muyi É—an alalan kwai, naga kin kawo mana koyaye da yawa."
Murmushi Aysha tayi wace, akefi kiranta da ƙarshen sunanta.
hannun ta miƙa Rafi'a, cikin sanyi tace.
"Help me my friend, jikina yayi sanyi da yawa, ji nake kamar bazan iya tashiba".
haka nan itama Rafi'a jikinta ya fara sanyi, sai dai sanin in ta baiyana kasalarta tashin hankali Aysha zaifi tsananta ne yasa ta dake, cikin sauri ta kamo hannunta ta jata-ta miƙa kana suka shiga kitchin ɗin.
Nan suka fara aikin sunayi tana É—an janta da hira.
a haka dai har suka gama, kana, ta shiga wonka.

Shi kuwa Ba'ana maida woyarshi yayi cikin al'jihunsa, kana ya kalli Sarkin mayaƙan ƙabilar ɓachama da yake ce mishi.
"Shege Ba'ana wato, yana bacci cikin kabarinsa babu ruwansa da damuwar duniya".
Dariyar mugunta sukayi dukansu,
wanda yake gefenshi ne ya kece da wata dariyar tare da cewa.
"Wai ita kuma Binto kukan natane waƙen SOYAYYA ko?".
Kanshi ya gyaÉ—a musu cikin muguwar fuskarshi.
Wannan matashin ɗaya fara sokawa Ya Lado wuƙane lokacin da suka kasheshi. yace.
"Ita kuma da yake sokuwace har ta yarda k...".

Wani irin tashi sukayi gaba ɗayansu sabida wani irin shaƙa da naushi da Ba'ana ya kai mishi, wanda a take ya fara kakarin mutuwa.
cikin zafin rai ya hankaɗa tarin mutanen dake son cotan yaron daya shaƙe ɗin amman ina sun kasa, wata zabgegiyar wuƙa ya lumtsumamishi a ciki wanda yasa sauran duk suka watse tura gawarshi yayi gaban su cikin ɗaga murya yace.
"Ina kashe wanda ya yabi Shatuma yace yana son Shatuma bare wanda ya zageta, duk wanda baya son ransa ya aibata min Shatu a gabana ya gani".
Cit kake jinsu sabida masifar tsoronshi sukeji.
Dan ya fisu taƙadiranci dan Ba'ana mugun babarbarene mai baƙar zuciya.

Haka dai aka tashi wannan taron da yake dama sun gama tattauna yadda zasuyi farmakin.

Washe gari ranar wata Tuesday 21 November 2017 itace ranar da har abada al'ummar Rugar Bani bazasu mance da itaba a tarihin rayuwarsu, itace ranar da duk motsin da numfarfashi Shatu zatayi sai ta tunashi ranace data girgiza, zukatan al'ummar musulmai, ranace da tasa duk wani bafulatani makiyayi jin ƙuna da tafasar zuciya.
Ranace da tada hankalin al'ummar ƙasarmu nan dama maƙotanmu.

Tunda safiyar ranar, dattawan garin suka gama shirinsu cikin shigarsu ta al'farma, Malam Liman (Bappa) ArÉ—o bani Jauronsu, Ahaji Horo da Ahaji Umaru, kana Malam Yero, da kuma Alhaji Sa'idu.
su rai takwas dai suka shirya cikin kamala da mutunci. Junaidu ne yake cikin Shikan ya samo musu mota kirar siyana wacce suka É—auki shatarta, domin zai kaisu har cikin fadar masarautar JoÉ—a kuma zai jirasu. Su dawo tare.

Nan suka shiga Mota gaba É—ayansu, suka tafi.
Chapter 28 · 0% Book details