← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 183

Sashe 19

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta saki kwaryar, a sorace, da sauri yasa tafin hannunshi, biyu ya tare kwaryar.
Cikin tsoro jiki na rawa ta zazzaro idanunta woje kana murya a hargitse tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, Ya Ba'ana mekabani? Me ka shayar dani? Na shiga uku me kasa nasha?".
Gaba É—aya ta gigice tana rawan jiki da murya, ga hawaye kuma tuni suke shatata.
Ganin yadda ta firgitane ya sashi matsowa gabanta cikin É—aga murya yace.
"Ba komai ba abinda na shayar dake Mata, wallahi Allah ki yarda dani wancan da kikasha babu komai a ciki".
Da sauri taja da baya tare da cewa.
"Ban yardaba me ka shayar dani?".
Sai kuma ta fara kakarin amai da ƙarfi, ganin kamar aman bazai zo bane yasa ta tura yatsunta biyu a baki, amman ina aman yaƙi zuwa sam.
Kawai sai tasa mishi kuka.
Cikin tashin hankali yace.
"Kiyi haƙuri Mata wlhi bazan taɓa shayar dake wani abu na guba, ko na ƙiba, duk abinda nasan bazaki shashi da sanenki ba bazan taɓa bakishi a ɓoyeba.
Ki yarda dani wlh ban shayar dake komaiba".
Ina taƙi ta saurareshi sabida tayi matuƙar firgita da tsananin razana da ganin abinda ke cikin kwaryar, cikin sauri yasha gabanta tare da cewa.
"Ki gani mana ki duba babu komai a ciki fa madarar shanunce".
Tsayuwa tayi tare da zubawa cikin kwaryar ido tas farin nonone kamar ko wanne nono da bashi da gamin komai".
Hannutasa ta mutstsuke idanunta tare da kuma sake kallon, cikin tuhuma ta maida idanunta kanshi tana mishi kallo mai cike da tuhuma.
A hankali ya sunkuya ya ajiye akwaryar kana ya taso ya fuskanceta da kyau fuska ya haÉ—e tare da cewa.
"Sam bakya min adalci Mata, na lura dake, wani mugun zato da zargina kikeyi.
A zatonki wai zan iya cutar da kene? Shin kin mance tun kina ƴar tatsitsiyarki nake sonki ne? Da inada mummunar niya a kanki da na cutar dake tun kina ƙarama.
Kullum idanunki na nuna min baki yarda dani ba. Me kike nufi?
ko dai wani kikeso ba niba?".
Ya ƙarshe tambayar da taune bakinshi kana ya tsareta da idanunshi, da sauri ta sunkuyar da kanta tare da cewa.
"A a ni kam babu wanda nakeso."
Kanshi ya É—an rausayar kana ya dawo ya zauna a bakin bukkar tashi, cikin kakkausar murya yace.
"Dawo ki zauna".
A hankali ta dawo gefen gaban bukkar ta zauna,
shi kuwa wani ɗan randar ƙasan dake gefenshi ya buɗe, cikin haɗe fuska ya ɗan kalleta tare da cewa.
"To zakiyi sabon Saurayi. Salmanun ArÉ—o Yabani, zai fara nemanki, kamar yadda munafukan tsoffin rugar nan suke tsarawa, dan ana son rabani dake".
Da sauri taketa jujjuya kai tare da cewa.
"A a Wallahi ni Yaya Salmanu, ba sona yakeba, ka sani tun ina ƙarama duk abinda ya shafi karatuna shike koya min har dai yasa aka sani.
Makaranta kai kuma baka hanaba".
Cikin haÉ—e fuska yace.
"Ehh ai nasan ke baki san yana sonkiba, amman na lura shi yana sonki, kuma zanci ubanshi da bulalin shaÉ—i bashi babu sake kallon duk wani abu da nakeso".
Cikin tarin tsoron kada a cutar da Yaya Salmanun tace.
"Wallahi ƙarya ake mishi, baice yana sona ba, shi yama tsaneni ne yanzu, dan Allah Ya Ba'ana kada ka yarda da ƙaryar mutane".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Uhum kinga nan cikin ranÉ—ar nan, to bulaline wanda nake shaÉ—i dasu, yanzu tsawon shekaru biyu kenan da aka hana shaÉ—i basu samu wanda suka dakaba, na tsumasu da tarin tsumi mai zafi, wanda muddin na zana jikin mutun dashi sai ya fashe,
Kuma gasu a ƙalla sun kai tamanin a cikin randar nan kuma a ƙa'ida da guda goma sha bibbiyu kawai zakayi shaɗi to kinga kenan zan iya shadi da mutun sama da shida dasu basu ƙareba".
Kanta taketa jujjuya mishi tare da cewa.
"Ya Ba'ana kada ka yarda da sharrin mutane kasanfa Yaya Salmanu shike karantar dani, tun ina ƙarama kuma ko yanzu dana girma tunda shi ya rigada ya gama digiri ɗinshi shike fahimtar dani duk abinda ya shige min duhu, kuma tunda nazo hutun nanma ban haɗu dashiba".
A hankali yace.
"Eh ai yau kam zaki haÉ—u dashi".
Yunƙura tayi ta tashi tare da cewa.
"Uhumm, shike nan ni bari in tafi gida an fara kiran salla."
Da sauri ya miƙe ya fito yabi bayanta tare da cemata.
"To Mata jirani inzo in rakaki Mana".
To kawai tace mishi, a haka suka jero suna tafiya yana gaya mata irin tsumin da yayiwa bulalin nashi.

Suna isa dai-dai garken su Shatu, ta É—an tsaya hango yayunta sun dawo daga kiwo,
cikin jin daÉ—i ta É—an juyo ta kalleshi tare da cewa.
"Bari inje wurinsu Ya GiÉ—i, in tayasu É—aure shanun".
Murmushi yayi kana yace.
"To Mata ki kulan min da kanki kada shanu ya taɓa min ke, dan akan ɗan mai shanun zan rama miki ba kan shanu ba".
To tace tare da juyawa ta nufi cikin tsakiyar taron dabobbi su da aƙalla zasu kai guda dubu da yan ɗaruruwa tsakanin shanu, tumaki, awaki, rakuma.
Da sassarfa take kutsa tsakiyar dabobbin tana cewa.
"Yaya sannunku da dawowa".
Da sauri GiÉ—i da Seyo suka juyo murmushi sukayi tare da cewa.
"Yauwa ƴar ƙanwarmu, daga ina kike?".
Da ido ta nuna musu Ba'ana dake tsaye can gefe ya zubawa dabbobin nasu idanu tamkar mai ƙidanya su.

Gaini ne da Lado suka zuba mishi ido domin gaba ɗaya ya shagala da kallon da yakeyi, har wani ƙan-ƙance idanu yakeyi.
Sam bayaji kiran da Babanshi Bukar ke auna mishi.
Har saida GiÉ—i yace.
"Heyy Ya ba'ana Ubanka na kiranka".
Ya ƙirishe mgnar da bagwariyar hausarsa.
Shi kuwa Ba'ana da sauri ya juya ya nufi wurin babanshin da yanzu ya dawo kiwo.

Cikin sakalci da gajiya GiÉ—i ya kalli yayunshi mazan tare da tura baki gaba yace.
"Wayyoooooooo Allah bayana zai karye, Ni dai na gaji bazan iya sunkuyon É—aure shanu ba, ga Shatu zata tayaku".
Sai ya kuma kalli yadda duk suka sunkuya sunata É—aure dabobbin suna É—an dariyar yadda itama Shatu ta dage tana tayasu.
Junainah ce wace dama duk lokacin dawowarsu zata kawo musu sassanyan kindirmo susha tun a nan kafin su koma gida.
Da saurinta take ratso cikin shanayen tana cewa.
"Ya GiÉ—i tareni, na gaji ga damunku".
Da sauri ya nufi inda take kwaryar ya amsa kana suka dawo gaban bukkokin da nanne ma kwancin masu gadin dabobbin suke.

Zama sukayi ludeyayen dumar dake kan fefeyin daya rufe kwaryar ya É—auke kana ya buÉ—e kwaryar, ludeyi É—aya ya sa musu a ciki.
Aysha dake kusa da sune ta zauna tare da cewa.
"Ya Giɗi kama ka bani". Kai ya gyaɗa mata kana ya cika ludeyin yasha sannan itama ta ɗebo rabin ludeyin tasha, kana ta bawa Junainah itama ta kamfato ta cika ludeyin ko rabinshi bata zuƙaba.
Ta miƙawa Ya Seyo dake tsaye gefensu, da murmushi a fuskarshi ya amsa ya sha, sauran nata,
Shatu ce ta gyara zamanta ta matso kusa da É—an uwanta tsokonta GiÉ—i abokin tsamarta, gyara zamanta tayi kana tace.
"Ya Seyo zauna ga fili."
To yace kana ya zauna suka fara sha,
Lado ne ya kallesu cikin gajiya yace.
"To wai mu aka kawowa ko kune?".
Shiru babu mai magana sai kamun ludeyin da sukeyi,
Gaini ne ya matso gefe shima ya zauna kusa da Junainah yasa hannu ya É—auki wani ludeyin, nan suka zauna suna sha, ganin hakane, Ya Lado yace.
"To ni naci girma".
Da sauri Shatu ta mike wurinda ta tashi ta nuna mishi tare da cewa.
"A a ya Lado zauna kusha ni na ƙoshi". Murmushi Bappa dake gefensu yayi, wanda yanzu ya iso da jarkan ruwa a hannunshi,
Cikin kallon so da tausayin yaran nashi yakeyi,
Cikin kula yace.
"Sannunku- sannunku da rana, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin suka amsa baki É—ayansu,
Sai kuma ya kalli Aysha da Junainah yace.
"Ayshatu maza kama hannun Junainah ku koma gida, kinji an fara kiran salla".

To tace tare da kamo hannun ƙanwar tata suka nufi gida.

Su kuwa Bappa da yaranshi da makiyayanshi anan sukayi al'wala, kana suka juya suka nufi cikin Rugar tasu dan zuwa masallaci.
Yayinda ko wanne garke an bar mutun É—aya sabida tsaro...

Bayan sallan isha sunci abinci sun ɗan taɓa hira, kaɗan kana Bappa ya tarasu yana karantar dasu kamar yadda ya saba duk dare, da kuma safiya kafin a tafi kiwo shiyasa sam ahlin wannan Rugar Bani ba jahilai bane.

Suna zaune, yaro yayi sallama, yace.
"Wai ana kiran Shatu a woje".
Ummey ce ta É—an juyo ta kalli yaron tare da cewa.
"Wake kiranta?".
"Wai yace ince mata inji Ya Salmanu ne".
Yaron ya faÉ—i.
Da sauri Ummey tace.
"A a Salmanu ne ya zobe? To maza kace ya iso mana ya zai tsaya a waje kamar baƙo".
To yaron yace kana ya juya ya fita.
Jim kaÉ—an sai gashi ya dawo gefen Ummey ya rusuna tare da cewa.
"Yace wai ince mata, ta fito woje".
"Da mamaki Ummey tace to gata nan zuwa".
Sai kuma Inna ta É—an kalli Shatu tace.
"Tashi kije ai mun gama aikin ma".
Ita kuwa Aysha dake zaune gaban Inna suna gasa tattabarun da aka yanka tunda yamma,
kwano ta É—auko a konÉ—onsu kana tasa gasassun tattabarun guda biyu.
Tasa yaji a gefe, ta rufe, kana ta gyara wuyan hijabinta sannan ta miƙowa Junainah kwanon.
A hankali ta ratsa gefen su Ya GiÉ—i ta wuce.

Ummey kuwa da ido ta rakasu tana fatan Allah yasa fata da shirin Bappa da ArÉ—o Yabani ya tabbata.
Chapter 19 · 0% Book details