← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 183

Sashe 25

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Isowar su ArÉ—o yasa aka basu hanya har suka iso gaba inda aka tanada musu, kujerun zama. Na bencin katako.
Daga nan manyan Dattawan duk suka Zazzauna.
Bisa ƙa'idar gasar Shaɗi wanda ya fara cewa yana son yarinya shi zai fara duka, in wanda yace yana sonta daga baya ya ƙetare bai zubda hawayeba baiyi kukaba, to sai asa kwanaki sai yaje yayi jinya ya worke daga zabgar da yasha, sai ya dawo ya ɗauki fansa, to in ya zana wannan yayi kuka shike nan yayi nasara in kuma wannan ma baiyi kukaba za'a sakeyi har sau uku to nan in babu wanda yayi kuka cikinsu sai yarinya ta zaɓi wanda takeso, don anada yaƙinin duk wanda ta zaɓa, zai iya kare kanshi tunda ƙarfinsu yazo ɗaya.

Bayan an gama dai-dai-ta komai, Salmanu ya cire rigarsa kamar yadda ƙa'idar gasar take, ya rage dagashi sai gajeren wondon.
Shi ma Ba'ana ya cire rigarshi ya zama dagashi sai gajeren modo, irin masu zuwa har guiwa É—innne.

To dole a ƙa'ida Ba'ana ne zai fara duka, amman da yake ya shiryawa abun sai yace, shi ya amince a fara dashi, kuma shima yau zai rama Ba sai an ware kwanakin zuwa jinya ba.

Nan kuwa take al'kalin gasa Barmuji yace an amince.
Daga nan aka zaro bulalin shaɗi na cikin tanɗun masarautar Arɗo Yabani wanda an ƙara tsumasu suma.

A hankali Barmuji ya miƙa wa Salmanu, bulalin,
kana ya É—aga hannunshi ya dawo dashi ta bayan Ba'ana.
Shi kuwa Ba'ana tsayuwa yayi ƙam tare da ɗan ware sawunshi,
Busar sarewar da mai busan yayine alamun a fara,
Ai kuwa cikin kuzari da jaruma Salmanu ya É—an ja da baya,
kana ya tattaro ƙarfin shi ga ba daya, ya ɗaga kitsetsten bulalan nan, ya taƙarƙara ya zabgawa Ba'ana shi a tsikar bayanshi,
Wanda a take taron matasan dake wurin suka kurma ihu mai karaji,
Yayinda shi kuwa Ba'ana, ƙim ya tsaya kamar ba shiba, domin ko idonshi bai ƙebtaba.
Sake taƙarƙarewa Salmanun yayi ya kuma zabga mishi bulalar a inda ya kima mishi na farin.
Still ihu, taron matasa sukasa, tarin ƙabilar ɓachama kuma dake wurin sai rurrufe idanunsu sukayi da ƙarfi sabida wai bazasu iya jurar ganin ana zabgar jakadan suba.
Mai irge kuwa da iya ƙarfinshi yake kware baki yana cewa.
"ÆŠaya! Biyu! Uku! HuÉ—u! Biyar! Shida! Bakwai!!!".
Haka yaketa irga duk bulalar da aka kaiwa Ba'ana amman wannan tagadirin mutumin ko a jikinshi kamar dutse ake zanawa ba shiba.

Ƙa'idar bulalin shaɗi Hamtsine akeyi.
Haka Salmanu yake ware iya ƙarfinsa yana zabgar Ba'ana, yana tsaye ƙiƙama. In wannan bulalan ya lauye, sai a bashi wani bulalan.
Har akaje arba'in da takwas ko gezau.
Gaba É—aya hankalin mutanen kirki ya gama tashi, domin sun sadakar da nasara ta kubcewa, Salmanu.
Shi kuwa Salmanu tattaro sauran ƙarfinshi kab yayi,
ya narka mishi bulala ta 49-50".
Amman shirunshi.
Ihun da kafuran ƙabilar ɓachama suka sakine ya tabbar an gama, nan take suka shigo filin da gudu ruggumeshi suketayi suna shafa bayanshi, da yayi shati-shati.

Shi kuwa Salmanu gaban ArÉ—o yaje ya zauna, nan aka basu ruwa sukasha gaba É—ayansu.
Hutun 30 minutes sukayi aka koma fagen fama.

Da ƙarfi mai busan sarewa ya busa alamun a fara,
wani irin kafurin murmushi Ba'ana yayi tare da gyara riƙon da yayiwa bulalar tashi.
Cikin tsananin mugunta ya É—an koma da baya, kana ya É—ago bubalar da masifan karfi ya zabgawa Salmanu ita a tsakiyar fatan bayanshi.

Wani irin gan tsarewa Salmanu yayi, sabida wani irin masifeffen azaba mai girgiza zuciya da yaki yana ratsa dukkan sasasan jikinshi.
Bai gama dawowa daga gigi da azabar bulalar forkoba, yaji ta biyu,
Rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi, gaba ɗaya inda bulalar ya taɓashe, harbin kunama yakeji yana ratsashi.
Wani irin numfarfashi yaka lokacin da aka zabga mishi bulala ta goma.

Gaba É—aya hankalin mutane ya tashi domin kowa yaganshi yasan yana jin azaba.
Bulala ta ashirin da biyar da akayi mishine ya sashi buÉ—e idanunshi da suka koma jajazir dan azaban da yakeji.
Su kuwa kafuran nan sai ihun farin ciki sukeyi.
Shi kuwa Barmuji zagayawa yayi gaban Salmanu wai yaga ko idonshi ya kawo ruwa,
babu ruwa kam sai azabar da yakeyi tamkar idanun zasu faɗo ƙasa, ci gaba da irgens yayi.
"Ashirin da uku! Ashirin da huÉ—u!!".
Wani irin tsalle Ba'ana ya buga da iya ƙarfinshi ya tsulawa Salmanu bulala ta ashirin da biyar.
Wani irin duhune ya rufe ganin Salmanu, saiga wasu zafafan hawayen azaba sun kwaranyo masa, ihu ya kuma zurma jin zafin bulalar ta isa kan mazantakanshi.

Gaba É—aya su Bappa dama matasan kowa rufe ido yayi sabisa dukan da akewa Salmanu dukane na son É—aukan rai.

Aysha kuwa tana gidansu kamar kullum tajiyo ihun Ya Salmanu kamar yadda kullum ihun wanda ake gasar dasu ke shaida mata sun faÉ—i.

Cikin kuka konta bisa cinyar Ummey tare da cewa.
"Shike nan Ummey zai kashe ya Salmanu".
Tuni itama Ummey da Inna hawayen suke zubdawa.

A can gidan ArÉ—o Yabani kuwa inna laure Maman Salmanu, kuka takeyi tamkar zata shiÉ—e domin yaranta mata sun zo sun gaya mata halin da yake ciki.

A can wurin gasar Shaɗi kuwa, ganin tuƙuru Ba'ana so yake ya kashe Salmanu ne yasa,
matasan Fulani sukayi kanshi dan dukanshi yake harda tattakashi kuma tuni ya wuce balali hamsin ɗin ƙa'idar gasar.

Koda matasan Fulani suka shiga dan crton ran Salmanu kawai sai ga ƙabilar ɓachamawan nan, sun fara zaro makamai sun rufa duk wani ba fulatani da duka da saran wuƙa.

Lokaci É—aya wurin ya hargitse gaba É—aya.
Aka kaure da faÉ—a saida.

Ganin wurin ya hargitse ne yasa,
Gaini yayi saurin kiran hukuma mafi kusa ya sanar musu.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka iso.
Hakane yasa duk ƙabilun Ɓachamawa suka gudu.
Allah ya takaita faÉ—an baiyi nisa ba, a take É—aya daga cikin police É—in wanda yake abokin Salmanu ne ya kwashesu suka tafi asibi.

Bayan garin ya lafa, kowa ya dawo haiyacinsa ne.
Isa ƙanin Salmanu ya tafi asibiti dan jinyar ɗan uwanshi kuma Alhamdulillah da yake ya samu taimakon gaggawa komai yazo da sauƙi.

Shi kuwa Ba'ana daga nan izayarsa ta ƙaru manufarsa shida ƙabilar ɓachamawa shine. Su tarwatsa al'ummar fulanin Rugar Bani baki ɗayansu.

Zuwa yanzu kuma ko ƙudane in dai na mijine to bazai sauƙa kan jikin Aysha ba,
sabida asirce, asircen da yakeyi da kuma tsoronshi da akeji.

Aysha kuwa ko zuwa dubo Salmanu ya hanata domin yace muddin taje a bakin ransa.

Yau kwana huÉ—u da faruwar abun, ya da faruwar abun kuma yau ta kasance jumma'a ne.

Kasan cewar jummace yasa gaba É—aya makiyayan suka taso kiwo da wuri, sabida son samun jam'in sallan jumma'a.

Iro É—aya daga cikin yaran Ahaji Horo, wanda yake yayan Binto da kuma Junaidu.
Kusan shine karshen dawowa kiwo.
ya taso ya taso tarin dabobbin sa a gaba kenan ya haɗu da gungun matasan Ɓachamawa, har sun wuceshi, sai kuma suka bishi a baya, cikin izaya babban cikinsu yace.
"Kai É—an fullo nan garin ubankane ko garin ubanmu?".
Cikin jarumtar jinin fulani yace.
"Gari dai da daji namune tunda iyaye da kakannimu sun saya, in kuma kuna maganar tushen nasabane, to Adanawa Yola dama kewayenta duk namune fulani".
Cikin mugunta É—aya daga cikinsu ya kai mishi mari da addan dake hannunshi".
Murmushi Isa yayi cikin hausar fulani yace.
"Kada ka sake dukana".
Kusan a tare suka haÉ—a bakin wajen cewa.
"In mun dakeka sai me?".
A kufule yace.
"Wallahi sai in rama, yawanku ba shine abin tsoro ba".
Ai kafinma ya rufe baki suka haushi da duka,
da sauri ya fara kare kanshi tare da kai musu duka,.
Kamar da wasa su rai shida sun gaza ji da É—an lenge-lengen saurayi matashi É—an Fulani.
Ganin kamar zaici galaba a kansune, yasa, ɗaya daga cikinsu ya dawo baya-baya ya zaro wukar dake ƙugunshi, da ƙarfi ya dawo kan Isa, ya luma mishi wuƙan a cikinsa wani irin ƙara isa ya sake, sai dai babu mai jinsa bare ya kawo masa agaji domin.
Dai-dai wannan lokacin duk wani musulmin wannan yankin yana masallacin jumma'a,
Da wannan damar suka samu suka kashe isa,
wanda suka daddatseshi da wuƙa.
Daga nan suka kira Ba'ana a waya, nan take ya kaÉ—a shanayen yace. "Yauwa aikinku yayi kyau, yanzu kuyi maza kuyi gaba da shanayen kasar Cameroon, zaku nufa birnin Yahunde kuna isa bakin boda yarana na kasar zasu amshi shanayen ku kuma sai ku dawo, kafin nan ma komai ya lafa baza'a zargekuba".
Haka kuwa sukayi, suka kaÉ—a kan shanu suka fasa daji, suka nufi hanya, shi kuma ya dawo cikin gari ya wuce É—akinsa bayan ya bawa uwarsa lbri.

Koda aka taso sallan jumma'a, anyi mmkin ganin isa bai dawoba, shiru-shiru dai har akayi sallan la'asar babushi, tofa daga nanne hankali ya ƙara tashi.
Cikin kiÉ—ima suka fara shiga daji a duba ko lfy bai dawoba.

Ai kuwa nan maza matasan Fulani suka watse cikin daji,
Bayan sun gama bulayin nemane babushi babu shanunshi, suna cikin zagayawan ne Sale yayi arba da gawar Isa dake malale cikin jini.
Nan suka É—auki gawa suka koma cikin gari dashin.

Wannan rana hankali Fulanin Rugar Bani yayi masifar tashi, gaba ɗaya ma sai ba'amaida hankali kam ɓatan shanunba,
Hankali ya tashi, É—auki É—ai-É—ai da akeyi musu ya fara hautsuna musu tunanin,
Gashi kisane da babu wanda za'a iya kamawa, koda aka sanarwa hukar cikin Numan sai suka korasu da case É—in, sabida a lokacin da suka zo shigar da report babu musulmi a police cikin officers É—in shiyasa suka korasu da batun.
Salmanu wanda shine ɗan bokon da kan iya jagorantan lamarinsu, yana gadon asibiti, bisa ƙarƙashin kulawar abokinshi badon hakaba da tuni Ba'ana ya kasheshi.

Koda fulani suka hatsala kamar kullum haka ArÉ—o Yabani ya tarasu ya taushi zuciyarsu, da kuma shawarar, su kai kukanmu ga sarkin Numan É—in, tunda ya hanasu samun damar ganin sarkin Nuruddeen Bubayero.

Koda sukaje masarautar Numan É—inma abin da akayi musu a police station, fiye dashi akayi musu.
Chapter 25 · 0% Book details