Sashe 154
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki take kallon Aysha dake kwance itama tana baccin.
Sauƙowa tayi ta tsaya kana ta gyara ɗaurin zaninta sannan, ta sunkuyo kan Aysha ta tasheta daga baccin.
Da sauri ta tashi zaune tana waige-waige.
"Tashi kije kiyi salla lokaci yayi".
Ummi ta faÉ—a tana shiga bathroom.
To tace tare da miƙewa ta nufi ɗakinta.
Bayan sun idar da salla ne, suka fito a tare.
Kitchen Suka nufa.
A nan suka samu Sara tana jajjaga kayan miya.
Ummi kuwa tukunyar data É—aura tun kafin taje tayi bacci ta buÉ—e, bul-bul haka yake bararraka a hankali sabida ta rage wutan sosai yadda ko zata kai magriba ruwan bazai kare ba.
Ƙara wutan tayi, tare dasa ludeye ta ɗan motsa ƴan ƙananan mulmulen tunkusa, wanda suketa bararraka da jan nama mai kyau da tantaƙwashi, sai ƙamshi yakeyi tuni saman ruwan ya cika da mai naman kab ya diddige ya marmashe.
Juyowa tayi ta kalli Aysha tare da cewa.
"Me zaki dafawa Sheykh?".
Matso tayi kusa da ita tare da cewa.
"Ba miyar kase za'ayi ba, ai yanaci".
Kai Ummi ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh yanaci kam, bare an kwana biyu ba'ayi ba.
Yanzu É—ebo nama mai É—an yawa ki haÉ—a kifi kizo.
Ki saka.
Ke kuma Sara gyara min ganyen yakuwar nan."
To sukace baki É—ayansu.
Sara ta fara gyara yakuwar.
Ita kuwa Aysha naman tukunyar dake gabanta ta buÉ—e wanda sulallen naman ke ciki.
Juyewa tayi cikin tukunyar miyar, kana ta juya ya shiga Store bandan kifi ta É—ebo manya masu kyau.
Ruwan É—umi ta zuba a ciki ta wonke ta gyarasu fes.
Kana tasa a cikin tukunyar.
Ummi kuwa tukunyar tuwo ta É—aura.
A masallacin Masarautar JoÉ—a kuwa, ana idar da sallan la'asar duk, aka fara fitowa.
Affan shi cikin gari ya wuce wurin aminansa Yusuf da Aryan.
Jalal kuwa amsa kiran uban gidansu ya tafi.
Jamil da Ya Jafar ne suka dawo gida.
Suma Side É—in su Jamil É—in suka wuce.
Ƴan tsirarun mutane ne suka rage a masallacin wanda Sheykh yana cikinsu.
Mafiya yawa karatun al'ƙur'ani mai girma sukeyi.
Wasu kuma tasbihi sukeyi wasu kuma a kwance suke suna sauraron sautin murya.
Sheykh dake Karatun Alqur'ani cikin sassanyan murya.
Biyar dai-dai Sheykh ya fito cikin masallacin da sauran mutane.
Sabida wani irin duhu da ya fara yiwa illahirin garin Æadamaya Æ™awanya.
Bisa alamu wani babban hadarine ke ketowa tun daga ƙasa.
Dimmmmmmm haka garin yayi, koda tsuntsaye baka ganin suna shawagi.
Gaba É—aya kowa hanyar gidansa ya nufa.
Cikin nitsuwa bakinshi É—auke da tasbihi yake tafiya.
A LamiÉ—o da Galadima suna gabanshi.
A haka ya isa farfajiyar Side É—insa.
Ya kai hannu zai tura ƙofar kenan yaga an buɗe.
Gefe ya É—an koma yana jiran mai fitowa.
Sara ce ta fito riƙe da kuloli a hannunta da alamun sun gama girki kenan.
Da sauri ta wuce saboda ganin hadarin.
Batama lura dashi ba.
A nitse ya shiga falon da sallama a bakinshi.
Ummi ce ta amsa tare da juyowa ta kalleshi.
Windows ya fara rurrufewa yana gyara labulayen.
"Hadari ne a garin namu ko?".
Ummi ta tambaya tana kallonshi.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Mai ƙarfi ma kuwa Ummi, ku rurrufe windows ɗin falon can da ɗakunan ku.
"To". Ummi tace tare da miƙewa ta nufi falon.
Gefen Aysha ya É—an ratsa ya nufi kitchen.
Zagayawa baya yayi, ya dudduba ko ina kana ya dawo.
A inda ya barta a nan ya sameta.
Tana ta danna waya.
"Nace kije ki rufe windows É—inki ko".
ÆŠan juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"A rufe suke".
Kanshi ya gyaÉ—a kana ya wuce ya barta a wurin.
Lib-lib haka gari ya ƙara ɗibkewa da duhu.
In dai wuri babu hasken ƙwan wuta to ko tafin hannunka bazaka gani ba.
Da sauri ta nufi É—akin Ummi.
A zaune ta samu Ummi tana gyara carbinta daya tsinke.
Gefe ta zauna ta fara tayata.
Shi ko Sheykh Windows É—insa ya rurrufe,
tare da kashe komai na wuta dake falonshi da Dinning area,
hasken wayarshi ya kunna kana ya wuce bedroom.
Wutan ya É—an kunna guda É—aya hasken yayi dai-dai misali.
Umaymah ya kira bayan sun gama mgna ya katse kiran.
Sai ya zauna bakin gadonshi tare da jawo system É—insa.
Gaba É—aya hankalinsa ya meda kanta, shiyasa baima san lokacin ya tafi ba.
Shida dai-dai, hadarin ya gama haɗa gangaminsa tako ina gabas da yamma kudu da arewa da tsakiyar sararin samaniya yayi baƙiƙƙirin
Sai wani irin walƙiya mai masifar haske da akeyi tako wani sashin.
Wani walƙiyane da a haska yazo tare da wani razanenne tsawa mai firgitarwa ne yasa Aysha wani irin zabura ta takure kanta cikin cinyoyinta tare da cewa.
Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Itama Ummi abinda ta maimaita kenan sabida ta razana matuƙa.
Sheykh kuwa hannunshi yasa ya rufe system É—insa tare da cewa.
"Subhanallazee yusabbihu ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min khifateeh".
Ya maimaita sau uku. Wani irin kumshe idonsa yayi lokacin aka kece da ruwa tamkar da bakin kwarya.
"Allahumma saiyiban nafi'an".
Ya kuma fara mai-maita wa.
Aysha kuwa da sauran matsorata irinta ajiyan zuciya ta sauƙe, tare da cewa.
"Kai ya Allah kasa mucika da imani, wlh Ummi ina tsoron walƙiya da tsawa a rayuwata, ina son yanayin damuna amman ina tsoronshi".
Jingina kai da jikin gado Ummi tayi tare da cewa.
"Tsawa abin tsorone Æ´ar nan. Nima kaina naji tsoron".
Kai ta gyaÉ—a jinjina tare da cewa.
"Tab Ummi kema kina tsoro".
Sosai ma kuwa tace. Dariya suka sa.
Ruwane fa ake tsulawa da iya ƙarfin shi.
Miƙewa Sheykh yayi tare da kallon time a wayarshi.
Shida har ta wuce.
Gab ake da kiran sallan magriba.
Gashi kuwa ruwa aketa fesawa babu kama hannun yaro.
Tsaki ya É—an ja tare da cewa.
"Da ban dawo bama sai nayi salla a masallaci".
Bathroom ya wuce. Al'wala yayi kana ya fito.
Turare ya fesa, a jikinshi kamar yadda yakeyi koda yaushe.
Falonshi ya fito, dai-dai lokacin aka kuma danna wata tsawar da ta kece da ruwa mai ƙarfi.
"Ya ilahi". Yace lokacin da ya fito babban falon, shiru ba kowa sai hasken wuta.
Sanyin dake ratsa jikinshi ne yake sashi cikin wata fitinar kuma.
Baka iya jin sautin komai sai na ruwan shuuuhhhh.
Ƙofar falon ya nufa, a hankali ya buɗe.
Jingina kanshi yayi da jikin ƙofar yana kallon ikon rabbil samawati.
Ruwane tako ina yake kwaranya.
Ƙasa tasha ruwa ta ƙoshi.
Tabbas in matsoraci zai gani zaiyi zaton ƙasar ma tsastsafo da ruwa takeyi.
Magadanan ruwan duk sun cika tambul.
Dole ya maida ƙofar ya rufe, sabida.
Ruwan yayi yawanda in ya shiga kafin ya isa masallacin zai iya cutar dashi Allah ya sani baya son yayi salla shi É—aya ba cikin jam'iba, gashi su Jalal ma yau duk basa nan É—in.
A nitse ya juyo.
Falon Aysha ya nufa.
Shiru ba kowa sai TV'n da suka bari a kunne.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli ƙofar ɗakinta,
TV'n ya kashe sannan ya nufi É—akin.
Da sallama a bakinshi ya shiga,
tsayuwa yayi a tsakiyar É—akin, ganin ba kowa.
juyowa ya É—an yi kana, ya fito falon,
ƙofar ɗakin Ummi ya nufa,
a bakin ƙofar ya ɗan tsaya tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Da sauri Ummi tace.
"Wa laikassalam, Sheykh ka shigo".
Kanshi ya É—an shafa tare da yin jim kaÉ—an kana yace.
"Umm Aish tana nanne?".
Da sauri Ummi tace.
"Eh gata nan muna tare".
Ta ƙare mgnar tana nunawa Aysha hanyar fita alamun taje.
Shi kuwa Sheykh É—an juyawa yayi tare da cewa.
"Ummi magriba ta kusafa".
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
"To Sheykh".
"Aish". Ya kira sunan a mutunce.
A hankali tace.
"Na'am".
"Kizo".
Yace yana mai juyawa.
Miƙewa tayi ta fito.
Da É—an sanÉ—a ta isa gefenshi tare da cewa.
"Gani".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta sama da ƙasa kana yace.
"Je kiyi al'wala kizo É—akina muyi salla, bazan samu zuwa Masallaci ba".
Cike da gamsuwa da mgnar sa ta É—an karya wuya tare da cewa.
"To amman zanyi wonka kafin nan".
Kanshi ya gyaÉ—a mata tare da cewa.
"To Kiyi sauri kada lokacin yayi baki fitoba".
To tace kana ta nufi É—aukinta.
Shima ya wuce ya nufi Side É—insa.
Kai tsaye bedroom ya wuce.
Babban sallayarshi ya shimfiÉ—a musu a tsakiyar É—akin kana ya zauna a wurin, tare da lumshe idonsa ya fara bita.
Ita kuwa Aysha Kai tsaye bathroom ta wuce.
Ruwa mai É—an zafi sosai ta haÉ—a, bayan tayi Brosh wonka ta farayi mai rai da lfy.
Sosai ta cuccuɗa jikinta lungu da saƙo kamar ko wani lokaci tana gama wonkan tayi al'wala kana ta fito.
Tana fitowa ta wuce gaban dreesing mirror, gashin kanta ta taje ta gyarashi ta tubkeshi a ƙeyanta sabida saurin da takeyi bata tsaya kitse jelarba.
body lotion mai ɗan karen ƙamshi ta shafa a jikinta, kana ta shafa humranta mai sassanyan ƙamshi.
Kasan cewar yanayin Weather'n garin ya sauya ko ina yayi sanyi iska mai sanyi nata busawa tana kaÉ—awa da sassayan ruwane yasa.
Ta saka dogon wondon blue jeans sai kuma tasa wani Baby top fari wanda ya lafe a jikinta yayi mata cib-cib kana ta ɗaura wani pink jacket wuyanshi da tattausan suma fari, sai dai jacket ɗin ba irin ƙattin nan bane ƴar cafalce dai-dai da jikinta kuma ya tare mata sanyin.
Gaban dreesing mirror ta koma wasu turaruka masu ƙamshi guda biyu ta fesa.
Kana ta zato wani ƙaton hijabinta Black blue mai ɗan karen kyau da sheƙi, ta zurashi har ƙasa ko idon sawunta bazaka iya ganiba.
Sallayarta ta É—auka kana ta fito da É—an sauri ta nufi Side É—insa.
Ganin baya falone yasa ta wuce bedroom da sallama a bakinta.
"Wa laikissalam".
Ya amsa mata lokacin da ta turo ƙofar ta shigo.
A gogon hannunshi ya kalla tare da cewa.
"Iso muyi lokacin na tafiya."
To tace tare da ƙarasowa tsakiyar ɗakin.
Sallayan dake hannunta ya kalla tare da taɓe fuska kana yace.
"Duk sallayan dake É—akin nan bazasu isheki bane sai kinzo da naki?".
Girgiza kai tayi alamun a a.
Hannunshi yasa ya amshi sallayar, kana ya juya ya fuskanci gabas.
Ita kuma ta É—an matso gefenshi ta tsaya daga bayanshi kaÉ—an. Ganin ta kimtsa ta nitsu yasashi tada kabbara.