← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 183

Sashe 34

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Bappa kuwa da Arɗo Bani, Alhaji Haro. Malam Manu, Alhaji Umaru, tashin hankali da kiɗima da firgici da ɓacin ransu ya tsananta, sabida ganin.
Duk Hukumar ma sun tafi,
Gashi babu wani babba da yazo ya duba halin da suke ciki, sabida ai su basu san da cewar su Waziri sun zo tun jiyan ba.
Ransu yayi matuƙar ɓaci, ganin Gwamnatin jihar,
da Masarautar jihar, babu wanda ya tako ƙafarsa, yazo ya dubasu ko ya turo wakilinshi.
Wato matsalarsu bata shafi kowaba.
Wannan abun shine mafarin Fara da baƙar Kaddarar Shatu a tarihin rayuwar ta, domin iyaye da yayun wannan Rugar sun tunzura sun hasala, iya hasala, sun cika fam da tarin baƙin cikin rayuwa, an rigada an taɓo zuciyar Fulani haka yasa zasu iya gayawa kowa mgna dai-dai da abinda yayi musu.

A can Saudia kuma, komai na dawowarsu Sheykh ya kammala, cikin kwana uku, domin hankalinshi yayi matuƙar tashi, jin irin kisan gillar da akeyiwa makiyaya, wanda Maimartaba ne, ya gaya mishi komai, ya ƙara da cewa.
Yayi maza ya dawofa, don yana jiranshi suje tare yaje ya danni fulanin ya basu hakuri ya kuma taushesu kada su É—auki mataki da sunan ramuwa ko É—aukar fansa.

Hakane yasa, Sheykh ya uzzurawa Haroon dole ya gama musu komai.
A kwanaki ukun.
Ranar Jumma'a da azahar jirginsu ya sauƙa, a birnin Shehu Sokoto.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi yaso. Jikan nashi ya kwana, sai dai ina ya tike dole a lokacin Haroon ya kuma saɓan mota suka fara kita hanyan kawoshi Adamawa.
Wanda sai ƙarfe uku da rabi suka isa.
Kasamcewar dama basu taso da wuriba.
Kasancewar isar dare sukayi babu wanda yasan Sheykh ya dawo.
Ƙasar sai Lamiɗo da kuma hadimanshi, uku kacal da sune suka tarbesu.

Sai washe gari da. Asuba, sautin muryarsa yana karatun limancin Sallah asuba ne ya shaidawa mutanen masarautar JoÉ—a dawowanshi.

Gaba É—aya kowa ya cika da mamakin, kana da farin cikin dawowanshi.

Duk da kasancewar sa, mai larurar da wasu ke mishi kollo ko kiranshi majanuni, yasan kiyaye lokacin salla dama yinta cikin kushu'i.
Wannan shine ya hanashi sallame sallar, da akeyi yana cikin sahu na tara,
wanda jin muryar ɗan uwanshi ƙaninshi, ya sashi zubda hawaye masu ɗumi.
Ya Jafar kenan.
Jalal kuwa dake gefenshi wata irin sassanyan ajiyan zuciya ya sauƙe tare da lumshe kekyawan ƙwayar idanunsa da suke iri ɗaya dana Sheykh, ga kuma bacci daya cikasu, domin daren jiya, Ya Jafar ɗinsu ya hanashi bacci.
Jin muryar ɗan uwansu da shi kaɗai ke iya sarrafa babban yayan nasune ya sashi sauƙe, numfashin.
Jamil da Affan kuwa, wani irin yalwataccen murmushi ya sake jin muryar É—an uwansun.

Abbansu kuwa, shi dai har yau yana rasa me yakeji a kan ƴaƴan nashi, Especially Sheykh, yana jin zuciyarshi na mishi nauyi duk sanda yaron baya kusa dashi, sai dai kuma in yana kusa dashi sai yaji tamkar bai taɓa wani farin cikiba a rayuwarsa.
Ya sani tabbas su abun tausayawa ne, suna buƙatar kulawarshi fiye data kowa a duniya, to amman ya rasa meyasa yake jin kamar baya son kusancisa dasu.

Maimartaba kuwa, suna cikin sahun na forko bayan liman,
Sai da sauran malaman fada.

A cikin gida kuwa, jin sautin zazzaƙar miryarshi yana rere karatun al'ƙur'ani, ya ida fatiha, kana ya ɗaura, Arrahama,
daga bisani ya rufe da lakadja'akum, kafin ya tafi zuwa ruku'uh.

Haka nan Juwairiyya ta tsinci kanta da zubda wasu zafafan hawaye, masu ƙuna a rai, tabbas ta sani.
Kasan cewar Sheykh a masarautar nanne kaÉ—ai yasa, suke a ciki.
Ta sani in badon daraja da al'farmarsa ba, da tun tuni, an tabbatar da sunan mijinta mahaukaci.
Hannu tasa ta share hawayenta cikin sanyi ta miƙe dan gabatar da sallan asuba, a zahiri tace.
"Allah ne gatanmu, kaine GARKUWAR mu, Sheykh in baka nan gidan kanyi mana duhu, ƙasar tanayi mana zafi."
Daga nan ta tada kabbara.

Ummi Jakadiyarsu kuwa,
Tana bayan gida, tana al'wala ta jiyo muryarshi, wani irin murmushi tayi tare da yin mgna a baiyane.
"Dan Halak kaƙi ambato, ɗa ɗaya tamkar dubu, maƙiyanka fadawanka, sunyi sake ɗan zaki ya girma, in sha Allah zaka dawo da farin cikin masarautarnan, sunyi sake, sun bar kari tun ran tubani,
Muhammad Jabeer bawan Allah".

Haka ta fito tana wasu irin kalamai masu wuyar fahimta.
A can sashin Hajia Mama kuwa,
Wata kekyawar budurwa, ce.
Konce kan gado gefen Mama, datake zaune bisa sallaya.
jiyo muryashine ya sasu saurin juyowa, suka kalli juna,
Cikin tsananin farin ciki da tarin shauƙi budurwar ta diro daga kan gadon gaban Mama ta zauna cikin zaƙuwa tace.
"Lah Mama, yaushe ya dawo! Muryar Sheykh Jabeer nake jifa! Mama ko dai dama yana nanne?".
Wani irin kallo Mama tayi mata cikin sanyi da murmushi a fuskarta tace.
"Batul shine, ya dawo!."
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe cikin tarin shauƙi tace.
"Yes Mama, farin cikina ya dawo, kamar yasan, nazo.
Alhamdulillah, Mama Allah yana sona, ki gani ina zuwa, na samu baya nan, naji baƙin ciki kamar in mutu jiya kafin inyi bacci, sai gashi Allah ya turo minshi cikin dare ɗaya."
Murmushi Mama tayi, tana mai jin mmkin yadda Batul ke masifar son Sheykh har take gaza ɓoyewa.
cikin haÉ—e fuska tace.
"To yanzu dai, sai ki tashi kiyi salla, tunda kinji muryar da kikafi so a duniya, kin sauƙo kan gadon, sau nawa ina tadake, sai kiyi miƙa ki kuma konciya".
Cikin jin dadi tace,
"Wayyo Mama baccinne bai isheniba Allah ko jiya kwana nai ina zulumi, sai 3:44 na asuba na samu bacci."
Murmushi Mama tayi kana ta miƙe ta kabbarta sallan.
Ita kuwa Batul, miƙewa tayi da sauri ta shige, bathroom tana cewa.
"Bari inyi wonka inyi salla, in shiga kitchin yau nida kaina zan mishi breakfast."
Tana faÉ—in haka ta shige ciki.

A masallaci kuwa, ana idar da salla kamar koda yaushe, da yawa basu fitaba saida sunata lazumi.
Yayinda Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero da kuma Sarki Nuruddeen Bubayero, da Habibullah Nuruddeen Bubayero, suka jero, suka fito a jere, domin su kullum ana idar da sallan asuba, suke fitowa su koma cikin masarautar, inda kowa zai wuce Side É—insa,
Yayi karatun qur'ani da kuma, Dua Azkar, inda har sai rana ta fito, kana suke É—an maida bacci, to kuma sudayin breakfast sai 11.
Suna isowa tsakiyar masallaci, Sheykh yaji an ruggumeshi ta baya, yasan mutun É—aya ne rak zai mishi haka a cikin masallacin,
Ya Jafar É—insu.
Yana juyowa kuwa yaga shiÉ—in ne.
Ruggumeshi yayi gam-gam Jalal, kuwa ido ya zuba musu,
shi kuwa Sheykh hannu yasa shima ya ruggume É—an uwan nashi.
Yayinda ya zubawa Jalal kwayar idanunshi, ya rame sosai, hancinsa ya ƙara fitowa, sai sajenshi daya ƙara yin lib, da uban gashin daya tara, yayi wani kafurin aski.
Ramar da Jalal yayi ta daki zuciyarsa sosai baya son ganin ƙannen nashi cikin halin matsala,
a hankali ya janye kwayar idanunshi ya maidasu kan Jamil da Affan dake gefen damanshi,
Calikan ƙanenneshi kenan ba,
sheƙiyancinsu ɗaya, baki suka haɗa wurin cewa.
"Sabahul Noor Al'Sheykh".
A hankali ya ɗan motsa laɓɓansa, yana mai kallonsu yace.
"Sabahul khair ya Uktih".
murmushi sukayi, suna mai jin son É—an uwan nasu,
Abbs da Maimartaba kuwa, kai suka É—an jinjina kana sukayi gaba,
Ganin hakane suma suka bisu, a baya,
shi kuwa Sheykh hannu yasa ya shafa kan Imran da yanzu ya iso gabanshi cikin sanyi yace.
"Hamma Jabeer barka da safiya".
jin yana shafa kanshine ya sashi lumshe ido, inama ace yadda Hammanshi ke nuna mishi so haka zai shirya da Mom É—in shi, yana masifar son É—an uwanshi baya jin daÉ—in yadda yake ganin wata iriyar mu'amala tsakanin Mom da yayunshi.

Ganin Sheykh yaja hannun Ya Jafar sun tafine yasashi bin bayansu.

Ƙofar dake cikin masallacin wacce zata ɓulla cikin masarautarsu sukabi.

Suna shiga, kowa yayi sashinsa sabida sun sani ko sunbi Sheykh yanzu ba lokacin mgna bane, karatu zaije yayi.
Shi kuwa Sheykh yana riƙe da hannun Ya Jafar ɗinsa suka shiga side ɗinsa,
inda ya samu hadimai masu tsaron ƙofar, suna tsaye.

Suna shiga, tamtsetsen falon nashi kai tsaye ya nufi wannan babbar kusurwar da zata sadashi da.
Big part É—in shi,
Suna shiga suka ɓulla cikin wani mashahurin, falo, wanda yaketa tashin ƙamshi mai masifar sanyi da daɗin shaƙa,
a hankali ya zauna bisa kujerar 3 str kana yaja hannun Ya Jafar É—in suka zauna, tare.
A hankali ya juyo kanshi ya zuwa É—an uwanshi idonu,
Karatu yakeyi kamar koda yaushe, yanayi cikin tsantsar lugga da tajwid, kana ga kushu'i,
Suratul yaseen yake karanta,
bisa alamu kenan ya kusa yayi sauƙa, domin step by step yake bin surorin, in yayi sauƙa sai ya sako daga sama, baya mancewa, kuma baya birkitashi,
Wannan rahamar da Allah yayi mishi, duk da anso a maidashi majanuni, sai Allah yayi mishi muwafaƙa da littafinsa maisarki, yazama sihirin yayi mishi tasiri tako ina, amman banda gefen addininshi.

Wasu irin hawa masu ƙunu yaji suna tsatstsafo mishi, cikin jijiyoyin kekyawan idanunshi,
sabida ganin yadda Ya Jafar É—inshi ke karatu yana, kuka ya za'ayi ya sama mushi farin ciki a rayuwarsa ta ina, zai san me ke cin zuciyar É—an uwan nashi.
Jin yadda ransa ke ƙuna da tafasa ne, yasashi. Komawa ya jingina bayanshi da jikin kujer, kamar yadda Jafar yake mahaddacin haka shima settin kab tana kanshi,
Ido ya lumshe tare da yin bisimilla kana ya fara karu inda ya ɗauko daga forkon suratul. Noor ya farayin ƙasa.

Saida sukayi awa É—aya cur kana,
Suka fara Azkar, wanda sai da sukayi 23 minutes suna, jero addu'o'in cikin harshen dake nuni da cikekkiyar jimla ta larabci da lugga.
Koda suka shafa, sai ya ɗan kalli ɗan uwanshi dake riƙe da hannunshi gam.
Ya lura Ya Jafar na tsoron kada ya kuma tafiya ya barshine, yasan duk sanda yayi doguwar tafiya ya dawo, haka yake liƙe mishi.
Hannunshi yasa, ya share mishi hawayenshi kana,
ya miƙa tare da jawo hannunshi,
yasani yanzu lokacin yin baccinsa ne,
Side É—insu, ya nufa dashi, ta wata Æ´ar siririyar hanyar dake tsakanin sashukansu.
Chapter 34 · 0% Book details