← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 183

Sashe 180

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanshi ya É—an juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor'n da zai sadashi da falonshi. "Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen.."
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
"Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba".
Da sauri tace.
"Zan fice ba sai ka koreni ba."
Ta ƙarashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaɗa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
"To wai É—aga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sarƙar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta ɓace ɓat ko in ce ta yi ɓatan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ƙirƙiro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts..."
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buÉ—esu a hankali yace.
"Dakata, tsaya kiji."
Da sauri tace.
"Uhum ina jinka".
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
"Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahaluƙiya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar Joɗa, duk da kyautar ta yi kaɗan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ƙwarai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ƙarfin tukuicin da masararutar Joɗa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan".

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙe ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaÉ—an ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya É—an juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya É—an lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daÉ—i.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta É—an jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta É—aga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daÉ—i Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin É—iyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daÉ—i sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji Æ´ata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na Æ´aÆ´an Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daÉ—in da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daÉ—i tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.

Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar surƙullen da zai bayyanar mata, ko meye ma'anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al'amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sauƙin Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar ta tashi daƙyar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom É—in ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al'wala ta É—auro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata zafin rabuwa da budurci.
Sallaya ta shimfiÉ—a kana itama ta tada kabbara.

Bayan ta idar da sallah ne,
ta kuma miƙewa a hankali ta fito falo, sabida ta gaji da baccin kwanciya tayi bisa kujera da wayarta a hannunta, tana mgna da Junaidu.

Ummi kuwa tana kitchen.

Murmushi ta É—anyi jin Junaidun na cewa.
"Dan Allah Adda Shatu kicewa su Bappa su dawo haka nan, zamansu a waccar ƙasar ya isa.
Ina kewar Junainah, Rugar Bani gaba É—aya muna kewarsu dan Allah su dawo".
Gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"To Junaidu in sha Allah zan gaya musu, su dawo maka da masoyiyarka dan nima nayi kewar Junnu ina kewar Ummey na".

Ummu dake kitchin ne ta É—an tsagaita daga motsa naman da take fasawa Aysha
Sabida jiyo sallamar Hajiya Mama da Aunty Zuwairiyya.
Haka yasa ta fito tai musu barka da zuwa kana suka gaisa tare.
Sannan tace su isa Aysha na ciki.

To Juwairiyya tace kana tai gaba Hajia Mama na biye da ita a baya.

Ita kuma Ummi ta koma Kitchen dan kawo musu ruwa.

Ba a jima ba sosai Ummi ta debo drinks ta fito da nufin kai musu.
Sai kuma sukayi kiciɓis a bakin ƙofar falon Ayshan. Sun fito falon Shatu fuskarsu a murtuke, da alamun ransu a ɓace, suka wuce ta.
A hankali ta bisu da ido, tare da tambayarsu.
"Har kun fito ko ruwa baku shaba".
Dukansu babu wacce ta kulata suka fice.
Ajiyan zuciya ta ja ciki da mamaki, sai kuma ta juya ta nufi falon Ayshan.
Tana gab da shiga falon ta ji sautin muryar Aysha na faɗa da ɗan ɗaga murya take cewa. "Mitssssss munafukan banza masu fuska biyu mugaye masu baƙaƙen zuciya. In sha Allah sai Allah ya toni asirinku!".
Da sauri Ummi ta ƙaraso gareta tare da ajiye tray'n hannnunta bisa stoll cikin kula tace.
"Lafiya dai Shatu Meya faru?".
Girgiza kai Shatun ta yi cikin jin haushi ta ce
"Ummi nace bana son su, bana son ganin sun shiga rayuwata, bana son su rinƙa zuwa inda nake saboda na tsani mu'amala da mai fuska biyu."
Ajiyar zuciya Ummi ta yi tana jujjuya zancen Shatun, da kuma tsananin mamakin takun sakar dake tsakanin Aysha da Hajiya Mama.
Numfashin ta É—an fesar tare da dafa kafaÉ—arta kana a hankali tace.
"Shike nan ki yi hakuri yanzu ai sun fita."
Ƙwafa Aysha ta yi tare da kishingiɗa sosai tana mamakin yanda mutanen gidan suka kasa fahimtar komai tana matuƙar mmkin in ance wai Hajia Mama itace Mamansu Sheykh kuma ita har yau bata yardaba bata kuma jin zata yarda har gaban abadan.

Bayan ta idar da sallar isha har yanzun jikinta ba kwari haka tana jin ciwo a gabanta musamman in ta miƙe tana tattakawa, miƙewa ta yi a ciccije, "Wash Allah na!".
Ta faɗa haɗe da miƙewar ta fara tafiya tana gwale-gwale kamar ƴar kaciya, kallonta Ummi ta yi tana nazarinta, bayan ta shige ɗaki ta tashi ta bita ɗakin.

A tsaye ta sameta gaban drower'nta.
Juyowa tayi ta kalli Ummin dake matsowa kusa da ita tare da cewa.
"Aysha kin sake shiga ruwan É—umi kuwa?".
Kai ta jujjuya mata a hankali tace.
"ÆŠazu da yamma dai na shiga".
Kai Ummi ta jinjina kana tace.
"Yauwa to kije yanzuma ki shiga ruwan ɗumi zakiji sauƙin abin sosai."
Ya mutsa fuska ta yi irin na mai jin ba daÉ—i kana cikin sanyi tsce.
"Ummi bana jin daÉ—i kwata-kwata."
Kusa da ita ta matso cikkn kula tace.
"Na sani, amma shiga ruwan É—umin zai tai maka kwarai wajen jin daÉ—inki, don zaki sake sosai, duk wannan ciwo-ciwon zaki daina ji." Kwafe fuska ta yi kamar zata yi kuka.
Yanayinta Ummi ta kalla, ta so yin dariya sai dai kuma danne tare da cewa.
"Yi haƙuri kin ji Ayshs, daure kada ki zama raguwa mana."
"Uhmm".
kawai tace ta miƙe ta shige cikin bathroom.
Chapter 180 · 0% Book details