Sashe 105
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Ummi ta matso kusa da ita cikin sanyi da kuma yin ƙasa da murya tace.
"Shatu ni kuma in tambayeki wani abu mana".
Kanta ta jujjuya a hankali ta buÉ—e baki tace.
"Na sani! Ummi nasan abinda zaki tambayeni! Zakimin tambaya ne kan menene yasa da na shiga É—akin Yah Sheykh na suma na fita haiyacina, ko?".
Ta ƙarishe mgnar wasu hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata a fuskarta.
Cikin sanyin jiki ganin Ummi ta gyaÉ—a mata kai alamar eh.
Jamil ma jiki a mace ya zuba mata ido.
Tafin hannunta tasa ta sharce hawayenta murya na rawa alamun tana son danne kukanta tace.
"Ummi É—akin Yan Sheykh É—akine mai cike da hatsara a rayuwarshi.
Tabbas dan Allah yayi shi mutun ne mai ibada da imani da kekyawar zuciya, da yawan ambaton sunan Allah da zama da al'wala wlh da badan wannan nagartar da Addu'o'in da suka zame mishi abokan rayuwa suka zame mishi GARKUWA ba, kamar yadda Manzon Allah yace.
"Addu'a'u saiful muminin da tuni sun kasheshi sun sabauta rayuwarshi.
Ummi ban san komai ba kan masarautar JoÉ—a.
Amman dan al'farma Annabi da darajar Umaymah.
Zan taimaki Yah Sheykh iyakar iyawata.
Zan taimake shi akan abinda Allah ya bani ikon gani".
A hankali Jamil ya zamo ya zauna a ƙasa.
Yana mai jin tsikar jikinshi na tashi.
Itama Ummi zamowa tayi ta zauna ƙasa.
Hakama Shatu a hankali ta zauna gaban Ummi hannunta tasa.
Ta kamo hannun Ummi cikin muryar kuka tace.
"Ummi ku yarda dani, ku bani haÉ—in kai, zan tone duk abun cutarwa dake É—akin Yah Sheykh. Bazan cutar dashi ba, zan taimake shi kamar yadda Bappa na yake bani umarni duk sanda mukayi mgn dashi.
Ummi keda Jamil ina buƙatar taimakon ku.
Amman kafin nan ki gayawa Umaymah in ta amince,
sai inyi aikin amman kada a gayawa Yah Sheykh dan bazai yarda ba."
Cikin tsoro ido cike da hawaye Ummi tace.
"To Shatu me zancewa Umaymah, me kika gani a É—akin har ya firgitaki yasaki suma?".
Cikin kuka tace.
"Ummi kada ku tsaya bincike a kaina.
Ni dai ku yarda dani bazan cutar da kowaba na cikin Masarautar JoÉ—a sai wanda ya cutar da kanshi Ummi bamu da sauran lokaci mai tsawo fa, komai zai iya faruwa da Yah Sheykh".
Cikin tsoro da firgici Jamil yace.
"Ba matsala mun yarda dake, ni yanzu taimakon me zan miki?".
Cikin sauri ta share hawayenta tare da juyowa ta kalli shi kana tace.
"Yauwa Jamilu zaka samo mana mai saka tayis, yazo da katon É—aya na tayis É—in irin na bedroom É—in Yah Sheykh sak da sak.
Sai kuma kayi ƙoƙarin mu samu ya Sheykh in ya fita ya wuni sai dare zai dawo".
Cikin sauri yace.
"Tayis da mai sawa ba matsala, batun in ya fita sai dare ya dawo kuma inaga.
Sai zuwa jibi ranar ne zaije asibitin gwamnatin Genaral Hospital.
To in yaje can wuni yakeyi wani lokacin sai dare zai dawo".
Cikin gamsuwa da hakan tace.
"To ba matsala.
Ummi ke kuma ki kira mana Umaymah ki sanar mata, muyi abun da saninta."
To Ummi tace kana a wurin ta kira Umaymah tayi mata bayani.
Ba wani neman ba'asi tace.
"A barta Ummin Jabeer na amince, tayi duk abinda ya dace a kan mijinta da yayanshi da ƙannenshi dama duk wani abu nashi".
Cikin jin daÉ—i ta jinjina kai lokacin da take jin mgnar Umaymah.
Wani irin dogon numfashi taja mai ƙarfi sai gata ta tafi luuuh kan...!
Wasa farin girki? Shatu kadafa allura ta tono garma.
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta ɗan ja tayi sama da bakin ƙafan wonɗon wanda yake na robane bakin a tsuke yake.
Da sauri cikin tsoro da rawan jiki ta saki robar.
Pat ya fetti a jikinshi.
Ganin ya motsa.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani sassanyan numfashi ya ja mai tsawo tare da fesoshi a hankali kana, ya mirgina a hankali ya juya ya kifu cikin kasalan nauyin bacci ya É—aura kanshi bisa cinyarta,
Kana ya ware hannayenshi da sukayi É—an tsami sabida pillow'n da yayi dasu.
Ware hannayen yayi tare da miƙarar dasu.
Ya zama tana tsakiyar hannunshi kana kanshi na kan cinyoyinta.
Haɗe hannuyen nashi yayi ya sarƙafe yatsunshi wuri ɗaya, ya zama ya zagayeta tako ina yayi mata ƙawanya.
Ya cusa hancinsa cikin mayafinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinta dana kayanta.
A hankali ya kuma gyara kwanciyarshi da kyau kana yaci gaba da sauƙe sassauƙan numfashin.
Ita kuwa Shatu wani masifeffen tsalle da bugu zuciyarta keyi tamkar zaiyi tsalle ya fito woje.
Gaba É—aya ida nunta kan sumar kanshi ta zubasu.
Tare da kallon tattausan sajenshi dake kwance lib-lib a gefen fuskarshi.
Wani sassanyan numfashi ta sauƙe tare da lumshe idonta cikin zuciyarta tace.
"Allah shi ƙara".
Sai kuma tayi sauri ta buÉ—e idonta tana tambayar kanta.
"Allah shi ƙara me ɗin? Ya ƙara ruggumata ko meyeye".
Cikin kauda zancen a ranta ta ɗan muskuta dan janye jikinta. Amman sai ta ji ya riƙeta gam-gam, yana ƙara cusa kanshi cikin jikinta yana mai shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren jikinta.
Cikin tsoro murya na rawa a hankali tace.
"Yah Sheykh!".
Karab sautin muryarta ya ratsa kunnuwanshi.
Sai dai ko motsi baiyi ba,
A hankali ta kuma ce.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh!!".
Shiru babu amsa sai numfashin da yake fiddawa a hankali yana kuma shaƙan ƙamshin jikinta.
Cikin sanyi ta ɗan ɗago hannunta a hankali tasa taffin tattausan hannunta, ta ɗan rinƙa buge gefen fuskarshi a hankali a hankali tanayi tana cewa.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh! ! Tashi wai Affan dasu Yusuf sunzo, shine Affan yace inzo in tasheka".
A hankali ya buÉ—e idonshi,
Yanayin yadda take É—an marin gefen fuskarshi da hannunta wanda ke É—aure da agogo.
A hankali ya ɗago hannunshi ya ɗan kan hannunta ya kamoshi ya riƙe, cikin tsoro ta fara kiciniyar kwace hannunta,
Sai kuma tayi zuru, jin ya ja hannun da ɗan ƙarfi ya kawoshi dai-dai saitin fuskarshi.
Idonshi ya zubawa yatsun hannunta da kullum in ya gansu da jan lalle yake tuna mishi baya.
Da sauri tace.
"Wash Allah na".
Jin ya murÉ—a hannun ya juyo da fuskar agogon inda zai gani.
Ƙarfe biyu da miti arba'in da ɗaya.
Du-du baccin 40 minutes yayi tazo ta tasheshi.
"Harda zuba min maruka".
Ya faÉ—a a ransa.
Ita kuwa kan tattausan suman ta ajiye sinsiyar hannunta.
tana jin kanta na sara Especially in ta kalli saitin ƙasan gadonshi."
A hankali ya sake hannunta kana ya yunƙura ya juya rigingine,
ya fuskanci sama, ita kuma tana zaune tana kallon ƙasa hakanne yasa suna fuskantar juna, cikin wani irin yanayi ya zuba mata ido na wasu sakanni.
Shigarta tayi masifar mishi kyau. Kodan tasa kalan kayan da yafi sone.
Cikin muryar bacci yace.
"Shine harda dukana? Meyasa ne ku mutanen garincan kuke son dukan mutun da kallon jikinsa?".
Cikin tura baki tace.
"Cinyana, nagaji kanka nauyi".
Bai janye idonshi a kantaba ya yunƙura ya tashi zaune tare da juyowa ya fuskanceta.
tanƙwashe sawunshi yayi tare da cewa.
"Me zaki kalla a jikina? Woto Kin zama kamar ɓarauniya ko? Me kike son gani? Wani abu kike sone?".
Cikin tura baki tace.
"Nifa tada kai a bacci kawai nayi".
Hannunshi yasa ya riƙo hannunta, yatsunta ya zubawa ido, cikin wata murya mai sanyi yace.
"Masha Allah, kinyi kyau."
Wani irin sanyi taji kalmar tashi tasa mata a ranta, ido ta É—an É—ago ta kalleshi.
Shima ita yake kallo, ido ya lumshe jin sautin zazzaƙar muryarta a hankali tace.
"Nagode".
Tonƙoshe kansa yayi bisa kafaɗa kana hankali ya sake hannun nata.
Fuskarta ya kalla tare da taɓe baki yace.
"Waya koya miki irin sa lalle Mammeyyyyy nah!? Dan tafi ko wacce mace iya lalle".
Cikin sanyi da nazartar yadda ya kira sunan Mammeyyyyy da yadda lokacin ɗaya idonshi suka fara sheƙin tsastsafo da zafafan hawayen da ba zubowa zasuyiba.
Cikin son gano meke cikin zuciyarsa tace.
"Ummeyy nah ce ta koya min tun ina ƙaramar".
Yatsunta ya jujjuya kana ya miƙe tsaye.
A hankali ya juya ya nufi bathroom sabida baya son ta hango wutar ƙunar dake ransa.
Ita kuma binshi da ido tayi,
tare da langoɓar da kanta tana kallon sharabansa da gargasa yayi musu ƙawanya.
A haka ta shiga wani nazarin tana mai maimaita sunan da taji ya kira da cikekken so shaƙuwa ƙauna tausayi rauni shogoba *Mammeyyyyy.* Ta maimaita sunan a fili.
Shi kuwa Sheykh Jabeer al'wala yayi kana ya fito.
Yayi mamakin ganinta a zaune bata fita ba.
Hararanta yayi ganin yadda taketa kallonshi. Jallabiyar shi ya zura, kana yasa al'kyabbar, tare da sa Hiraminshi.
Sannan ya fesa turare.
Duk inda yayi tana binshi da ido.
Wayarshi da yafi yawan riƙewa ya ɗauka ya zura a al'jihunsa.
Sannan ya nufi bakin ƙofa inda takalminshi suke yana cewa.
"Wannan kallon maitan fa".
Da sauri ta janye idonta.
Cikin daƙilewa yace.
"Kada ki cinyeni da ido fa. Bana son kallo, ko kina bina bashine?."
a hankali ta miƙe tare da lumshe ido ta biyu bayanshi.
Tana gyara mayafinta tare da cewa.
"Ni ban kalleka ba".
"Uhummm." yace a taƙaice.
Kusan a tare suka fito.
Yana gaba tana bayanshi,
Suka fito tsakiyar falonshi.
Tsayawa ya ɗanyi ya gyara masaƙalin Al'kyabbar tashi.
Shiyasa ya zama a jere suke tafiya tana gefen damanshi.
A haka suka fito cikin corridor'n.
Suka doshi Falon cikin kwarjini da dacewa da juna sai ƙamshi da sheƙi zallan kyau sukeyi.
Da Sallama a bakinshi suka kutsa kai cikin falon.
Wani irin dariyar jin daÉ—i Affan da suke can Dinning area yayi, suna cin abinci da Ummi ta matsa suci.
Wani irin murmushi Yusuf da Aryan ma sukayi tare da miƙewa suka nufi inda uban gidan nasu ke tsaye da kekyawar tauraruwarshi mai haskawa.
Affan kuwa wayarshi ya zaro yana kekkebta musu hoto tare da cewa.
"Ga amarya, ga ango, suna carabki da zallan kyau da ƙamshi".
Murmushi sukayi dukansu, ita kuwa Shatu tana tsaye gefenshi.