← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 183

Sashe 74

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin bada umarni Abba ya nuna mishi Aysha tare da cewa.
"Kama hannunta kuje, ka gabatar da ita, ka fara daga sashin ƙannen Lamiɗo, sai na Mamanku, daga nan kuje wurin Gimbiya Saudatu,
dama sauran matansu Babanku Nasiru".
Bisa dole yace.
"To kana ya yunƙa ya miƙa,
da sauri Umaymah ta miƙe tazo ta miƙar da Aysha.
kana ta kamo hannunta ta miƙa mishi alamun ya riƙe hannunta.
Cikin tsuke fuskarsa da kwaɓeta tamkar zai ɗaura hannunshi a ka ya kurma ihu.
Ya zuba mata ido. Muryar Abbanshi ce ta katse tsayuwar da yayi kamar an dashi.
"Riƙe hannunta ku je". A hankali ya ware tafin hannunshi da Umaymah ta kamo
kana lokacin guda yaji zuciyarshi tana tsalle da harbawa, kamar dai tana mararin wani abu.
Hannun Aysha Umaymah tasa mishi cikin nashi tare da meda yatsunshi ta rumtsesu.
Dam-daradam-dam haka zuciyarshi tayi wani masifeffen bugun mai kama da na aradu kana tafara wani irin tsalle.
Ita kuwa Aysha, wani irin tsuma jikinta ya fara lokacin da taji tattausan yatsun hannunshi da fatar tafin hannunshi ya rumtse nata.
Hannun wani irin masifeffen tsoro da kunyane suka diro mata, a lokaci guda.
Shi kuwa Sheykh wani irin asirtace kuma ɓoyeyyen dogon ajiyan zuciya ya sauƙe mai sanyi, jin gaba ɗaya zuciyarshi ta koma ta nitsu tabar wannan tsinkewar da bugawar da tsalle tayi lib a cikin ƙirjinsa.
Jin muryar Jakadiya ne yasa, Sheykh Jabeer, yin ƙarfin halin ɗaga ƙafarshi ta dama.
Jin ya ɗan yi gabane yasa itama, ta ɗaga ƙafarta ta hagu, sai hakan ya bada wata dama ta musamman, ya zama suna ɗaga ƙafafuwan su, a tare kana suna taku a jere.
Sai dai shi É—in ya É—an kereta kaÉ—an.

"Masha Allah. Tabarakallah,". Sune kalaman da Umaymah ke Maimaitawa, lokacin da take biye dasu a baya.

LamiÉ—o da kanshi da Galadima sunga wani irin dacewa na musamman a tsakin Muhammad Jabeer da Aysha.
Abba kuwa murmushi yakeyi mai baiyana jin daÉ—i.
Malam kuwa, Addu'o'in yaketa jero musu na fatan al'khairi da zaman lafiya da nitsuwa da samun zuriya É—ayyiba.

A hankali suke taku yayinda kowa zuciyarshi ke bin takun sawunsa,
A haka suka fito babban falon Gimbiya Aminatu nan suka samu Ummi. Tana ganinsu ta miƙe da tsauri tayi gabansu, hadimai hudu cikin na Gimbiya Aminatu kuwa, sukayi bayan Umaymah dake bayansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer suna fitowa yayi wani irin saurin sake hannunta tare da janye nashi,
Sabida shi ji yake tsikar jikinsa na tashi tamkar ya riƙe wutan lantarki ne sabida masifar tsuma da yaki naman jikinsa nayi.
Murmushi Umaymah tayi ganin still dai suna tafiya a jere a jere suna wani irin taku mai ƙayatarwa.

Suna fitowa, suka samu sallama a bakin mashigar wurin.
Nan ya shaida musu, duk sashukan gidajen anje anyi sallama dasu an kuma basu daman shiga.

Tafiya kaÉ—an sukayi daga sashin Gimbiya Aminatu, ta gefen hagunshi,
suka ɓullo farfajiyar wani babban part,
Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu.
A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya.
Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru.
Cikin murmushin da muryar tsufa tace.
"Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa."
A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita.
wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima.
Cikin kula yace.
"Barka da safiya Innano". Cike da kula tace.
"Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko".
Kanshi ya gyaÉ—a mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta.
"Cikin muryar tsufa tace.
"Allah ya sanya al'khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya É—ayyiba."
Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki É—ayansu.
Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta É—an kalli tsohuwar tare da cewa.
"Ina kwana".
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace.
"Lafiya lau, ya baƙu ta?".
A hankali tace.
"Alhamdulillah". Jakadiyarsu ce ta É—an rusuna tare da cewa.
"Mun barki lfy".
Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi.
Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta.

Kana suka miƙe suka fita.

Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga.
Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne.
Saida suka gama da sashukan manyan masarautar.
Kana suka nufi sashin Hajia Mama.
Tuni tasan da zuwansu.
haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata.
A matsayinta na uwar ango.
Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya.
Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi,
Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiÉ—ar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara'a tace.
"Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy".
To shifa suna É—aure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.

Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.

Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
"Amarya ki É—ago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike".
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
"Ina kwana Mama".
Cikin kula tace.
"Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta".
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
"Gashi É—iyata amshi kisha."
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
"Alhamdulillah".
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
"A a É—iyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar JoÉ—a, dole in marabceki dashi."
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
"A a Shatu amshi kisha kinji ko?".
Cike da mamaki ta É—an kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Bana shan madarar".
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
"Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi".
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
"Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne".
Cikin rawan murya tace.
"Bana sha".
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
"To gashi kai kam kasha naka".
Zamanshi ya É—an gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
"Kawo hannunki ko É—iyata".
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya É—ago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta É—an kaikaice, ta buge c...!

Ƙaƙa tsara ƙaƙa

By
*GARKUWAR FULANI*Ta bugi kofin madarar, ba zato ba tsammani, Jabeer yaji kofin ya tsumbce mishi.
ya faÉ—i gefenshi.
Tass ya fashe madarar ta kwaranye a ƙasa.
Cikin sauri da tsuƙe fuskarshi ya juyo ya kalleta.
Itama É—in shi take kallo.
Ido cikin ido sukayi da ita a karo na forko a rayuwarsa duk da yasan sun taɓa haɗuwa.
Kallon kwaÉ—ayye mai irin bakin Junainah, tayi mishi.
Sai kuma ta janye ƙwayar idanunta cikin nashi da sauri.
Sabida wani irin kallon da taga yanayi manata.

Umaymah da Ummi kuwa, kallon junansu sukayi, cikin yanayin son gane ya akayi kofin ya faÉ—i dan basuga sanda ta ta É—an buge mishi hannunta.

Hajia Mama kuwa cikin tashin hankali da kiÉ—ima ta kalli Umaymah tare da cewa.
"Akwai matsala, ita batasha, shi nashi ya kwaɓe."
Sai kuma ta maida dubanta ga Shatu cikin alamun damuwa tace kawo hannunki na dama."
Still maida hannun nata tayi baya, ba tare da tace komaiba.
Ummi ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
"Miƙa mata hannunki ku gaisa".
Murya can ƙasa tace.
"Yana ciwo". Ta ƙarishe mgnar da jin haushin kanta da ƙaryar da suka satayi.

Batool ce ta kalleta sama da ƙasa kana cikin gyatsine tace.
"Umaymah ai wannan ba irin matar Sheykh bac."
Sai kuma ta haÉ—iye ragowar mgnar dan ganin wani irin kallon daya watsa mata na alamun.
Ki kama kanki da kiran sunana a bakinki.

Wani dogon ajiyan zuciya Hajia Mama ta sauƙe cikin fargaba tace.
"Tashi Kuje ku gaida sauran. Allah yayi muku al'barka ya baku zaman lafiya.
In sha Allah babu komai".
Kamar jira Shatu takeyi a basu izinin tashi tayi fit ta miƙe.
Chapter 74 · 0% Book details