← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 183

Sashe 118

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun kuma yau yayi biyun na jiya.
Idanunta sun kaÉ—a sunyi jazir.
tana zaune kan kujera Umaymah na tsaye gefenta gudun kadda ta arce.
Ta É—aura hannun a kai tana kuka iya kuka, kukan azaba haÉ—e da salati.
A haka Sheykh ya shigo ya samesu.
Cikin takaici Umaymah ta juya ta nufi falon Ayshan tana kallonshi tana cewa.
"Gata ka barta kada ka kula da jinyarta da haƙƙinta ne Allah ya rataya a kan wuyanka ai ka fini sani.
Ka sani kana take sani".
Ta ƙarishe mgnar tana zubda hawaye sabida duk wanda yaji kukan da Aysha keyi yasan na wahala ne.

Ita kuwa Aysha da sauri ta miƙe ta kife kanta jikin gini tana mai ci gaba da kuka.
Jamil, Jalal, Affan, sunata yi mata sannu.

A hankali yabi bayan Umaymah da kallo tabbas ranta yayi matuƙar ɓaci, ga tashin hankali ga rashin bacci.

A hankali ya isa inda take.
Hannunshi yasa ya kamo nata. Da sauri ta É—ago jajayen idanunta ta kalleshi, cikin zubda zafafan hawaye tare da cewa.
"Yah Sheykh zafi, hannuna zai tsinke."
Wani irin masifeffen rauni da tausayinta ne yaji sun rufeshi, kanshi ya juya cikin sanyi, yaja hannuntan.
Suka nufi É—akishi.
Ita dai binshi a baya takeyi tana tafiya kamar a sama takejin kanta.
Kai tsaye har bedroom ya wuce da ita.
Kan gadonshi ya ajiyeta yanajin kukanta na hawa kanshi.

Bakin gadon ya zauna ya bata baya tare da cewa.
"Ki kwanta kiyi addu'a zakiji sauƙi."

Ba jinshi takeyi ba bare ta gane abinda yake nufi.
Da sauri ta yunƙura zata sauƙa.
Juyowa yayi ya kamata ya ajiyeta kusa dashi kana ya juyo suna fuskantar juna.

Cikin kuka ta faÉ—a jikinshi tana cewa.
"Umaymah hannu zai tsinke.
Zafi zai kasheni".
A hankali ya ruggumeta tare dasa hannunshi ya kamo hannun dake ciwon.
Da sauri tayi tsalle zata zille hakan ne yasa ya ƙara ruggumeta gama ya haɗa jikinsu wuri ɗaya.
cikin sanyi ya fara mata karatu a kunne yana hura mata iskar bakinshi kan hannun

Ajiyan zuciya mai ƙarfi da numfarfashi ta fara sauƙewa da ƙarfi-ƙarfi.

Umaymah kuwa jin shirune yasa, ta nufo Side É—insa.
Ganin baya falone.
Tace.
"To ina suke ina ya kaita?".
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom.

Tana tura ƙofar sai kuma tayi sauri taja da baya sabida hangosu da tayi yana konce lib yayi rigingine ya ɗan jingina da allon kan gadon.
Kana ita kuma ya kontar da ita kan jikinshi, ya ɗaura kanta bisa ƙirjinshi hannunshi na kan...!

Jinyar Sheykh ta musamman ce. To ya zata kaya ne in É—an gidan ba'ana yazo. Hege Sarkin baka wa yakewa aikin.

By

*GARKUWAR FULANI*
Cikin tsuke fuskarsa da muryar dake nuna zafin abinda ke zuciyarshi yace.
"Ummi in ya fito kiyi mishi jagora zuwa wurin sarkin ƙofa ki nunashi kada a sake barin yazo ko kusa da katangar masarautar Joɗa ne, a korashi ya bar jihar Ɓadamaya."

Da sauri Ummi tace. "Toh".
Kana tayi gaba tare da cewa.
"Mu tafi".
Da sauri Barun yabi bayanta.

A can falon Sheykh kuwa komawa yayi ya zauna gaban Bappa cikin sanyi yace.
"Bappa kayi haƙuri, ka gafarceni, bisa korarshi da nayi.
Wannan sunada manufar data kawoshi, ni zan ji da ciwon hannunta, in sha Allah zata samu lfy. Ka kwantar da hankalinka."

Ido Aysha ta zuba mishi cike da mamakin ta ina ta yaya ya gane meke tafe da Barun har ya gane sunada wata manufa, ta yaya ya gano kuramen bakin da Barun ya karanta mata, ta yaya yayi musu wasali har ya basu cikekkiyar jimla ya karancesu da fassararsu, meya sani a kanta.

Hakama Bappan kallon Mamaki yakeyi mishi amman sai ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Ba komai Muhammad Allah ya bamu sa'a ya kuma bata lfy".

Amin Amin yace shida Umaymah.

Al'amin ne ya É—an gyara zama tare da cewa.
"To Allah yasa a dace. Amman ko za'a gwada asibiti ne?."
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Kada ka damu, in sha Allah ba damuwa".
Kai ya É—an gyaÉ—a cikin gamsuwa.
A hankali Umaymah ta miƙe ta fita.

Shi kuwa Sheykh Aysha ya kalla tare da cewa.
"Tashi ki barsu suci abinci mana".
Da sauri Bappa da Al'amin sukayi mgna kusan a tare sukace.
"Alhamdulillah mun ƙoshi".
Kanshi ya É—an juyo ya kalli Al'ameen da kyau kana a hankali yace.
"Ba'a zuwa masarautar JoÉ—a a fita ba'aci komaiba".
Murmushi mai cike da gamsuwa Bappa yayi kana yace.
"Eh Alhamdulillah munci a wurin LamiÉ—o ai".
Kanshi ya gyaÉ—a cikin gamsuwa da hakan yace.
"Toh Bappa".
Cikin sanyi ita kuma Aysha tace.
"Ya Al'amin bani zanci".
Murmushi Al'amin yayi kana ya jawo Foodflaks É—in,
a plate ya zuba mata Couscous da biyar hanta.
gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau itama gyara zamanta tayi.
Bappa kuwa Murmushi yayi yana kallonsu.

Shi kuwa Sheykh ido ya zuba musu zaiga dai iya gudun ruwansu duk da zuciyarshi ta gama gano mishi nasabarsu.

Shi kuwa Al'ameen. A hankali yasa spoon ya É—an É—ibo, kana ya nufi bakinta da spoon É—in tare da cewa.
"Ha, buÉ—e bakin".

To tace kana ta buÉ—e bakin ya saka mata.
lumshe idonta tayi tare da tauna abincin dan ya mata daÉ—i.
Sake dibowa yayi ya bata, still ta buÉ—e baki yasa mata.

Cire kanshi yayi a kansu, ya maida dubanshi kan Bappa dake mishi mgna.
Umaymah da Ummi ne suka shigo a tare ita Ummi cewa.
Sheykh tayi an fidda Barun.

Ita kuwa Umaymah ƙwaryar fura da nono ta kawo musu.

Murmushi sukayi ganin yadda Aysha ta zage tana cin abinci.
Shi kuwa Al'amin ya dage yana bata.
"Ya Al'amin zan sha ruwa".
Tace mishi tana taunar sokar naman da yasa mata a baki.
Kanshi ya É—an juyo ya kalli Umaymah tare da cewa.
"Allah rene a sammin ruwa in bata".

To Umaymah tace ta miƙo mishi ruwa.
Tana kallon kamanninshi da Aysha ba sai an gaya maka cewar É—an uwanta jininta bane.
Bata ruwan yayi har baki.
Tasha sosai.
Kana ya kalleta tare da cewa.
"In ƙara miki abincin ne?".
Kai ta gyaÉ—a mishi.
murmushi yayi tare da cewa.
"Bubbuga rumbun Abboi".
Murmushi tayi itama tana mai share hawayen da suka silalo mata.
Ƙara mata yayi tare da ci gaba da bata.
Sosai kuwa taci tayi haniƙan.
Sheykh kuwa da wutsiyar idonshi yake kallon dukkan motsinsu.
Bayan tayi gyatsa ne, Ummi ta matsar da kwanukan.
Babu yadda Sheykh da Umaymah basuyiba, amman Al'amin da Bappa sunƙi suci abinci.

Kiran sallan azahar ne,
Yasa duk suka miƙe.

Cikin sanyi Al'amin ya kalli ogogon hannunshi da yaketa sheƙi yace.
"Bappa muyi salla mu tafi kada lokacin ya ƙure mana".
Cikin kula Umaymah tace.
"Ba kwana zamuyi ba".
Murmushi Bappa yayi tare da cewa.
"A'a zamu koma tunda jiki da sauƙin gata taci ta ƙoshi tana hira."
A hankali Ummi tace.
"Eh ai dama haka takeyi, anjima kuma in ciwon ya tashi zakace kamar zata shiɗe, sai an mata tofi take ɗan samun sauƙin".
Murmushi Al'amin yayi tare da kallon Sheykh cikin nitsuwa da gogewar cikar wayewar dake nuni ba makiyayin daji bane yace.
"Sheykh ka samu sabuwar wayar hannu, kenan tunda sai kayi tofi akejin sauki.
Dan Allah duk inda kake ta kasance a nan a ƙara kulan mana da Boɗɗin Abbai".
Murmushi ya É—anyi tare da cewa.
"In Sha Allah".
Cikin karrama Sheykh ya nuna musu wata ƙofar dake gefen ɗakinshi yace.
"Ga wuri kuyi al'wala mu tafi masallacin".
kai Al'amin ya gyaÉ—a kana yace.
"Bappa je kayi al'wala kazo mu tafi.
Cikin nitsuwa Bappa yace da al'wala ta".
Shima Al'amin gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"Nima inada al'wala".

Cikin gamsuwa Sheykh yace.
"To bisimilla muje nima da al'wala".
To sukace kana duk suka nufi babban falon.

Suna isa tsakiyar falon. Al'amin ya É—an tsaya tare da cewa.
"Parvina zo".
Da sauri ta ƙaraso gabanshi.
Shiru sukayi jin Al'amin ya juya harshe zuwa wani Yaren ba larabciba ba Turanciba ba hausaba ba fillanciba.

Mgna yakeyi riƙe da hannunta.
Ita kuwa Aysha kai taketa gyaÉ—a mishi ido cike da kwalla.
Hannunshi yasa ya share mata hawayen kana yasa hannunshi ya shafa kanta tare da juyawa ya fita.
Ita kuwa Aysha cikin sanyi tace.
"Bappa dan Allah a kawo min Junainah".
Kanshi ya gyaÉ—a kana shima ya fita.
Binsu a baya Sheykh yayi.

Ita kuwa hannunta mai lfyar tasa ta share siraran hawayen da suka zubo mata.
Kana ta juya ta nufi É—akinta.
Ummi da Umaymah kuwa kallon juna sukayi suma suka wuce É—akin su.

Bayan an idar da sallan ne, Sheykh da kanshi ya É—auki su Bappa ya kaisu tasha kamar yadda sukace.

Bayan ya kaisune. Yayi musu fatan isa lfy ne, yaja motarsa kamar ya tafi.
Ya koma can baya ya ajiye motar kana ya kira Ado drevernshi da yake cikin but ya fito.
Sannan yace.
"Bisu".

Da sauri Ado yabi bayansu.

Shi kuma yayi gida.

A hankali Ado yake binsu.
Ga mamakinshi sai yaga sun tari taxi sun shiga.
Shima taxi ya tsaida ya shiga,
tare da cewa.
"Bisu duk inda suka nufa."

To yace, kana yabi bayansu kai tsaye international airport Ɓadamaya suka shiga.
Suna shiga.

Kuwa suka fito. Suka biya mai taxi ɗin da kuɗin ma da bana ƙasar Nigeria bane kuɗin ƙasar Cameroon ne.
Cikin sanyi Al'amin yace.
"Yi haƙuri bamu da canji ne, kaje wurin yan canji za'a canza maka su zuwa Naira".
Cikin jin daÉ—i mai taxi É—in ya tafi.

Shima Ado ya sallami nasa mai taxi É—in.

Kana yabi bayansu tafiya kaɗan sukayi yaga wasu mutane a ƙalla su shida, sunbi bayansu duk suna cikin shigar sut.

Al'amin dake gefen Bappa ne ya miƙo wa ɗaya na kusa dashi hannu.
Wayar iPhone ƙirar wannan shekarar ya miƙa mishi.
Sai kuma system É—inshi.
Daga nan kan tsaye sukaje suka shiga jirgi.
Dole Ado ya rakasu da ido.

Su kuma jirgi ya É—aga dasu.

Tun kafin Ado ya koma gida ya kira Sheykh ya labarta mishi.
Murmushi Yayi jin abinda Ado yace mishi. Kai ya jinjina tare da danna wasu ababe a wayarsa.
" ?+? ".
Murmushi yayi kana ya jefa woyar a al'jihunsa.

Bai shiga gidaba sai bayan sallan isha'i.
Chapter 118 · 0% Book details