Sashe 117
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin zillo tayi tare da sunkuyar da kanta ta kifeshi kan hannun kujerar da LamiÉ—o ke kai.
Gaba É—aya jikinta karkarwa yakeyi tamkar mazari.
A haka ya gama shafe magungunan sannan ya bata wani yace sai dare ta shanye shi.
Ummi ce ta amsa tare da yi mishi godiya.
Kana LamiÉ—o da Galadima sukayi mata sannu da jiki suka tafi.
Suna fita, ta miƙe da sauri ta nufi falon ta.
Da sauri Ummi ma tabi bayanta tana cewa.
"Lafiya kuwa."
Babu mgna tana shiga kan gado ta faɗa ta kife kanta a filo murya na rawa alamun sanyin zazzaɓi tace.
"Ummi rufeni rufeni sanyi zai kasheni a kashe min AC."
Da sauri ta ajiye maganin kana ta rufeta da jibgegen blanket É—in sannan ta juya ta kashe AC'n.
Ta dawo gefenta ta tsaya.
Cikin al'hini take cewa.
"Sannu! Sannu ko Aysha".
Ina babu mgna sai karkarwa takeyi tamkar zata faɗo ƙasa.
Haka yasa hankalin Ummi tashi.
Shigowar Aunty Juwairiyya ce da ta kawo musu abincin rana.
Dana tarban Umaymah ne.
Cikin mamaki tace.
"Ummi ko dai in kira. Sheykh yazo muje asibitine gafa yadda take rawan sanyi".
Ummi kam tama rasa bakin mgn, shiru kawai tayi tana riƙe da haɓa.
Suna cikin hakane Hajia Mama ta iso.
Cikin tashin hankali tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummin Jabeer ya za'ayi da wannan yariyar ne? Mu tafi asibiti fa, da sauri ta juya ta fita zata kirawo Affan.
Tana fita da miti bakwai. Su Umaymah suka shigo.
Kai tsaye suka wuce har cikin É—akin jiyo mgnar su Ummi a can.
Shi kuwa Sheykh, asibitin Valli ya wuce.
Umaymah na shiga ta isa bakin gadon.
Zama tayi a gefe tare dasa hannu ta buÉ—e borgon.
Ganin yadda taketa karkarwa ne, yasa Umaymah É—agota ta É—aura kanta bisa cinyarta.
Tana cewa.
"Innalillahi wannan wane irin sabon al'amari ne mai firgitarwa".
Da sauri tace.
"Hibba kiyi gudu ki kirawo min Jazlaan kada ya fita."
Da sauri Hibba ta juya ta nufi waje.
Ita kuwa Ummi da Aunty Juwairiyya ko sannu da zuwa Allah bai basu ikon yiwa Umaymah ba sabida ruÉ—ani.
Wani irin numfarfashi ta fara fiddawa a jere-a jere sai ga jikinta ya fara lafawa da rawan da yakeyi.
Wani irin zufa ya fara tsastsafo mata duk ta inda hudar gashi yake a jikinta.
Cikin sanyi suka fara sauƙe ajiyan zuciya.
Suna cewa.
"Alhamdulillah".
Gyara mata konciya Umaymah tayi ganin tayi bacci.
BuÉ—e mata borgon tayi kana ta kalli Juwairiyya tare da cewa.
"Kunna AC".
To tace kana ta kunna.
Ajiyan zuciya ta sauƙe da ƙarfi.
Haka yasa Umaymah ta sauƙo kan gadon.
Cike da al'hinin abin suka fito falonta suka zauna.
Juwairiyya ce taja jakar Umaymah ta kai É—akin Ummi.
Kana ta fito.
Cikin sanyi Ummi tace.
"Umaymah sannu da zuwa ya hanya".
Tallaɓe habarta tayi tare da cewa.
"Uhummmm Alhamdulillah Ummi ya mai jiki".
Cikin sanyi tace.
"To jiki kam dai babu daÉ—i.
Sai dai godiyar Allah".
Cikin sanyi tace.
"Dukkan tsanani yana tare da sauƙin.
Ya iyayenta sunji ko?".
Kai ta gyaÉ—a alamun eh.
Juwairiyya ce taje falon ta kawo mata ruwa da abinci.
A hankali tace.
"Juwairiyya ajiye abin cinnan bazai ciwuba".
Dai-dai lokacin Hajia Mama ta shigo da Affan yana cikin kiÉ—ima.
Ganin Umaymah ne yasa suka zaune kusa da ita tare da cewa.
"Ya jikin nata".
"Alhamdulillah ta samu tayi bacci."
Umaymah ta basu amsa.
Cikin kula Hajia Mama tace.
"Sannunki da zuwa, ya hanya".
Yauwa sannu Alhamdulillah tace.
Hibba ce ta dawo tacewa Umaymah kafin ta fitama ya tafi.
To kawai tace.
Daga nan suka zauna suna al'hinin abin.
Har azahar tayi nan suka watse kowa taje tayi salla.
Ita Umaymah a É—akin Aysha tayi salla.
Bayan sunyi sallan ne Ummi ta kawo musu abinci suka É—an ci.
A nan suka zauna Ummi da Umaymah a É—akin Aysha.
Juwairiyya kuma taja Hibba suka tafi dan yin girkin dare.
Haka suka zauna har la'asar bata tashiba.
Sheykh kuwa sai ƙarfe biyar na yamma ya dawo gida daga asibitinshi.
Nasa falone ya wuce Side É—insa kai tsaye.
Biyar da miti bakwai dai-dai ta farka daga nannauyan baccin azabar.
Da sauri Umaymah tayi kanta.
Ganin tana ƙoƙarin tashine yasa Umaymah taimaka mata.
Cikin disashewar muryar tace.
"Lah Umaymah yaushe kikazo? Sannu da zuwa".
Cikin tausaya mata tace.
"Sannu Aysha ai ke za'a cewa sannu. Ya jikin naki".
Cikin sanyi tace Alhamdulillah".
Sai kuma ta zuro ƙafafuwan ƙasa tare da cewa.
"Umaymah zanyi salla zanyi wonka".
To tace da sauri kana ta juya zata shiga bathroom É—in.
Da sauri Ummi tace bari in haÉ—a mata ruwan wonka."
Umaymah kuwa kamota tayi ta tsayar da ita.
Dai-dai lokacin Ummi ta fito hannun ta zubawa ido cikin sanyi tace.
"Ya naga kamar hannun ya ƙara kumɓura ne?".
Kallon hannun sukayi a tare.
Cikin sanyi tace.
"Eh kamar ya ƙara kumɓura".
Umaymah ce ta É—an kalli hannun kana tace.
"Je kiyi wonka ki fito kizo kiyi salla kici abinci, in baki mgnin da nazo miki dashi."
To tace kana ta nufi Bathroom É—in tana cewa.
"Bana iya gogo sosa a jikina sai sabulu kawai.
Shiyasa nakeji kamar ba wonka nakeyi ba".
Cikin tausayawa Ummi tace.
"Allah sarki in kin samu lfy dai shike nan".
A haka ta shiga bathroom É—in yau ko sabulun bata iya gogashi da kyauba.
Ita kuma Ummi kaya ta fito mata dashi kamar kullum.
Ita kuwa Umaymah Dinning area taje.
Ta É—auko Foodflaks É—in da plate ta dawo nan.
A hankali ta fito bathroom É—in.
Cikin É—aga hannun sama ta kalli rigar da aka fito mata dashi a hankali tace.
"Ummi bazan iya sashi ba, matsastsene a bani mai faÉ—i".
To Ummi tace ta sauya mata wani.
Mai faÉ—in ita kuwa dogon wondon dake kan gado ta É—auka ta koma bathroom ta saka da kyar sannan ta fito.
Koda Ummi ta bata rigar sai ta gaza sata.
Ido cike da hawaye tace.
"Ummi samun hannun rigar a hannu mai ciwon a hankali kada ya taɓa shi, sai kin buɗashi da hannu biyu.
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Bakisa bra É—inba".
Kanta ta sunkuyar tare da cewa.
"Bazan iyaba".
Shiru Umaymah tayi tana tunanin dole jinyar hannu sai da mataimaki.
Ita da Ummi kuma surkaine Hibba ƙaramace.
Shiru dai tayi tana nazari.
Bayan Ummi ta taimaka mata tasa rigar ne.
Ta saka hijabi tayi sallan a daddafe da taimakon lafiyayyan hannun.
Tana idarwa Umaymah tasa mata abinci a plate kasan cewar tuwone da miyar ganye da É—an tsami.
Sai ya zama gaba É—aya a kaikaice take sa spoon É—in da niyar gutsuro tuwon.
Kuma taji tana son cin miyar.
Da kyar ta gutsuro gaya ta É—an É—ebi miya ta É—aya zata kaishi bakinta kenan ya faÉ—i a jikinta.
A hankali ta kallesu cikin sanyi tace.
"Umaymah a bani tea kawai bazan iya cin wannan ba, zai tazubewa."
Da sauri Ummi ta gyara zama tare da cewa.
"To matso in baki".
ÆŠan gajeren murmushi tayi cikin jin kunya tace.
"A a bari in sake gwadawa to".
Dai-dai lokacin Sheykh da Umaymah ta kirashi a waya ya shigo yanata buɗe al'kyabbar jikinshi gudun kada a iya ganin tudun abinda yake ɓoyewa.
A bakin ƙofar ya tsaya tare da yin sallama.
Cikin É—an É—aga murya Umaymah tace.
"Shigo".
A hankali ya tura ƙofar ya shigo.
Tunda tazo gidan tsawon watanni biyu kenan yanzu bai taɓa tako ƙafarsa nan ba sai yanzu.
Ta gefen ido ya kalleta ta sake ɗaukan loma a karo na uku kafin ta kaishi bakinta ya ɓare.
Ture plate É—in tayi tare da cewa.
"Bana iya cin abu da hagu gwara tea zan iya kafa kofin insha wani wani ya É—an zube".
Ta ƙarishe mgnar tana shere hawayen da suka zuba mata.
A hankali Ummi taja flaks ta fara haÉ—a mata tea.
Umaymah kuwa.
Gefenta kan Bedside drower'n ta nuna mishi tare da cewa.
"Zauna".
fuska ya É—an kauda kana ya zauna.
A hankali tace.
"Me zamuyi kan hannun yarinyar nanne?".
Cikin jin haushi yace.
"Sai abinda su LamiÉ—o sukace ai.
Ni Ko nayi mgna sai sun musamin ya rigada sun maidani kamar sa'ansu, bani da ancin mgn kan komai nawa sai yadda suka tsara min in naƙi bin unarninsu keda Abba kuyi faɗa, to ya zanyi?".
Murmushi Ummi tayi ganin yadda yayi mgnar a tsare kamar shine babba a kansu ba suba wai sun É—auke shi sa'ansu.
Ita kuwa Umaymah cikin sanyi tace.
"Kaga bata iya ko cin abinci tana bukatar kulawa ta musamman.
Wonka ma wuya yake bata haka al'wala ko kaya sai an saka mata".
A hankali yace.
"Toh lallai kam Allah ya baku ladan jinya".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Amin". A ranta kuma tace.
"Zanyi mgninka".
Ganin tayi shiru ne ya sashi miƙewa tare da cewa.
"Allah ya sauwaƙa kana ya fita."
Yana mai jin zafin katsalandar dasu LamiÉ—o ke mishi a kan lamuran rayuwarshi, komai nashi sai sun saka mishi baki. Yace kar asa mgnin amman dan rainin wayo sunce dole sai an saka.
Su Umaymah kuwa nan suka zauna har akayi sallan magriba.
Su Jalal Jamil Affan sukazo suka ci abinci aka É—anyi hira dasu.
Har zuwa ƙarfe goma na dare hannun shiru ba ciwon sosai.
Haka kowa ya shiga yana cemata saida safe Allah ƙara sauƙin.
Umaymah tace Ummi ta tafi da Hibba É—akinta ita zasu kwana tare.
Haka kuwa akayi, har sun fara bacci.
Habawa sha É—aya dai-dai,
Ciwo yace salamu alaikum.
Tashin hankali iya tashin hankali Umaymah ta ganshi a ranan.
Domin har gabanin asuba basu rintsaba kamar dai yadda ta kwana jiya da Ummi abinma har yafi haka yau.
Sau biyar Umaymah na kiran layukanshi duka basa shiga.
Kuma Aysha guduwa kawai take nufa.
Haka yasa dole tai ta riƙe ta.
Asuba na ƙaratowa tayi bacci kamar na jiya.
Sai da akayi sallan Umaymah ta tada ita.
Tayi salla lfy tasha tea.
ta koma bacci rana na fitowa ciwo ya dawo.
Gaba É—ayansu sun gigice sun tsorita da lamarin Umaymah ta tura Ummi taje ta gayawa LamiÉ—o yazo yaga yadda take.
Hibba kuwa da Saratu sun kasa yin aikin da aka sasu sai kuka.