Sashe 45
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ArÉ—o Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa.
"To, ina gwanin naku?".
Cikin karaÉ—i ÆŠanzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa.
"Malami ba faÉ—en Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero JoÉ—a, GARKUWAN sarki LamiÉ—o, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar JoÉ—a."
Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma'anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi,
Cikin yin ƙasa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya ɗan ronƙofo kanshi, kusa da Lamiɗo murya a kausashe yace.
"Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace".
Da sauri LamiÉ—o ya katseshi da cewa.
"Eh amman koyarwar Masarautar JoÉ—a ce".
Cikin kufula yace.
"Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar JoÉ—a ce".
Cikin haɗe fuska da ƙasaita Lamiɗo yace.
"Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce".
Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taɓe fuska yace.
"Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje".
Cikin kausasa murya LamiÉ—o yace.
"Kai ne dai zaka tashi".
Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace.
"Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?".
Cikin faÉ—a LamiÉ—o yace.
"To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba".
Jin muryar Lamiɗo ta ɗan yi samane, yasa fadawanshi suka miƙe tsaye,
Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu,
Cikin haÉ—e fuska Jabeer yace.
"Yesss shi bazai ƙiba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ƙaton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaɗaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ƴaƴan ai, ka kira ɗaya daga cikin ya'yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya'a in tsaya wani gardin makiyayi ya ɗimeni, tunda ba faɗin Allah bane".
Ya ƙarishe mgnar yana yunƙirin tashi tsaye.
Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaɓe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al'kyabbar jikinshi,
Cikin tausasa harshe Galadima yace.
"Jabeer kafa san ma'anar GARKUWA a masarauta."
Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaɓe fuska tare da cewa.
"Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani."
Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace.
"Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine".
Rai a ɓace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace.
"Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama".
Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata.
Jalal kuwa cikin haÉ—e fuska yace.
"Wannan ma ai zancen banza ne,
An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi."
Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya É—aga mishi hannu.
Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ƙarar da ƴaƴan ɗakinsu,
Laminu kuwa É—an Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daÉ—i yakeyi.
Shi kuwa LamiÉ—o, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi.
Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.
A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni.
ArÉ—o Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa.
Ana gamgamin ShaÉ—i yanzu-yanzu tsakanin Ba'ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.
Tuni an firfito da ganguna anata kaÉ—e-kaÉ—e da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za'ayi ShaÉ—i yanzu.
Kafin kace kobo, Rugar Bani ta cika tayi maƙil da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za'ayi Shaɗi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za'ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma'ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma'a.
Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa.
Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.
Bukar kuwa mahaifin Ba'ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya É—auko tukunyar tsumin bulalim shaÉ—in da Ba'ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon.
Matasa majiya karfi ne keta É—ebo ruwa, cikin rijiyoyin garin.
Suna jiƙa taron wurin dandamalin, da za'ayi gasar kaɗe-kaɗen duk sun taru sun cika kunnen kowa.
Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali.
A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito.
A gidansu Shatu kuwa,
Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar ShaÉ—i tsakanin Ba'ana da jikan sarki.
Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiÉ—ima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace.
"Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi."
Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace.
"Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na haƙura zan auri ya Ba'ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ƙoƙarin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina".
Da sauri Rafi'a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace,
"Rafi'a wlh ya Ba'ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahaluƙin da zai iya cin Ya Ba'ana gasar Shaɗi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa."
Cikin sauri ta miƙe tare da miƙar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna,
Jin muryar maƙocibsu Sarkin aska, yana cewa.
"A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya .
Yanzu ma ArÉ—o Bani ne ya aikoni da in gargaÉ—eki."
Yana faÉ—in haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar.
Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta miƙa ta nufi kitchin ɗin su, tana cewa.
"Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba'ana ya kawo mana muci.
ÆŠazu da nace muci Adda Rafi'a ce, tace mujiraki."
Cikin sanyi Rafi'a tace.
"Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba."
Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace.
"Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma taƙi cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji ɓatansu ya Giɗi da rasuwar Ya Lado da Inna."
Cikin zubda hawaye ta gyaÉ—a mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta.
Da sauri Junainah ta nufosu riƙe da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin.
A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa.
Tuni su Ba'ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ƙa'ida shi zai fara duka,
Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaÉ—a da mabusa nata yi mishi kirari.
A cikin wurin da Fadawa suka kange LamiÉ—o da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer,
Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi.
"Nifa babbar matsalarta wannan abun da za'ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taɓa cin karo da wannan banzar al'adar da kukeso in yarda ayita dani ba,
Ina kuma da yaƙini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za'a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan Lamiɗon Joɗo da yaji haza a gasar Shaɗin shine ya hana wannan al'adar a masarautarsa sannan yanzu ace za'a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba'ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba."
Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace.
"To ya kakeso ayi ɗan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da ɗan karen son jiki kana gudun abinda zai taɓa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir ɗin kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba".
Gaba É—aya sun hautsuna mishi zuciya,
Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al'adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a ɓace yace.
"Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za'ayi wannan abunba, sun daÉ—e basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane.
A kirani da ko wacce ƙabilar ma in anga dama aikin kawai!".
Yana faÉ—in haka ya katse kiran.
Laminu kuwa da yake cikekken É—an jarida, tuni yana naÉ—e komai a faifai jawaban su.