← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 183

Sashe 39

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi kuwa Sheykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes,
fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi.
Yunƙurowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buɗe idanunshi.
Da sauri ya kauda ƙwayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa,
Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace.
"Innallaha ma'assabirin".
Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ƙara sashi jin ƙarfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ƙara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan baƙin cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami.
Tana ƙara nusar dashi.
A hankali yace.
"Barka da safiya Mama".
Murmushi tayi kana tace.
"Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta,
Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya ɓata maka rai daga dawowa?".
Cikin sanyi yace.
"Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Tsoho mai ran ƙarfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?".
"Alhamdulillah". Yace mata, yana mai sa hannu ya É—auki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya É—aura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi.
Ita kuwa Batul ido ta ɗan lumshe, ganin yadda ya tamƙe fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ƙasaita.
A hankali ta buɗe idonta kana ta sauƙesu kan sajenshi,
Wani gajeren tsaki yaja,
tare da kauda fuskarshi.
Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi.
"Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa'a, Uhumm jin kai da ƙasaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana."
A hankali tace.
"Ya Jabeer ina kwana".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai.
Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta É—an, kalleshi tare da cewa.
"Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo".
Kanshi ya ɗan rusunar tare da miƙewa tsaye, cikin sanyi yace.
"Masha Allah".
Daga nan ya É—anyi taku biyu zuwa uku, kana yace.
"Mama barin inje inyi shirin jumma'a".
Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.

Daga nan shi dai yayi, ciki.
Su kuma suka, fita.

Haroon kuwa Data ya kunna,
Umaymah ya turawa video É—in da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.

A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan mayaƙan cikin garin Shikan ɗin sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja'iunsu, suna mitin.
Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin Ɓadamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.

Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa.
Dan an fara rade-raɗin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu ɗauki fansa, to shisa ƙabilar ɓachama suma suketa guzurutsoma, har ta kai da matakin in dare yayi matasan hausa fulani na cikin garin ma zauna cikin garin Numan, sai su futo suyi ta yawo da makawai suna kare amguwanninsu.
Kana suma ƙabilar ɓachama sai su fito da makamai suna kare amguwanninsu.

Shatu kuwa basu wuce cikin Ɓadamaya ba, sabida Ummiy ta dawo hayyacina ta, hakama Junainah ta dawo haiyacinta da ƙarfin addu'o'in da Aysha da Bappa keyi.
Dan haka su cikin Rugarsu-suka koma.

Shatu kuwa, tunda Junainah ta gaya mata batun ɓacewarsu Ya Giɗi da kuma kashe ya Lado da akayi, har zuwa yanzu bata daina kukaba.

Koda Ba'ana yazo wurinta daren jiya, da yaji lbrin sun dawo babu abinda takeyi sai kuka.
Shi kuwa Ba'ana, baƙin cikinsa shine da Ummiy ds Junainah da Bappa suka rayuwa,
Shiyasa yanzu, yayi musu nasu shirin mutuwa namu samman.

Inda Bugulu Maman Ma'ans ta gasa zabbbin da Ba'ana ya yanka, kana ta daka musu, yajin borkono, da busasshen kan maciji.
Ta barbaÉ—a musu, kana ta yaryaÉ—a man shanune da ya gauraya da dafin macijin cikin man shanun da tayi musu gashin dashi, kana ya nufi, bakin garkensu, da akoshin gasassun zabbin.
Sannan ya aika aka kira mishi Shatu,
cikin kuka Rafi'a tacewa ɗan aiken yaje, ya zazzaɓi ke damunta.
Koda yaron yaje ya gaya mishi,
sai yace zai a kira mishi Junainah,
Koda yazo ya gaya musu,
Sai Junainah ta miƙe tabi bayan ɗan aiken.
Kasan cewar garken nasu ba nisa, tafiya kaÉ—an tayi ta isa, ta isa ta zauna a bakin Æ´ar bukkarsa da yake, cikin.
cikin disashewar muryar hawaye na zuba tace.
"Ya Ba'ana, kaje ka dubo jikin Ya Junaidun ne?".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau, cikin sanyi yace.
"Eh naje na dubashi, jikinshi da sauƙi, ke ya naki jikin? Ya Ummiy da jiki".
Cikin sanyi tasa hannu ta share hawayenta dake shatata kana a hankali tace.
"Ummiy jikinta da sauƙi sai dai har yanzu bata mgn, Adda Shatu kuma sai kuka takeyi".
Hararanta yayi a fakaice, ji yake kamar ya jawota ya caka mata mashi ya mata kisan zahiri sai kuma ya fasa,
Kanshi ya kauda tare da tura mata akoshin gasassun zabbin nan kana yace.
"Ayyah sannu Junnuna, kiyi haƙuri dena, kuka, kici nama, sai kije kicewa Mata, tazo zan gaya mata inda su ya Giɗi suke".
Cikin rawan jikin jin yunwa tace.
"Yauwa bani inci dama yunwa nakeji, tun jiya banci komaiba, tunda muka dawo, bamuyi girkiba."
Da sauri ya turo mata akoshin tare da buÉ—e mata fefeyin.
Cikin rawan jiki irin na masu jin yunwa tasa hannu ta...!

Uhummm Allah kaimu gobe lfy, mu ƙara sa free page, daga PAGE 15-16 an gama.

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 15

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘

*Littafin GARKUWA na kuɗine, daga wannan PAGE 15 da 16 FREE PAGE sun ƙare, turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276, ko ki turo dubunki ɗaya rak dan shiga Special Group, wanda anfi yawan posting, ta wannan asusun zaki turo 1k ɗin 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*

```Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki in dai kin san kin sayi littafina ne ko zaki sayane ɗan ki fitar min dashi na roƙeki da Allah da Manzonsa🙏🏻 kada ki saya, in kuwa har kin sayane kawai gaya min in biyaki kuɗin ki ki barmin littafina, mu rabu innahu annahu.```

Akwai kayyakin gyara namu mata setin amare da masu jego, da masu kwaskwarima, idan kina buƙatar saya ko sari, tuntuɓi wannan number tawa 09097853276.

Hannu tasa ta jawo pepeyin jin yana ce mata.
"Kici kije da gudu ki kira Mata, tazo in gaya mata, su Ya GiÉ—i sun kusa dawowa ta dena kuka, anji lbrin inda suke".
Rufe akoshin tayi kana ta miƙe da sauri tace.
"Da gaske ya Ba'ana an ji inda suke?".
Cikin haÉ—e fuska yace.
"Na taɓa yimiki ƙarya ne?".
Da sauri ta jujjuya kanta kana tace.
"Bari inje in gaya mata tazo sai inci naman a gida".
Da sauri yace.
"A a jeki kirata, in tazo sai ki tafi da naman, kije kuci keda Ummiy da Bappa da ita ƙawar Mata, ita kuma zan bata nata a nan".
Ai tana jin hakan ta juya ta tafi, da sassarfa.

Tana isa gida, ta kamo hannun Shatu, cikin haki tace.
"Adda Shatu taso, taso muje ya Ba'ana zai gaya miki inda su ya GiÉ—i suke, yace anji lbrinsu".
Wani irin zabura tayi, hakama Rafi'a dake bakin ƙofar kitchin ɗinsu.
Cikin tarin kaÉ—uwa tace.
"Ke Junainah, kada kiyi mana ƙarya".
Cikin haki tace.
"Wallahi tallahi, haka yace min zo muje kiji".
Da sauri ta kamo hannun Rafi'a tace.
"Adda Rafi'a kema zo muje tare".
Cikin jin daÉ—i Rafia tace.
"A a Junainah kuje, Ni kuma kafin ku dawo nayi mana abinda zamuci, da sauri tace.
"A a Adda Rafi'a ki bari kar kiyi girki, Innar ya Ba'ana ta aiko mana gasassun zabbi yanzu zan amso mana su sai muci".
Murmushi tayi kana tace.
"To sai kinzo".
Ita kam Shatu tuni ta fita, ta nufi Garkensu Ba'ana.

Ita kuwa Ummiy ido kawai ta zuba, musu tana son ta kira Shatu ta hanata zuwa amman ta kasa.

Ita kuwa Rafi'a kitchin É—in ta shiga.
Chapter 39 · 0% Book details