← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 183

Sashe 136

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty Rahma ce ta É—an harareta tare da cewa.
"Maza tashi a jikinta ki barta ta huta".
da sauri ta ɗan zame ta sauƙa ita kuwa.
Aysha kai ta É—an karya tare da cewa.
"Aunty Rahma barta".
Safiyya ce tace.
"Ahyya baki san Ishma bane da shegen surutu da son jiki".
dariya sukayi ganin yadda Ishma ta zumbura baki.
Sitti ce ta miƙe tsaye tare da kallon jikokin nata da yar autar tata, tace.
"Toh maza ku tashi muyi sallan azahar, in mun idar ku isa wurin Jadda ku gaisa."
Kusan a tare suka mimmiƙe, Aunty Rahma ce ta kamo hannun Ishma tare da cewa.
"Jadda ya fita, ai É—azu ya kirani yace in masa abincin dare, wai ya É—an fita zai kai dare kafin ya dawo".
Dariya Sitti tayi tare da cewa.
"Uhumm kai Jadda wato ki masa abincin dare. In kun koma kuwa naga wa zai ce ta dafa mishi".
Safiyya ce tace.
"Oh zai ci girgikin yar autarsa".
Ita dai Ramatu murmushi tayi tare da cewa.
Aysha Juwairiyya Jazrah Safiyya mu tafi É—akina".
To sukace kana suka bita a baya.
Har zasu fitane Sitti tace.
"A a Aysha dawo nan, ke kam baƙuwa tace ga masauƙinki".
Murmushi Aysha tayi kana ta juyo ta dawo sabida tafi gamsuwa da zama kusa da Sitti akan a tsakiyar Juwairiyya da Jazrah dake mata wani irin mayataccen kallo.

Haka dai sukayi sallan azahar,
kana suka fara shirin kamu.
Wanda tuni ango Haroon da tawagar abokanshi sun iso.

Anayin Sallan la'asar suka fara.

Sai gab da magriba suka tashi.
Ranar kusan kwanan zaunen sukayi anata hirar yan uwantaka.
Yayinda Aysha bata gajiya da jin muryar Aunty Ramatu da kallon fuskarta da fuskar Ishma.

Basu samu sun isa wurin Jadda ba.
Sun bari a akan sai gobe da safe in Allah ya kai rai.

A can Tsinako kuwa, gaba ɗaya al'ummar masarautar Tsinako da baƙi abokan Abbansu Haroon dana kakansu Sarki.
Da kuma baƙi na nesa dana kusa duk an kwana cikin shirin, tafiya ɗaurin auren.
Masu tafiya a jirgi ƙarfe tara jirginsu zai tashi.
Masu tafiya a motoci kuma sammako zasuyi.
Sabida sha É—aya na safe za'a É—aura auren.

Haka kuwa akayi washe gari da safe masarautar Jalaluddin, ta fara amsar baƙi tako wani saƙo na ƙasar Nigeria.

Fadar masarautar dama farfajiyar ta cika tayi tab da baƙi da ƴan gari, tako ina halarta mutane keyi.

Karfe sha É—aya dai-dai na safe taron al'ummar musulmi suka shaida É—aurin auren Haroon da Jannart.

Bayan an É—an wawwatse mutane duk sun kama hanyar komawa inda suka fito.
Sai Abokan ango da zasu ɗauki ƙawayen Amarya da wasu yan uwa.
Dan amarya dasu Aunty Juwairiyya da Jazrah da Aunty Rahma Ishma da ƙannen mamansu Jannart duk sun tafi a jirgi, da ango.
Safiyyah da Aysha da Azeema da Hibba ne kaÉ—ai suka rage.
Dan Safiyyah ce ta hana Aysha tafiya dasu Auntyr Rahma tace, ita tare zasu tafi.
Haka kuma Sitti ma tace haka yasa koda suke ribibin tafiya ita tana bacci a É—akin Sitti bisa gadon mulkinta, dan kwanan da sukayi ba bacci yasa duk suna cike da bacci.

Ibrahim da Sheykh kuwa sune suka tsaya da wasu abokan Haroon biyu, sai sunga duk mai buƙatar zuwa ta tafi.

Ƙarfe sha biyu dai-dai Sheykh Jabeer da Ibrahim da Munnir da Mansur abokan Haroon Suka shigo babban falon Sitti.

A nan suka samu Jalal da ya Jafar da Ammar ƙanin Aunty Juwairiyya da Ibrahim wanda shine yayan Jannart.

Sai kuma Goggo Mairo ƙanwar Jadda da kuma sauran yaran Jadda wanda kishiyoyin Sitti suka haifa.

Safiyyah na ganin shigowarsu ta miƙe ta nufi Dinning area fridge ta buɗe ta haɗo musu ya'yan itatuwa masu sanyi, ta gyara kana ta kawo musu.

Bayan sun gaggaisa ne,
Ibrahim ya É—an kalleta tare da cewa.
"Kun gama shiryawa ko?".
Kai ta gyaÉ—a mishi al'amar eh.
Sai ta kuma kalli Sheykh dake miƙawa Ya Jafar nonon inabi yana kuma ce mata.
"Sitti fa?".
jujjuya kai tayi cikin falon ta kalli gabas da yamma kudu da arewa.
Gane wai neman inda Sitti takene yasa Goggo Mairo cewa.
"Bata nan ai ta fita".
ɗan miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"Ikon Allah kuma fa da muna nan tare da ita. To ina tayi".
Aunty Salima wacce take itace Babba a yaran Jadda ne tace.
"Nima fa ita nake jira".
Jalal ne ya ɗan kurɓi ruwan sanyi tare da cewa.
"To ko tayi ciki ne".

"Ba mamaki". Goggo Mairo tace.

Cikin nitsuwa Sheykh ya miƙe tsaye, kekyawar al'kyabbar jikinshi ya ɗan buɗa tare da gyara zamanta jikinshi.
Corridor'n da zai sadashi da special Side É—in Sitti ya nufa, a nitse.

A can bedroom É—in Sitti kuwa.
Aysha ce tsaye gaban dreesing mirror bayan ta gama ado da kolliyar ta.
Wani dandatsetsen Shadda lace ne mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi ne a jikinta, ɗinkin Doguwar rigace.
Ta zauna É—as a jikinta gwanin burgewa da ban sha'awa.

Kalan kayan sun taimaka kwarai wurin burgewa, dark red wine mai masifar kyau, sai ratsin zare Royal blue mai azabar kyau da sheƙi da aka zubashi suffar zanen ɗawisu.

Turare ta feshe jikinta dashi,
kana ta maida kolbar sannan ta dawo gaban dreesing mirror kujerar ta jawo ta zauna.
Kasan cewar dreesing mirror babbane mai tudu hakama kujerar.
hannu tasa ta fara tsaɓule ribon ɗin da ta tubke himilin gashinta dashi.

A nitse ya iso bakin ƙofar Bedroom ɗin Sitti.
hannunshi yasa ya tura ƙofar,
ɗan wani guntun tsaki yaja tare da sa guiwar yatsunshi biyu ya ɗan ƙonƙosa kofar sau uku.
Kana ya É—an tsaya gefe.

A hankali ta juyo kanta ta ɗan kalli bakin ƙofar,
har kamar bazata tashi ba.
Sai kuma ta tuna ta rufe ƙofar lokacin da Safiyya ta shigo ta tasheta kan ta tashi ta shirya su tafi.
To da zata shiga wonka ne ta rufe ƙofar dan tana jin kunya kada ta fito tana shiryawa wasu su shigo su sameta.

A hankali ta miƙa tare da juyawa ta nufi ƙofar tana ƙoƙarin warware ɗan kwalinta.

Isowarta bakin ƙofar yayi dai-dai da lokacin ɗaya kuma ɗan buga ƙofar.
Hakan yasa bata gama warware ɗan kwalinba tasa hannu ta buɗe ƙofar dan a zatonta Sitti ce ko Safiyyah.

Tana buɗe ƙofar sai ta ɗan koma da baya, haka yasa bata ganshi ba.
Bai ganta ba.

Kutsa kanshi yayi cikin É—akin tare da sallama a bakinshi.
kana yasa hannunshi ya maida ƙofar.
Kasan cewar dreesing mirror yana fuskantar ƙofar shigowan ne, yasa. Mutun zai iya ganin abinda ke bayansa muddin yana kallon cikin madubin.

Kanshi a sunkuye da alamu wayarshi yake É—an lallatsawa.

Haka yasa hankalinshi baya kan madubi.

Ita kuwa Aysha, wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe a hankali jin daddaɗan ƙamshin turaren jikinshi.

A hankali ta zubawa bayanshi idanu tun daga kan dudduniyar farar kekyawar ƙafarshi, har zuwa kan tattausan suman dake kwance lib a ƙeyanshi.
Kasan cewar da yasa hiramin yau yayi irin siririn sakun nanne ya tattare gefe da gefen hiramin.

Taku uku yayi ana huÉ—u ya tsaya cak, ba tare da ya É—ago kanshi ba ko ya juyoba, yace.
"Wannan kallon fa?".
Cikin tsananin mamaki da tsoron al'amarin Sheykh tayi saurin yin ƙasa da kanta.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya É—ago kanshi, ya dire idanunshi kan faffaÉ—an mafubin daya hasko mishi ita ras a ciki.

Shigarta surarta yanayin tsayuwarta da yadda take wasa da yatsun hannunta da kuma sumanta dake zube a kafaÉ—unta sunyi masifar jirkita mishi jiki da jini da kwanya.

Tabbas jikinshi ne ya sanar mishi ana kallonshi.
Shiyasa yace.
"Wannan kallon fa?".
A zatonshi ma Aunty Rahma ce, ko Sitti dan yasan sun iya tsura mishi ido duk da sun san baya son kallo a rayuwarsa.

Ita kuwa Aysha, Koda tayi ƙasa da kanta digadigin sawunshi ta zubawa ido.

Shi kuwa Sheykh a hankali yaja wani nannauyan numfashi ya sauƙe a hankali.

A hankali ya É—an juyo fuskarshi ya haÉ—e tare da cewa.
"Ke da izinin waye kika baro Tsinako kika zo nan?".

A hankali ta É—an É—ago kanta, kana ta É—an turo baki,
sannan ta gyara tsuyawarta, tare da cewa.
"Cemin akayi in zo".
Ta ƙareshe mgnar da yin taku biyu zuwa na uku da nufin zata koma gaban dreesing mirror ta ƙarisa shirinta.

Tana isowa gab dashi, da nufin zata wuce da sauri ta rumtse idanunta.
jin ya...

Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k a mako biyi huɗu ake gama Part one da two. Normal group Kuma 300 a mako takwas za'a gama Part one da two. Idan kina buƙatar special Group kimin TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta wannan number da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. In kuma Normal group kikeso na ɗari ukun, shima kiyi min TRANSFER ta ASUSUNA na Jaiz din in baki da halin turowa ta banki to ki sayi katin Mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ki turo min ta WhatsApp 09097853276. BANA SON VTU KADA KIYI MIN TRANSFER'N DIN KATI BANA SO.

By
*GARKUWAR FULANI*
Yasa ƙafarshi ya ɗan taɗe mata ƙafa.
Da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannunta ta kamo nashi ta riƙe gam.
Haka yasa bata ida faÉ—uwar da ta kusa yiba.
Chapter 136 · 0% Book details