Sashe 106
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka su Affan suka iso.
Suna Isa Affan ya ruggumeshi shima Sheykh ruggumeshi yayi tare da make ƙeyarsa.
Da sauri ya janye kanshi tare da cewa.
"Wayyo Allah na yanzu Hamma Jabeer na girma harda yaran nawama ban wuce dukaba".
Murmushi yayi tare da, Ruggume Yusuf da Aryan Allah ya sani yana masifar son yaran nan har gobe bashi da ɗalibai sama dasu yana sonsu so na musamman, duk sanda ya gansu yakan tuna ƙuruciyarsu tun suna yan shekara goma sha biyar-biyar yake tare dasu shi ya horas dasu.
Yana tura irin tarin ƙalubale da suka fuskanta a gasar Polo da kuma irin nasarorin da suka samu Especially Yusuf nashi yana tuna yadda yaran suke sheƙiyanci in sun haɗu, yana jinsu tamkar su Jamil.
Cikin murmushin ya shafa kansu tare da cewa.
"Sannunku da zuwa".
Cikin jin daÉ—i sukace to.
Bisa kujera ya zauna su kuma suka zauna a ƙasa a gabanshi kan carpet.
Ita kuwa Shatu a hankali ta juya ta nufi kitchen ganin Ummi ta nufi can.
Hibba kuwa na gefensu tana gayawa su Jalal ga Ya Affan fa.
Da gefen idonshi ya bita da kallo.
Har ta ɓacewa ganinsa, Allah ya sani yana son abu blue baya iya cire idonshi kan abu mai kalar shiyasa yake jin baya gajiya da ganinta, da zai samu kada tayi nesa dashi, dan tayi mishi kyau sosai farar fatarta ta fito fes kamar balarabiya ji yake tamkar ya bita duk inda tayi.
Cikin murmushin ya kalli Aryan yace.
"Aryan Ina su Yusuf ƙaramin".
"Alhamdulillah suna lfy Malam".
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Masha Allah".
Sai ya kuma kalli Yusuf yace.
"Ina mai sunana baka zomin da shiba".
Murmushi Yusuf yayi tare da cewa.
"Malam baka tambayi Aryan ƙaramin ba da yakeso ya zama kamarka sai ka tambayi mai sunanka".
Dariya sukayi kana yace.
"Ayyah my Aryan, sun kusa tafiya ai in sha Allah Jami'atul Madina zaiyi karatunshi".
Da sauri suka juyo suka kalli Jalal da Jamil da suka shigo da sauri.
Ruggume Affan sukayi suna cewa.
"Oyoyo ya Affan".
Hannu ya basu suka tafa kamar sa'ao',insa ne su.
Cikin dariya yace.
"Tun É—azu nake kiranku bakwa É—agawa.
Nace waÉ—annan ana can cikin hayani ".
Murmushi Jamil yayi tare da miƙawa Yusuf hannu wanda ke cewa.
"Oh wato Affan kawai kuka gani mu ko oho ko".
Cikin É—an sakin fuska Jalal yace.
"Afwan Hamma Yusuf ya Aunty Zahra da Mama".
"Suna lfy. Sun gaidaku". yace tare da bashi hannun.
Kana suka gaisa da Aryan.
Sannan suka miƙe sukace bari suje wurin Aunty Mami.
Cikin dariya Affan yace.
"Eh kujema kuzo da ita taga matar babban yaya".
Da sauri Jamil yace.
"A a ka kawota da kanka dai".
Ya ƙarshe mgnar suna fita.
Su kuwa cikin yin ƙasa da kai Yusuf yace.
"Uhum dama Malam zamu É—an shiga wasan daba ne in batsala".
Murmushi mai faÉ—in Sheykh yayi tare da cewa.
"Wato ku dai har yanzu baku girma da batun doki ba".
Shiru sukayi sai Affan ne yace.
"Tab Yusuf kuma da in ya ga doki bai hauba jikinshi har rawa yakeyi".
Murmushi Sheykh yayi kana yace.
"To muje muyi salla. Tukun tunda sai anyi sallan la'asar za'a fara ko".
To sukace tare da miƙa ganin ya miƙa dan tuni uku da kwata ta wuce.
Affan ne ya kira Ummi tare da cewa suzo zasu tafi.
A tare suka fito kitchen.
Sabbin kuɗi rafa yan dubu-dubu Yusuf ya miƙawa Hibba ƙulli ɗaya dubu ɗari kenan yace.
"Gashi miƙa wa Ummi ta raba muku."
Affan ma ya basu.
Hakama Aryan.
Hibba sai tsalle take tana cewa.
"Yessss my brother's Allah ya ƙara buɗi Amin Amin sukace kana suka juya zasu fita.
Cikin tsare girma Shatu tace.
"Mun gode, a gaida gida".
Gida zaiji sukace kana suka fita suka tafi.
Suma su Ummi wucewa sukayi yin al'wala.
Ana idar da salla kuwa aka fara hawan daba, hawan sarki dama duk sauran shagulgula na gidajen masarautun gargaji yayin wurin taron bikin salla.
MASARAUTAR Joɗa ta cika tayi maƙil da bani Adam.
Haka dai akayi taron lfy aka tashi lfy sai kuma gobe in Allah ya kai rai.
Washe garin ranar da sassafe.
Sheykh ya tafi asibitinshi.
Ko karyawa baiba.
Sai kusan sha É—aya ya dawo da alamun yunwa da gajiya tare dashi.
A falon ya zauna suna gaisawa da Ummi dan basu gaisaba ya tafi daga masallacin can ya wuce.
Ummi kuwa tasa Shatu ta kai mishi breakfast É—in shi da yanzu kam in yacima ya zama lunch ne.
Hibba kuwa na can ɗauki tana ƙenƙesa ado.
Cikin isa da ƙasaita Gimbiya Saudatu ta shigo tsakiyar falon babu ko sallama.
HaÉ—e fuska Sheykh yayi tare da cewa.
"Wannan banzan É—abi'a na arnatakun baya, dan ko arna yanzu suna cewa konkon, mutun kamar shanu ko mahaukaciya".
Cikin isa ta iso tsakiyar falon.
Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito falonshi.
Cikin shigar doguwar riga mai ruɓi biyu.
Kanta ta É—ago ta kalli Shatu kana ta kalleshi cikin yin dariyar mugunta tace.
"Eh kam tabbas tunda ka auro mahaukaciya dole kasan hali da É—abi'un mahaukata ai.
Zuwa gaba kaÉ—an kaima zaka fara ihu da kuka da sume-sume irin na wannan al'janar fulanin daji daka auro É—in".
Cikin tarin mamaki Ummi ta kalli Shatu ta kuma kalli Hibba da yanzu ta fito, cike da al'hinin ta yaya taji wannan batun ya fasa Masarautar JoÉ—a yes in dai Gimbiya Saudatu taji to ai shike nan kowa ma zaiji.
Shi kuwa Sheykh ba gane inda soki burutsunta ya nufaba yayi.
Ita kuwa cikin watsa musu kallon ku sakarkaru ne tace.
"Kuna mamakin ta ina naji, cewar ji shekaran jiya iwar haka dai wannan matar tashin tana yashe a sume da ido a wulkice tana ƙarkarwa farfaɗiya kamar mazari ne.
To ai Ni duk wanda yaci tuwo dani miya yasha.
Inada tawa a cikinku duk motsinku ina dashi a tafin hannuna.
Nan gaba kaɗan zamu samu riƙeƙƙiyar mahaukaciya a masarautar Joɗa".
Cikin tsuke fuskarsa yace.
"Yanzu ma ai muna da su mahauka ta kam, ke É—in me banbancin ki da zararrun".
Shiru yayi ganin yadda Shatu keyin taku a hankali cikin isa ta nufi gaban Gimbiya Saudatu.
Ummi da Hibba kuwa miƙewa tsaye sukayi.
Shi kuwa Sheykh gyara zamanshi yayi tare da ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya.
Ita kuwa Shatu a hankali ta isa gabanta.
Ido ta zuba mata tare da yi mata kallon tara saura kwata.
Cikin dakkeyar Muryar rashin tsoro tace.
"Toh *Bushiya* mai mugun baya, Bushiya mai bayan ƙayoyi masu kama da allurai, ki buɗe idonki da kyau ki kalleni Ni AYSHA ALIYU GARKUWA ba sa'ar yinki bace uwar mahassadan duniya, in kina cin ƙasa to tabbas ki kiyayi ta curi, ki bar min mijina ya sarara ki far masa rayuwa, ɗan shi ba sa'an yinki bane ki bar min mijina ya huta baya son ihun nan da kikeyi mishi, zan kuma iyan komai dan ganin na kauda dukkan abinda baya so."
Wani irin daɗi ne ya rufe zuciyar Ummi da Hibba Sheykh kuwa ƙafarshi kawai yake kaɗawa yana mai binta da wani irin kallo mai tarin ma'anoni kalmarta ta *Mijina* yake ji tana sa duk wani hudan gashin jikinsa na amsa amon kalmar yana ratsa jikinshi da zuciyarsa haka yasa bai san sanda wani yalwataccen murmushi ya subce mishiba, tabbas Shatu akwai ƙarfin hali.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu tsuru tai da ido.
Itako Aysha cikin karsashi tace.
"Na lura ke dabbace, sam bakya gane yarukan mgna na bani Adam, kinfi son sai an miki irin yarukanku na dabbobi.
Kina tsaye da farin yawu a bakinki kina zubda jini.
Yayinda wasu ke bayanki da jini a bakinsu suna fidda farin yawu.
Sokuwar rama mai tsami.
Ni nan da kike ganina da idona tar a buÉ—e na shigo Masarautar JoÉ—a, kada ki ganni haka Ni É—an hakine da zaki iya renawa amman tabbas zan tsole idanun magauta ruwanshi ya tsiyaye.
In kin san fullanci to.
*MIN MI KURORI CITTA NFAMÆŠA NHEYAH* NI ```DAKKEN YAJIN BORKONE INYI KAÆŠAN IN KUMA ISHI MUTUN```
Ki tsumayeni tabbas zanyi daka inyi tankaÉ—e inyi rairaya a masarautar JoÉ—a!.
Ke ko kallo baki isheni ba domin bata ke akeyi ba da manyan Magauta nakeyi.
Ja mugun bakinki ki fice min a gidana!".
Rab-Rab.
Jalal da Jamil dake da Jafar shigowa ne, suka tafa mata da hannu bibbiyu.
Hakama Hibba. Ummi kuwa ƙasa tayi da kanta.
Shi kuwa Sheykh ƙanƙance idonsa yayi yana kallonsu yana kaɗa ƙafa ya watsa idanunshi cikin na Gimbiya Saudatu yana mata kallon itama ta isheki.
Aunty Juwairiyya kuma da tun ɗazu tana bakin ƙofar shigowa da sauri ta juya ta koma Side ɗin ta.
Ya Jafar kuwa sai murmushi yake tare da dunÆ™ulawa Shatu hannunshi kamar hakaðŸ‘ðŸ»
Wani irin juyawa Gimbiya Saudatu tayi tare da jan al'kyabbar ta ta fita.
Har taje bakin ƙofa Shatu tace.
"Ki riƙe kalmar mahaukaciya tabbas zakiga mahaukata a masarautar Joɗa zasu baiyana bila'adadin."
Daga nan ta juya ta nufi Dinning area É—in babban falon.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu ta juya ta fita.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya sauƙe ƙafafunshi kana ya miƙa ya nufi falonshi.
Haka nan yaji murmushi na tsubce mishi.
Tabbas ya gamsu da ƙarfin halin Shatu da rashin tsoronta, sai dai yana jiye mata tuggun mutanen da bata san halinsu ba.
Yana shiga yaci abinci kana ya shiga yayi wonka.
Kana ya É—auki wayarsa.
Jalal, Jamil, Hibba, Ya Jafar, Shatu kuwa zama sukayi a falon cikin mamaki Ummi tace.
"To wacece yar leƙen asirin Gimbiya Saudatu a wannan sashin?
Ya akayi tasan abinda ya faru da Shatu?
Waya gaya mata?
Bayan in banda muyamu.
Ni Juwairiyya, Hibba, Jalal, Jamil, Jafar. Wanda shi baya mgna, ita kanta Shatu bata san meya faruba batasan ya akayi ba.
To waya fitar da wannan zancen a cikinmu?."
Cikin gsky da gsky duk suka ce wlh babu wanda suka taɗawa mgnar Hibba harda ƙollarta tace.
"Wlh ita ko Umaymah ma bata gayawa ba".
To lallai kam akwai buƙatar bincike a tsakanin mu."
Ummi ta faÉ—a tana mai cike da al'hinin abin.
Ita kuwa Shatu uhummm. Kawai ta iya cewa tayi shiru bata ce komaiba.
Haka dai suka tashi taron.
Sheykh kuwa, number Umaymah ya kira bayan sun gaisa ne yace.
"Uhumm Umaymah wai me kika sani ne ya faru da wannan yariyar shekaran jiya?".