← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 183

Sashe 14

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ta kama hanyar gidansu, tana gab da shiga gidane ta haÉ—u da É—an makotansu Iro cikin girmamawa tace.
"Ina wuni Ya iro".
Fuska cike da fara'a yace,
"A a lale marhabin da ƙanwarmu yar al'barka anyi hutukenan?".
Kai ta gyaÉ—a mishi sannu da hanya ya mata sannan ta wuce ya wuce.

A gindin bishiyar mangoro dake kofar gidansu gab da zaure ta hango Bappanta yana zaune bisa dakalin dake wurin yana al'wala, da sauri ta nufi in da yake fuska cike da jin daÉ—i.

Shima Bappa da sauri ya miƙe yana murmushi yake cewa.
"Maraba lale da Æ´ar al'barka."
Da sauri ta iso inda yake tana murmushi mai nuna tsantsar jin daÉ—inta tace.
"Oyoyo Bappa na, Alhamdulillah na sameka lfy, ya Ummey na da Innata?".
Dariya yayi tare da matsota yace.
"Duk muna lfy".
da sauri suka juyo ta cikin gida jin muryar yayunta suna cewa.
"Oh wato mu kam bakiyi kewarmu bama ko?".
Da sauri tayi gabansu cikin jin daÉ—i tace.
"Oyoyo Æ´an uwana Ya Gaini, nayi kewarku mana, musamman Ya GiÉ—i sarkin son girma".
Murmushi sukayi dukansu,
Seyo ne ya kalleta tare da cewa.
"Wallahi yanzuma mgnarki mukeyi da Ummey, har Junainah na cewa wai ai duk munfi sonki".
Dariyar jin daÉ—i tayi tare da cewa.
"Ayyah ƴar ƙanwaliya tawa mai kishidani".
Murmushi sukayi baki É—aya kana Lado ya kalleta tare da cewa.
"Shiga gida mu zamu wuce masallaci ne".
To tace kana ta nufi cikin gida tana cewa.
"Yauwa yaya GiÉ—i dan Allah a kawomin rake".
Kai ya gyaÉ—a mata kana suka wuce ita tayi cikin gida.

Tana shiga da fara'ar jin daÉ—i da É—an karfi ta buÉ—e murya tare da cewa.
"Assalamu alaikum, gani na dawo, ina Inna ina Ummey, Junainah ina kike?".
Ai kusan a tare suka fito gaba É—ayansu, wani irin tsalle Junainah ta buga tare da rugawa ta nufi kan yayar tata cikin ihu da É—aga sauti take cewa.
"Oyoyo Addana oyoyo".
Da sauri Ummey ta harateta tare da cewa.
"Ke Junainah magriba cefa, kike irin wannan ihu ke sam baki da nitsuwa".
Ita dai batama jitaba.
Da gudu ta faÉ—a jikin Aysha, itama Aysha wurgar da jakarta tayi ta ruggume yar uwarta.

Inna da Ummey kam ido suka zuba musu, suna masu jin daɗi irin soyayya da shaƙuwar dake tsakanin yaran nasu.

Dariya sukayi baki É—ayansu, cikin jin daÉ—i inna tace.
"To yanzu dai lokacin salla yayi ku shigo kuyi salla tukun sai ayita murna dan yau dai kam nasan kwanan zaune za'ayi".
Murmushi Shatu tayi tare da karasowa gabansu cikin ladabi ba biyayya tace.
"Inna ina wuni".
Fuska a sake tace.
"Lfy lau Alhamdulillah ya karatu".

"Alhamdulillah karatu dai mun samu É—an hutu."

"Masha ALLAH yayi kyau".
cewar Ummey
hannun Ummeyn ta kamo tare da cewa.
"Ummey ina wuni".
Murmushi tayi tare da shafa kekyawar fuskarta tace.
"Lfy lau Shatu muje muyi salla ko?".
Kanta ta É—an sosa tare da cewa.
"Ummey ni nayi sallana a mota".
Dariya Ummey tayi domin ta gano cewa Shatu na fashin salla,
Ita kuwa Junainah baki ta tura tare da cewa.
"To ba gashi ba, ba yanzu muka gama musuba ya GiÉ—i ba nace mishi nafi Addana son salla, tunda ni kullum sai nayi ita kuma wata rana sai tace a a ita tayi a makka ko kuma tace wai ai tayi kuma babu wanda zai ganta tanayin sallan".
Ummey ce ta.
Buge bakinta tare da cewa.
"To Aku uwar mgna maza wuce kiyi salla, babu wanda ke son jawabin ki".
Tura baki tayi kana ta wuce cikin É—akin nasu, tana cewa.
"Ai dama nasan kunfi sonta".
Ita kuwa Ummey harara ta watsawa Shatu tare da cewa.
"Ke kuma kada dai ki rinƙa kiyaye bakin wannan magananniyar".
Murmushi tayi ta bita kana ta É—auki buta ta shiga bayan gida dan gyara jikinta, sannan ta dawo.

Tana shiga ta samu Junainah ta idar da sallan,
Gefenta ta zauna, tare da jawo jakarta, sweet É—inta data seyo mata, ta kwaso ta fitar mata.
Ai kuwa tuni fushi ya ƙare, tazo ta raɓa jikin yayartata.

Ummey kuwa da Inna saida sukayi sallan isha, kafin suka, fito tsakar gida dan tuni hadarin nan ya watse sai iska mai sanyi daketa kaÉ—awa.

Bappa da su Ya Ladoma saida aka idar da sallan isha kafin suka dawo gida.

Gaba É—ayansu a tsakiyar gidan suka zauna bisa manyan taburmaii guda biyu mazan na kan É—aya matan na kan É—aya.

Abinci sukeci mai rai da lfy, tuwon faran ɗanyar shinkafa, da miyar ɗanyar kuɓewa data sha man shanu da tantakwashi, sai kifin banda sabi kifi na araha a wurinsu.

Sai kuma zazzafan kunun nono da yaji nono da zuma.

Sunaci suna ira ga hasken farin wata daya fito yayi ral ya haska ko ina na gidan.

Cikin jin daÉ—i, GiÉ—i yace.
"Shatu hutun mai tsawone ko gajere?".
Kunun nonon data kurɓa ta haɗiye kafin tace.
"Eh to Yaya GiÉ—i hutun sati uku ne muka samu".
Seyo ne ya amshi zancen da cewa.
"A hutun da É—an yawa".
Shi kuwa GiÉ—i dariyar mugunta yayi tare da cewa.
"Ai kuwa naji daÉ—i wlh sai kinyi kiwo kema kiji hazar da muke ji".
Bappa ne ya amshi zancen da cewa.
"GiÉ—i mugunta ba kyaufa, Wato kai wuya kakeso tasha".
dariyar ƙeta ya kumayi tare da cewa.
"Ai naga duk anfi kashe mata kuÉ—i kuma muke wahalar kiwo, makarantar da takeyi kawai duk shekara kusan million 1 takeci muko sai wuyar tsiya da muke ci".
Gaini ne yace.
"To ai kuma ita bata da shanu ko É—aya kaikuma garke biyu kakeda naka na kanka haka kuma muma".
Ladone ya É—anyi murmushi bayan ya haÉ—iye lomar da yasa a baki yace.
"Ato gaya mishi kam".
Ummey ce ta É—an kalli Shatu tare da cewa.
"Kici abinci ki dena shan ruwan kunu ba rike miki ciki zaiyiba".
Da sauri Junainah tace..
"A a Ummey ai Inna tana tasa an yanka zabbi zata gasa mana Adda karkici tuwo".
Dariya sukayi baki É—ayansu dan duk kowa yasan Junainah tsakaninta da.
Nama akwai ƙauna.

Haka dai sukaci gaba da hira da dariya,
Hatta makiyayan gidan nasu wanda ba yan gidan bane saida suka shigo akayi ta hira da dariya dasu.
Suna cikin hirar ne yaro yayi sallama cewa Ba'ana yana kiran Aysha, cikin sauri Aysha ta konta tare da lumshe idonta, ganin hakane yasa Ummey cewa yaron.
"Ayyah kaje kace mishi yayi hakuri AYSHA har tayi bacci, in ba matsala yaje sai gobe, in kuma da matsala a tada ita".
To yaron yace ya juya ya tafi.
Fitarshi bada daÉ—ewa ba ya dawo,
Yace,.
"Yace a barta tayi baccinta gobe da safe zaizo".
To sukace kana yaron ya fita ya tafi. Sukuwa sukaci gaba da hira.

Gashin zabbi mai kyau Inna tayi musu gashin da yaji haÉ—i, nan ta ware na maza ta basu kana ta ware nata da Ummey sannan ta bawa Aysha da Junainah, nan fa sukaci gaba da ci, suna hirarsu ta zumunci wanda ko yaushe haka suke duk daren kuma anan Bappa ke karantar dasu.

Bayan duk sun fara miƙewa da dare ya fara nisa, a hankali Bappa yace.
"Aysha kinyi baccine?".
Cikin sauri ta miƙe zaune daga konciyar da tayi kanta na bisa cinyar Ummey, a hankali tace.
"A a Bappa idona biyu".

Tashi zaune yayi tare da fuskantar ta, ganin haka yasa ta rarrafa a hankali ta iso gabanshi, cikin kulawa yace.
"Ya karatun naki?".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah Bappa karatu na tafiya yadda ya kamata".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Baki da matsalar komai dai ko?".
Da sauri tace.
"Babu matsalar komai Bappa na".

"Masha ALLAH haka nake son ji, Allah ya miki al'barka dake da sauran ƴan uwanki baki ɗaya. Allah ya miki zaɓi da miji na gari".
A hankali suka amsa da Amin Amin gaba É—ayansu.

Daga nan kuma yayi ta mata nasihar ta kama kanta,
Jin sanyi ya fara yawane yasa sukayi saida safe kowa ya nufi makoncinsa.

Yayinda a can cikin garima masu hira a dandali duk sun watse.

Al'walan konciya bacci sukayi kana suka shiga, É—akin Ummey da yake mai girma da faÉ—i an laileyeshi da siminti da leda carpet, kana ga jere da gadajenta biyu masu kyau,
Ita da Junainah suna kan babban gadon ita kuwa Ummey tana kan ƙaramin gadon.
Hira sukaci gaba da yi irin hira ta tsakanin uwa da Æ´arta, cikin sanyi tace.
"Aysha, kinji Hashimu É—an ArÉ—o ya rasu ko?".
Da sauri cikin razana AYSHA ta tashi zaune tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Ummey banjiba yaushe ya rasu meya sameshi?".
Ta jero tambayoyin a tare kana ga hawaye na kwaranya cikin sanyi Ummey tace.
"Kwanan ya rasu, yankan rago akayi mishi sai tsintar gawanshi akayi a burtali ana zaton Ɓachamawa ne suka kasheshi".
Cikin shessheƙan kuka tace.
"Allah sarki Ya Hashimu Allah ya jiƙanka da rahama yasa ka huta, Allah ya saka maka duk wanda ya kasheka Allah ya toni asirinshi."
Sai kuma ta konta tana kuka sosai saida tayi kamar 3 minute tana kuka kafin tace.
"Yanzu shike nan Ummey duk wanda zai soni ƙarshensa yankan rago?".
Cikin yin ƙasa da murya Ummey tace.
"Ba dukaba in sha Allah akwai wanda zai soki ya kuma rayu dake bisa lfy".
A hankali tace.
"Ummey wa zai soni a irin yadda kullum ya Ba'ana yake kara zama masafi mugu, wa zai tsira da tarkonshi?".
Da sauri Ummey tace.
"Wanda yake mai ƙare rayuwarsa a amɓaton Allah da kekyawar zuciya."
Kai kawai ta kife tana mai kukan rasuwar Yaya Hashimun ta, a haka dai sukayi ta hira har bacci ya sacesu.

A can cikin masarautar JoÉ—a kuwa.
Bayan anyi sallan ishane, Sheykh ya fito cikin shirinsa na tafiya, riga da wondon yaÉ—in wagambarine a jikinsa sai bakar alkyebbarsa dayasa kana sai hiraminshi fari da kuma bakin tarden dake saman kanshi.
Sai takalman sarautar da ya saka, suma farare kalar hiraminshi.
Jamil ne ke biye dashi a baya yana riƙe da ƴar madai-daiciyar jakar Hamman nasu, kana hannunshi ɗaya na riƙe da jakar System ɗinshi, shi kuwa Sheykh woyoyinsh ya zura a al'jihunshi.
Chapter 14 · 0% Book details