Sashe 75
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da tarin mamaki Umaymah da Ummi suka miƙe, dan abubuwan da suka faru da yanayin Shatu, ya tsaya musu a rai.
Shima Sheykh Jabeer miƙewa,
yayi kana suka jere suka fita.
Sai dai Shatu na É—an sassarfa.
Cike da mamakin wannan abun suka nufi Side É—in Gimbiya Saudatu.
A falonta suka sameta tana hakimce bisa kujerar ikonta,
ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana karkaɗa ƙafar cike da izza.
Ummi na gabansu suna bayanta Umaymah na bayansu.
Cikin rusunar da kai Jakadiyarsu ta durƙusa gefenta tare da cewa.
"Barka da safiya Gimbiya Saudatu, ga Sheykh Jabeer ya kawo miki da amaryarsa!".
Cike da izza ta ɗan kallesu sama da ƙasa, kana ta nuna musu gabanta.
Alamun su zauna, cikin sanyi Shatu ta rusuna tare da sunkuyar da kai ta zauna gabanta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo yayi mata, mai cike da ma'anoni,
gefen ta ya kalla inda wata kujerar ke kusa da tata komansu iri É—aya.
Taku yayi cike da ƙasaita ya isa gaban kujerar, kana ya juyo ya zauna kan kujerar.
Hakan yasa ya fuskanci Shatu da Umaymah.
zaman ƙasaita da isa yayi.
wani mugun kallo take binshi dashi har ya zauna.
Ita kuwa Shatu kanta a duƙe tana murzam ƴan yatsunta.
Umaymah ce ta ɗan taho zata zauna kusa da ita, a hankali ya jujjuyawa Umaymah kai, alamun. A a kada ta zauna a ƙasa.
gane manufarsa ne, yasa ta zauna bisa kujera.
Shiru kakejin falon, sai takun sawun hadimanta dake kawo ababen motsa baki, suna ajiyewa gaban Shatu.
Suna gama jerawa suka koma can gefen.
Jin shiru-shirun yayi yawane yasa Shatu É—an É—ago kwayar idanunta, ta kallesu.
A ranta take mgnar zuci.
"Ikon Allah, ohoho ni Shatu wannan wanne irin bahagon gidane, mai cike da sarƙaƙiya da tubkar baƙin zare,
To ko dai ita wannan É—in kurmace."
Muryar Gimbiya Saudatu ce ta ƙatse mata tunani ta,
cikin isa da izza ta kalli Sheykh Jabeer, kana ta juyo ta kalli Shatu, murya a daƙike tace.
"Bakiyi sa'an mijiba, yarinya duk da gashi kamar kinada nitsuwa".
Ido Shatu ta jujjuya cikin hular al'kyabbar jikinta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, ko ta kan mgnar ta bai biba,
sabida ai dama ya tsammaci, hakan
kai ta juyo ta kalli Umaymah cikin É—agawa tace.
"A buÉ—e min fuskar amaryar in ganta da kyau, inga wanne irin idone da ita".
Bata rufe bakintaba taji yana cewa.
"Baza'a buÉ—e ba!."
Murmushi Umaymah tayi sabida tsamar Sheykh Jabeer da Gimbiya Saudatu wani lokacin yadda kasan shi ubanta ne, haka yake mata mgna da yanke hukunci kai tsaye a karan kanta ma bare akan abinda ya shafeshi.
ita kuwa Shatu a hankali take juya ƙwayar idanunta, tana kallon sawun Gimbiya Saudatu.
cikin al'kyabbar ta ɗan juya idonta da kyau ta maidasu, kan kyawawan fararen sawun Sheykh, wanda suke tamkar ka taɓa jini yayi yo tsalle ya fito, sabida taushi da laushin fatar
Wanda duk mutun mai zama da al'wala da yawan karatun al'ƙur'ani tafin hannunshi da ƙafarshi sukanyi wani kala mai masifar kyau da ɗaukar hankali koda baƙin mutun ne sai fatar hannunshi dana ƙafarshi sunyi kyau na musamman, hakama kuma fatar jikinshi wannan shine baiyanennen darajar zama da al'wala da yawan ambaton Allah kenan.
Da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da buɗe su.
kan babbar yatsar kafarshi ta zubawa ido, sosai da sosai.
wani ɗan zane baƙi mai suffar tafiyar maciji ta gani.
sai dai bata samu ganinshi ras yadda take soba, shiyasa taketa zare ido,
shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya ɗan turo ƙafar damanshi gaba.
Dan ya gyara zaman É—ayan a kanta.
Hakanne ya bawa Shatu damar zubawa yatsun nashi ido, suna nan zara-zara alamun mutum ne mai matsakaici tsawo.
Ras zanen bindin maciciyar nan yake kan babbar yatsarshi.
har zuwa bisa rumfar ƙafar kamar zanen dayis,
cikin tarin mamaki da al'ajabi take bin zanen da idanunta.
har inda igiyar takalminshi ya tsare zanen.
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe a hankali.
sabida rashin ganin ƙarshen wannan zanen, da kuma inda ya nufa, da kuma ganin ya saman zanen yake.
Hankalinta kab ya tafi ga zanen shiyasa bata jin ta ƙaddamar da Gimbiya Saudatu ke zubawa ba.
Muryar ta taji da ɗan ƙarfi tana cewa.
"Bata da sunane? Ke me sunanki".
Ta É—ago kai da nufin yin mgna kenan sai kuma tayi shiru.
jin Umaymah na cewa.
"Sai kisa mata naki sunan, ba sai kiji namu ba".
A gyatsine ta kalli Umaymah kana, ta É—an matso bakin kujerar,
hannu tasa ta É—auki tupa cikin jerin Æ´aÆ´an itatuwan da aka jera a gaban Shatu.
miƙa wa Shatu tayi tare da cewa.
"Kici kada ki tafi bakici komaiba,".
A hankali tace.
"Alhamdulillah!". Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
"A ni ba'a zuwa sashina a tafi ba abinda akaci".
Hannu ta miƙa ta amshi tupan kana ta riƙe shi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer miƙewa tsaye yayi alamun tafiya hakane yasa.
Suma suka miƙa suka fita.
Daga nan kai tsaye Side É—in.
Baba Nasiru suka nufa.
A falo suka samu matarshi da yaranshi dama shi kanshi.
Bayan sun zaunane.
ya kallesu sama da ƙasa yace.
"Dama baku zauna ba, a hakama na ganku.
ba sai kun zauna ba".
Cikin sanyi ƴarshi Jamila ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
"Ayyah Baba ka barsu mu gaisa".
HaÉ—e fuskarshi yayi sabida yasan irin masifeffen son da Jamila keyiwa Jabeer lokuta da dama, takanyi ta kuka in taji abubuwan da mahaifinta yakeyi mishi.
shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya zauna ya harɗe ƙafa,
Jamila kuwa cikin nitsuwa ta gaidasu kana.
Ta kawo musu abin sha,
Ummanta ku ko kallo Bata ishesuba yadda itama bata lallesu ba.
Haka dai suka fita suka tafi.
gidan Baba Basiru kuwa suna shiga ya tashi ya bar musu wojen.
Daga nan suka shiga gidan Barrister Kamal
Baba Kamal kenan.
Yana ganinsu ya tashi ya ruggume Sheykh tare da cewa.
"Masha Allah, Alhamdulillah yau dai Allah ya nuna min É—ana da matarsa".
Zama sukayi bayan sun gaisane yayi musu addu'o'in al'khairi.
Daga gidanshi gidan Dr Aliyu sukaje,
wanda yake mutun mai mutunci da kamar Barrister Kamal.
Sosai suka jima a sashinsa,
yayi musu addu'o'in da sanya al'khairi da al'barka.
Daga nan kuma sai Sashin Mom tsakar gidan Abbanshi.
Maman Imran, ba yabo ba fallasa ta amsa musu.
Daga nan wurin Amryar Abbansu sukaje, wanda suka sameshi a can.
Daga nan sukaje gidan Ya Hashim da sauran Æ´an bappanunsu.
Gida na ƙarshe dai gidan Aunty Juwairiyya ne, can suka samu Hibba da Ya Jafar.
Bayan sun gaisane,
Umaymah ta ɗan matso kusa da ita cikin sauƙe numfashin gajiya tace.
"Ɗago kanki Shatu kinga nan ƙofar Aunty Juwairiyya ce, ga mijinta shine babban yayan Jabeer, kuma yanada matsalar ƙwoƙolwa.
Yanzu daga nan Side É—inkin zamu wuce, wanda yana nan kusa da nasun. Sai gefen nakun kuma nasu Jalal ne."
A hankali ta ɗago kanta ta kalli Ya Jafar, yana riƙe da hannun Jabeer yana karatun shi a hankali.
Cikin sanyi tace.
"Ina kwana yaya!".
KafaÉ—arta Umaymah ta dafa tare da cewa.
"Baya mgnar komai a duniya inba karatuba, sai dai yanajin komai kuma yana gane komai in an gaya mishi amman fa baya mgna kam in ba karatuba."
Cikin tsananin rauni da tausayawa,
idonta cike da ƙwalla tace.
"Allah sarki, Allah ya bashi lfy".
Karon forko kenan tunda suko fito dashi taji ya amsa addu'a duk da tarin addu'o'in da akayi ta musu sai yanzu taji yace.
"Amin ya Allah". Hakama Umaymah da Jakadiyarsu da Hibba sai dai duk ya riga su amsawa.
A hankali take É—an satan kallonshi a fakaice.
Hibba ce ta janye mata hankali da cewa.
"Aunty Shatu kin gaji kam. muje ki huta, gashi azahar ta kusa ma."
ÆŠan guntun murmushi tayi tare da cewa.
"Uhum".
Umaymah ce ta miƙe ita da Ummi kana sukace.
Taso mu tafi, yanzu Hibba zata cikaki dan zance."
Cikin murmushi Aunty Juwairiyya tace.
"Ayyah Umaymah ku bar mana ita mana".
Ummi ce tace.
"Lokacin sallafa ya ƙara to".
"Hakane kam". Juwairiyya tace tare da É—aukar Foodflaks dake kan dinning table, tabi bayansu tana cewa.
"Hibba É—auko sauran!".
To tace kana ta suggumi sauran tabi bayansu.
Nan suka bar Jabeer da Ya Jafar É—in.
A babban falon suka zauna.
Aunty Juwairiyya da Hibba suka ajiye Foodflaks É—in bisa Dinning table,
kana suka dawo tsakiyar falon.
Umaymah ce ta miƙe tare da kallon Shatu, tace.
"Taso mushiga ciki, kiga tsarin wurin naku".
Miƙewa tayi cikin alamun gajiya, domin zagaye masarautar Joɗa babban aikine mai zaman kanshi. Donma su sun saba, ita kuma bafulatanar dajine tafiya baya bamu tsoro.
Bayan Umaymah tabi, ta gefen Dinning area ta É—an ratsa da ita,
Suka shiga cikin kitchen, juyowa tayi ta kallesu Ita da Hibba,
"Nan shine babban kitchen É—in ki, dake babban falonki.
Shine wanda in kinada aiki mai yawa, kamar na salla ko azumi, ko zakiyi ki aikawa surakanki.
Hadimai zasu iya shigowa su tayaki."
cikin fahimta tace.
"Toh". Hibba ce ta ɗan ƙara so shigowa ciki tare da cewa.
"Kai wanga kitchen badai girmaba, gashi komai a tsare gonin kyau. Kalarsa green and white komai na ciki gwanin kyau".
Murmushi suka É—an yi kana, Umaymah ta juya dasu.
Daga nan cikin kitchen ɗin ta gefen dama akwai wata ƙofar da sai ka hau stpes huɗu.
A gefen ƙofarne wani datsetstsen Fridge mai girma yake kwance.
Haurawa sukayi kana Umaymah ta tura ƙofar ta shiga.
Store ne mai zaman kanshi.
akwai komai na buƙatar rayuwa, sai dai ba mai yawa bane.
Shatu ta É—an kalla tare da cewa.
"Ga kuma store ɗinki. Nan za'a ke aje miki duk wani abun buƙata".
Kai ta gyaÉ—a, kana suka fito.
Wata ƙofar daketa hannun hagu ta nuna mata suna buɗe wa suka fito.
Sai gasu bisa wata baranɗa mai girma, kana can ƙasan barandar fulawine da kuma pompona ke jere iya ganinka,
Daga sama kuma igiyoyin shanya ne da a ƙalla sun kai huɗu.
sai saman barandar kuwa, injin wanki ne.
Nan dai ta nuna mata komai na wurin kana suka dawo cikin gida.