← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 183

Sashe 104

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A lokacin ne kuma sunan jihar nan ya dawo Ɓadawaya sabida.
Nunawa duniya ba haka bane duniya Allah zai iya baka zai iya hanaka.
Masarautar Fulɓe kuma ta zama masarautar *JOƊA.*
Sabida sunan sarkin kenan.
Kuna ya zama adalin sarki mai son baƙi duk inda baƙo yazo zai wuce.
Sai Sarki JoÉ—a ya bashi wurin zama yace mushi JoÉ—a wato zauna ga wurin zama kayi kasuwanci kayi kiwo ki ciya ka ciyar kasha ka shayar."
Shiyasa Jihar Ɓadamaya tayi zarra da tarin ƙabilu sabida son baƙi da basu muhallin zama a wancan lokacin kawai fili za'a yanka a baka ka zauna in Kai baƙone

To babban É—an JoÉ—a shine Bubayero wato kakan LamiÉ—o.
Bayan JoÉ—a ya rasune Bubayero ya hau kan karagar mulki masarautar JoÉ—a.
Ahlin Gimbiya Falmata kuma suna yaɗuwa suma buri da kwaɗayin sarauta na jiƙa a ransu duk burinsu suga yadda sarauta zata dawo ɗakinsu.
To koda Bubayero zaiyi murabus ya bawa É—ansa Nuruddeen mulki sai ya aurawa É—ansa yar bappan shi jikar Madu É—anshi.
Sukayi aure aka naÉ—a Sarki Nuruddeen da matarsa yakura.
Bayan anyi aurene da shekara biyu.
Ya auro wata Æ´ar masarautar su Gimbiya Sumaye.
To itace tazo ta haifi LamiÉ—o.
Ita waccar bata taɓa haihuwa ba.
To shima LamiÉ—o sai ya auro yar masarautarsun Gimbiya Sumaye, wato Gimbiya Aminatu a matsayin matarsa ta biyu.
To Galadima da kike gani yanzu bappan LamiÉ—o ne É—an autan su marigayi sarki Nuruddeen.

To shi kuma LamiÉ—o da aka bashi mulki sai aka aura mishi yar zuriyar Gimbiya Falmata itace uwar gida.
Ta haifi Baba Basiru da Baba Nasiru da kuma Baba Kamal da kuma babban yayansu Marigayi Auwalu. Sai Dr Aliyu shi kuwa mamanshi daban itama ta rasu su biyu ta haifa da Gimbiya Surayyah.

To Mamansu Baba Nasiru.
Yanzu haka tana raye amman ta haukace babu mai shiga Side É—inta, sai LamiÉ—o da yaranta. Duk wanda yaje sai tace zatayi duka, ita da bakinta take bayanin Abbansu Sheykh da Gimbiya Aminatu da Gimbiya Aisha tayiwa asiri ya dawo kanta.

Galadima da yaga ya tsufane kuma baida É—a namiji da zai gajeshi shine.
Yacewa LamiÉ—o ya naÉ—an babban É—an shi Auwalu mijin Gimbiya Saudatu a matsayin Galadima.

To bayan ya naÉ—a shi da shekara biyu ne, ya rasu.
To sai ya naÉ—a Ya Jafar É—in nan da kike gani a matsayin Galadiman Masarautar JoÉ—a.
Lokacin lafiyarsa lau yadda kikaga Sheykh haka yake da ibada addini ilimi nitsuwa tausayi.

Kwananshi goma a kan mulkin washe gari za'a naÉ—a shi ne, ya dawo haka babu mgna sabida wani babban ibtila'i da tashin hankalin É—aya samemu.
Kuma a lokacin an kusa amishi aure sabida sarautar da za'a bashi.
To wannan shine babban mafarin hargitsi da kitimurmurar dake masarautar JoÉ—a a yanzu.
Dan ranar da Jafar ya zama haka akwai babbar masifar data fi wannan muni daya faru a masarautar JoÉ—a.
Shine abunda yayi masifar girgiza mutane.

Lokacin Sheykh yana saudia yana karatu a jami'atul Madina.
Hankalin Hajia Mama yayi masifar tashi tayi ta suma tana sakewa Umaymah kuwa da Sitti mutuwace kawai da basuyi ba, dan baƙin ciki da tashin hankalin ɗaya samemu.

To kuma tun daga nan sai duk magautan suka dena kiyayyarsu kansu Jafar da ƙannensa.
Koda Jabeer yayi karatunshi a can yayi digirinsa na biyu da PHD dinsa duk a can.
Wani sabon tashin hankalin da Jabeer ya dawo LamiÉ—o yabashi mulkin GARKUWAn FULANI, nanfa Magauta sukace zasu mutu.
Dan ma mulkin na gefen yaya mata aka bashi shine abin ya É—anyi sanyi.
To kuma ingiza gabar sunga É—awisun masarautar JoÉ—a tayiwa Jabeer abinda sai sarki takeyiwa.

To kinji lbrin a taƙaice sai a hankali zaki gane komai in kina bin komai a hankali."
Numfashi mai sanyi Shatu ta sauƙe tare da cewa.
"Ummi wacece Gimbiya Aisha?".
Da sauri Ummi tace.
"Baki santaba".
Da sauri Shatu tace.
"Toh ina take?".
"Bata nan". Ummi ta bata amsa a gajarce.
Da sauri Shatu tace.
"Ta rasu ne?".
Cikin zubda hawaye Ummi tace.
"Bamu san halin da take cikiba shine babban burin Sheykh a duniya, sanin inda take".
Cikin sanyi Shatu ta kauda waccar tambayar dan ko Ummi bata amsa mataba ita ta gane matsayin Gimbiya Aisha. Haka yasa a hankali tace.
"Allah ya baiyana ta. Ya cika mishi burinsa."
Amin Amin Ummi tace tana sharce hawaye.
Cikin nitsuwa Shatu tace.
"To Ummi mene kuma banbancin mulkin gefen yaya mata dana maza".

Cikin jin bacci tace.
"Da safe ki tambayi Hibba ko Jamil zasu gaya miki, yanzu jeki shiga dare yayi bacci nakeji".
Da haka tatashi taje ta shiga ta fahimci a duddunƙule Ummi ta bata lbrin Sarkin yanzu da matsalar dake faruwa.

Washe gari da safe, bayan sunci abinci.
Ummi ta miƙe dan taje tayi walaha, Hibba kuma ta tafi sashin Juwairiyya da tun jiya da safe bata sake shigowa ba.
Jamil ne ya shigo neman Jalal da sauri tace.
"Uhum yauwa Jamil zo mana".
To yace kana ya dawo ya zauna.
Cikin nitsuwa tace.
"Dan Allah in É—an tambayeka mana".
Jingina yayi da jikin kujera tare da cewa.
"To ba matsala Allah yasa na sani".
Wayarta ta ajiye kana tace.
"In sha Allah ka sanima.
Wai menene banbanci sarautar gefen Æ´aÆ´an Æ´aÆ´a mata, dana gefen Æ´aÆ´an Æ´aÆ´a maza".

Dariya yayi mai sauti tare da cewa.
"Uhumm kema kin shiga Masarautar Joɗa cikin kitimurmuran yanayi ko kin ratso cikin ahlin da ba'a sonmu, kin fara fuskantar ƙalubale ko".

Tashi yayi yaje ya sha ruwa kana ya dawo ya zauna ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Banbancin tsakanin sarautar gefen Æ´aÆ´an Æ´aÆ´a maza da gefen Æ´aÆ´an Æ´aÆ´a mata.
Shine kamar haka.
1 Galadima (must be a prince )
2 Chiroma (crown prince)first born to the king
3 Tafida ( most be a prince )
4 Santuraki (must be a prince )
5 Sarkin dawaki ( prince)
6 ÆŠan buram
7 ÆŠan isa
8 ÆŠan lawan
9 Durbi
10 Wambai
11 Turaki
12 ÆŠan maje
13 Yarima
14 ÆŠan iya
15 Majidadi.
Dan ɗagowa yayi ya kalleta tare da saƙe yatsunshi da yake naɗewa yana irga mata yace.
"Wannan duk royal family ne mostly biological sons din sarki ne wasu kuma jikokin sarki kuma kunne biyu sukeyi a rawunansu sabida su Æ´aÆ´an sarki ne ko kuma iyayensu Æ´aÆ´an sarki ne.
Kanta ta jinjina mishi alamun ta gamsu tana kuma ganewa.
Shi kuwa a nitse yaci ga da ce mata.
"Anan ake samin chief of staff da kuma senior councillor kamar galadima mostly shine senior councillor shine elders in royal bloodline ana samun galadima yapi sarki a shekaru kuma shi ake bama riqon gari in sarki bayanan.

Sannan duka anan sunayen dana irga miki da fari kowa zai iya yin sarki tunda daga É—an sarki sai jikokinsa na gegen Æ´aÆ´a maza, shiyasa su kunne biyu sukeyi a rawanunsu.

A hankali ya kalli Ummi data fito da Hijabi a jikinta ta zauna kusa da Shatu.
Tare da cewa.
"To kinji bayanin Æ´aÆ´an Æ´aÆ´a maza na sarki."
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"Na gane kuwa Ummi, yanzu gaya min na Æ´aÆ´an yaran sarki mata kuma inji".

Gyara zama Jamil yayi tare da cewa.
"To sukuma sarautar gefen yaya mata sune.

1 Madawaki
2 Garkuwa
3 Makama
4 Majidadi
4 Waziri
5 Matawalle
6 Sarkin yaki
7 Magayaki
8 Jarma
9 Talba
10 Shatima
11 Ubandoma
12 ÆŠan kadai
13 Magajin gari
14 ÆŠan masani
15 Barma.
Ɗan sauƙe numfashi yayi tare da ci gaba da cewa.
All of these hakimai ne wanda sukeyin kunne daya a rawunansu.
Kuma wasu a cikinsu jikokin sarki ne ta bangaren mamansu, mum dinsu ce yar sarki kamar dai mu a Masarautar su Sitti ko za'a bamu mulki iya waÉ—annan za'a bamu kinga baza suyi kunne biyu ba shiyasa suke kunne daya amma suma hakimai ne manya kuma yan majalissar sarki also akwai kin makers a cikinsu.
Sai dai su cikin jerinsu babu wanda zai gaji sarautar sarki kamar dai mu yanzu bazamu gaji Jadda ba da masarautar gargajiyace sai dai da yake nasu na musulcine, in Kuma a masarautar Joɗa ne sunayen da na ƙirga miki na forko cikinsu za'a iya bamu, domin yanzu GARKUWA da aka bawa Hamma Jabeer matsayinsa yafi ƙarfin hakan shiyasa Magauta basu damuba."

Ya ƙarishe mgnar da cewa kin gane ko Aunty Shatu,
Kinga shiyasa da aka bawa Ya Jafar Galadima cikin kwana goma aka sabauta manashi.
Ana tsoron kada tarihin Sarki Bala da mahaifinshi Madu É—an Sarki Sule ya maimaita kanshi a kan Æ´aÆ´an É—akinmu.
Shiyasa da aka bawa Hamma Jabeer Garkuwa mu bamu soba.
To sauƙin abin ma ɗaya ne da suga sarautar gefen ƴaƴan ƴaƴa mata aka bashi duk da shi jikan ɗan ɗan ɗansa namiji ne".

Ajiyan numfashin tayi kana a hankali tasa hannunta ta tallaɓe habarta, cikin alamun nisan zango na tunani da nazari.
Chapter 104 · 0% Book details