← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 183

Sashe 165

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falon ta dawo dai-dai lokacin kuma Sara ta shigo.
Gefe ta zauna jin Ummi na cewa Jamil.
"Gobe in Allah ya kaimu zaka kaimu, gidan hajia Kubra aminiyar Umaymah mu dubota da jiki nida Juwairiyya".
Kai ya gyaÉ—a alamar "To".
Da sauri Shatu ta kalli Ummi cikin zumuÉ—in son fita tace.
"Yauwa Ummi nima zanje".
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Eh ki tambayi mijinki in ya barki sai muje".
Kai ta É—an kauda tare da cewa.
"Kai dai Ummi sai na wani tambayeshi ai bazaiyi faÉ—aba tunda aiken Umaymah ne".
Da sauri Ummi ta jujjuya kai tare da cewa.
"A a badani za'ayi hakabs kam gsky ki dai tambaya in ya amince kinje in ya hana ki haƙura muje Salim alim".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Toh zan gwada Allah yasa ya barni".
Amin Amin sukace.
Kana Ummi ta É—an kalli Sara dake takure a gefe cikin kula tace.
"Saratu ya dai zazzaɓin ne?".
Cikin rawan sanyi ta gyaÉ—a kai.
Shatu ce ta kalleta cike da kulawa tace.
"Allah sarki sannu Sara kinsha mgni kuwa?".
Cikin rawan murya irin na mai fama da fitinenne masassaran cizon sauro tace.
"Naje asibitin mu na cikin masarautar JoÉ—a an min allurai, to kuma duk jikina rawa yakeyi.
Shine nace bari in zo in gaya muku, bazan iya zuwa muyi girkikiba.
Amman naje na samu Huwaila zata zo ta tayaku".
Cikin tausayawa Shatu tace.
"Ba komai Sara Allah ya baki lfy je ki kwanta".
Cikin kulawa Ummi tace.
"Allah ya sauwaƙa ko kada kice zakizo gobema Huwailan zata ke zuwa tana tayamu sai kinji sauki sosai."
To tace kana ta miƙa ta tafi.

Huwaila É—ayace daga cikin hadiman Sashin Aunty Juwairiyya wacce asalinta hadimar Hajia Mama ce.
Kuma har gobe a sashin Hajia Mama take kwana.
Ita da gidan Aunty Juwairiyya sai in zatayi girki tana gamawa take tafiya.
Sai Indo ita kuma a sashin Aunty Juwairiyya take, kuma asalinta daga masarautarsu Sitti aka kawota da ita.

Huwaila itace idon Hajia Mama a sashin Yan Jafar, shiyasa duk motsinsu ta sani sabida itace yar rahoto ko lokacin ciwon Shatu taji Aunty Juwairiyya na Umaymah a wayene daga nan taje tana fesawa Hajia Mama, dai-dai lokacin kuma yar rahoton gefen Gimbiya Saudatu na jinsu shiyasa mgnar ta isa ga Gimbiya Saudatu.

Su kuwa nan sukaci gaba da hirarsu.

Yau Sheykh bai dawo da wuriba sai ƙarfe goma na dare ya dawo.
Ba kowa a babban falon haka yasa ya rufe ƙofar.
Kana ya wuce Side ɗinsa jiki na karkarwa sabida masifeffen zazzaɓin daya zame mishi abokin rayuwa in dare yayi tun randa ya kusanci Shatu na forko yau kusan mako biyu kenan.
Sosai zazzaɓin ya shiga jikinsa sabida har ya ɗan faɗa.

Jiki na rawa ya É—an rage kayan jikinshi,
a daddafe yayi al'wala kana yazo ya kwanta.

Haka ya kwana da masifeffen zazzaɓin ya dai sa a ransa gobe zaije yabinciki lfyarsa.

Washe gari da safe.
Bayan sun gama aiki.

Ummi ta kalli Huwaila cikin kula kamar yadda ta saba da Sara tace.
"Yauwa ga naki tafi dashi kije ki huta sai anjima kizo muyi na dare dan zamu fita anguwa yau É—in".
Cikin wani irin kallon ƙasa-ƙasa ta kalli Ummi tare da cewa.
"To sai kun dawo".
Tana faÉ—in haka ta fita.

Tana fita ba jimawa su Jalal suka shigo.

Dinning area suka wuce kai tsaye.
Dai-dai lokacin Shatu ma ta fito cikin shigar doguwar riga mai masifar kyau da taushi sai ƙamshi take bazawa.

Gefen Ummi ta zauna kana ta kalli Jalal dake cewa.
"Adda Shatu Hibba ta kiranki bakya É—agawa".
Kai ta É—an juyo ta kalleshi tare da cewa.
"Fushi nayi da ita ai".
Murmushi sukayi baki É—ayansu.
Ita kuwa Shatu ido ta zubawa kular soyayyan Arish É—in da Ummi ta buÉ—e.
da sauri ta rufe idonta cikin sanyi tace.
"Ummi wannanfa waya kawo mana shi?".
Jamil ne ya amshi zancen da cewa.
"Wa kuma zai kawo mana tunda duk wanda ya kawo korarsa da abinsa kikeyi".
Cike da mamaki da tsoro ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi waya kawo mana wannan?".
Dafe kai Ummi tayi tare da cewa.
"Babu wanda ya kawo mana shi Shatu.
A nan mukayi girkin nida Huwaila".
Shiru Shatu tayi tare da jan dogon numfashi kana tace.
"Ohooooooh Allah sarki ba laifi Ummi rufe kular".
Cike da mamiki suka haÉ—a baki wurin cewa "Meyasa?".
Miƙewa tsaye tayi tare da tattara kulolin duk tayi cikin kitchen dasu tana mgnar zuciya.
"Yah ilahi ya mujibadda'awati meyasa? Me mukayiwa Aunty Juwairiyya?".
Ajiye abincin tayi gefe.
A take ta fara kiciniyar yi musu wani girkin.

Su kuwa a Dinning area da ido suka rakata.
A hankali Ummi ta biyo bayanta.
Ganin tana jajjaga kayan miya ne, yasa Ummi matsowa kusa da ita kana tace.
"Shatu meyasa zargina kikeyi ne nima É—in?".
Cikin sauri tace.
"A a Ummi har abadan bazan zargeki ba.
Amman naga abinda nake gani a abincin Hajia Mama da Aunty Juwairiyya ko na wasu gidajen in an kawo mana.
Ummi akwai mgni a ciki.
Ban zargekiba Amman zargina ya ƙara ƙarfi kan Aunty Juwairiyya duk da kareta da wonketa da kikeyi da nunamin ita yar uwarsuce.
Tunda kinga dai yar aikinta ce tazo ta tayaki aiki mukaga abin nan"
Wani irin dogon nazari da tunani Ummi ta faÉ—a can kuma sai ta nisa tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil.
Shatu anya kuwa matsalar nan Juwairiyya tasan da ita, anya ba zagon ƙasa akeyi mata ba ita kanta da mijinta da ƴaƴan taba".
Da sauri ta juyo ta kalli Ummin tare da cewa.
"To Ummi ina dai Huwaila yar aikinta ne?".
Da sauri ta gyaÉ—a kai tare da cewa.
"Allah sarki Juwairiyya ashe bamu saniba magautan sun samu damar tura wakilai sashinki, sunaci gaba da rarakarmu".
Cikin sanyi Shatu tace.
"Ummi me kike nufi?".
Cikin sanyi da zubda hawaye tace.
"Juwairiyya tasha yin kuka tana rantse min da abunda zai kasheta bata san me kike gani a abincin taba.
Tace min Ummi inrasa wanda zan cutar sai Æ´an uwana.
Shatu shiyasa Juwairiyya tayi fushi ta dena zuwa sashinki.
Sai yanzu na tuno asali Huwaila hadimar Hajia Mama ce, daga baya ta bawa Juwairiyya ita wai aiyukanta sunyi mata yawa".
Wani irin ajiyan zuciya Shatu ta sabƙe tare da cewa.
"Uhummm makashinka taburmanka, Ummi ko dai har yanzu baki yarda da wacece Hajia Mama ba, ko baku cemin ba ita mahaifiyar Yah Sheykh ba na sani ba ita ta haifeshi ba kuma nasan kuma kun san ita majirace, sai dai bansan dalilinku na zuba mata ido kuka meda kanku baku saniba, wata ƙil ƙofar rago zakuyi mata."
Sai kuma ta juyo taci gaba da aikinta tare da cewa.
"Kwantar da hankalinki Ummi barni da ita ai nida aita kar tasan kar.
Jeki zauna bari in tafasa mana ko indomei".
To Ummi tace kana ta fita.

Ita kuwa Shatu cikin hanzarin ta dafa musu indomei.
Kana ta kai musu.
Tana zuzzuba musu ne ta kalli Ummi tare da cewa.
"Yah Sheykh fa wanne abinci aka kai mishi?".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"A a shi Gimbiya Aminatu ce ta aiko mishi nashi karin kumallon.
Nama kai na ajiye mishi a falonshi.

Kai ta gyaÉ—a cikin gamsuwa kana sukaci gaba da cin indomein.

Bayan sun gamane suka tashi.
Jamil ne ya É—an kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi ku shirya mu tafi gidan Hajia Kubra ko, dan da yamma inada inda zan je".
To Ummi tace kana ta miƙe ta nufi ɗakinta, shi kuwa Jamil fita yayi ya nufi Part ɗin Yah Jafar dan ya cewa Aunty Juwairiyya ta shirya su tafi.
Jalal kuwa Part É—in Affan ya nufa.
A can ya samu Imran Sulaiman.

Itama Shatu kai tsaye É—akinta ta wuce.
Bathroom ta shiga dan sake yin wanka.

Shi kuwa Sheykh kasan cewar zazzaɓi na yawan addabarsa da dare.
Shiyasa bai samu isasshen bacci ba.
Kasan cewar yau asabar bazai je asibitiba dan yanada zaunanan likita dake zuwa asabar da Lahadi.
Shiyasa tunda ya dawo Masallaci ya kwanta yayi bacci sabida zazzaɓin ana kiran sallan asuba zai sakeshi.
So sai ƙarfe tara ya tashi daga baccin.
Jinshi garau yasashi shiga Bathroom.
Wanka ya fesa mai rai da lfya.
Kana ya fito ya murje jikinsa da OudKareem ɗinsa mai sasayyan ƙamshi.

Wata tattausar jallabiya royal blue ya sake mai ɗan karen taushi da sulɓi ya ɗaura kan boxes ɗin dake jikinshi fara ƙal irin mai taushi nan mai botura biyu a gaba.
Jallabiyar kuma hannunta guntaye ne, farin hular taɓa kaji hadisi ya murza a kanshi.
Turare ya ƙara fesawa kana ya ɗauki system ɗin shi ya fito falonshi.

Ganin tray'n dake kan stoll É—in dake tsakiyar falon ne ya gane, cewa Gimbiya Aminatu ce ta turo mishi breakfast haka yasa, yazo ya zauna bisa kujerar 2 str da stoll É—in ke kusa dashi.
kasan cewar stoll ɗin nada ɗan faɗi da tutu yasa, ya miƙa ƙafafunshi gefen tray'n sabida ba yanzu zaici abincinba.

Wani É—an aiki ya farayi a system É—inshin.

A can ɗaƙin Aysha kuwa.
A hankali take fesa turaren a jikinta.
Tayi É—an karen kyau cikin wata doguwar rigar Getzner mai masifae kyau,
rigar tayi cin da jikinta color Getzner Sky blue ne mai masifar kyau kana sai kolliyar pent work pink, green, red, da yellow akayi kwalliyar tamkar zanen ɗawisu, ƙasa duk akayishi kamar zanen ƙirjin ɗawisu saman kuma kamar irin ɗaziwisu ya ɗaga fikafikansa nan.
Tayi É—aurin É—an kwalintagwanin burgewa.
Gyalenta pink color hakama takalmita,
Cover'n wayarta ta sauya tasa shima pink.

Sosai tayi kyau rigar tayi cib-cib da jikinta sai dai wuyan rigar irin mai faÉ—in nanne.
Chapter 165 · 0% Book details