← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 183

Sashe 64

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa Shatu Junaidun Junainah ta kalla lokacin da aka dawo dashi daga É—akin tiyata,
Inda aka É—inke mishi inda aka sareshi.
Cikin murmushin yace. "Adda Shatu zamu kwana ko?".
Murmushin jin daÉ—i tayi tare da cewa.
"A a Junaidun yanzuma zan tafi, kasan Ummey ba lfy, amman jibi ma zanzo gobe su ya Salmanu zasu zo, yanzu dai hankalinmu ya konta tunda kun samu kulawar likitocin yanzu sai matsalar abinci".
Cikin sanyi Sumaye matar marigayi Sarkin bakansu, tace.
"La abinci kam bamu da matsalarshi, tako ina zakiga musulmai na dafo abinci suna kawo mana sadaka, harda kayan zaƙi da kuɗi wasu ke bamu".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah yau kam mutanen Rugar Bani zasuji lbri mai daÉ—i".
Cikin kula tace.
"Toni yanzu zan tafi in Sha Allah gobe akwai masu zuwa, Allah ya baku lfy".
Ta faÉ—i tana kallon sauran mutanen nasu.
Haka Rafi'a ma tayi musu fatan lfy kana suka fita tare.
Adaidaita suka shiga, saida ya kai Shatu tasha kafin.
Ya wuce da Rafi'a school É—in su.

A can wurinsu LamiÉ—o kuwa ganin lokacin sallan la'asar yayine yasa Jabeer cewa, suyi salla a masallacin asibitin kafin su tafi.
Haka kuwa akayi, sai gashi masallaci ya cika maƙil da bani adam,
saida suka idarne kana suka kama hanyar tafiya garin Rugar Bani.

A cikin motocin kuwa kowa da abinda yakeyi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer tsuratul Khaf yake karantawa a hankali.
Hakama LamiÉ—o.

Su Jalal kuwa kowa na ruggume da waya.
Haroon ma waya yakeyi da Umaymah tana tambayarshi sun isane.
Nan yake gaya mata inda suke da abinda sukayi.

A cikin Rugar Bani kuwa, kamar ko wacce ranar jumma'a yauma hakane.
Tunda aka taso sallan jumma'a suka dawo tsakar garinsu suka zauna suna ƙara jadda mitin ɗin su na ɗaukar fansa.
Zuwa yanzu garin yana amsar baƙoncin Fulanin da suka gaiyata tako wani sashi na Afirka. Sunata shirye-shiryen su.

Suna cikin masallaci suna sallan la'asar ne suka rinƙa jiyo, shigowar motoci cikin Rugarsu kamar bazasu ƙare ba.

Cikin nitsuwa sukaci gaba da sallan su.

Su LamiÉ—o kuwa suna shiga garin ganin tsit kuma alamun ana salla, sai yace su tsagaita gudun.

Jabeer kuwa zuwa yanzu tuni zuciyarshi ta fara luguden dukan ƙirjinshi ya rasa wannan abu na menene?
Yanzu wannan karo na huÉ—u kenan yana jin wannan abun a rayuwarsa, ya kuma gwada kanshi yaga bashi da BP dan sani BP nayin hakane ya sashi godawa.

A jere a jere sukayi parking motocinsu cikin nitsuwa,
Dogarai da fadawa suka fito suka zagaya motocin.

Bayan sun idar da salla sunyi addu'o'insu ne kana suka fito.
Gani fadawa da dogarai ma kaÉ—ai ya ganar dasu waye yazo.
Dan haka cikin karrama da mutun-tawa ArÉ—o Bani ya nufi inda suke.
Sosai dogarai sukayi mamakin yadda wannan karon kuma yakeyi kamar ya haɗiyesu dan farin cikin zuwansu saɓanin wancan karon da yayi ta aunawa Lamiɗo boma-boman baƙaƙen maganganu.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli matasan tare da cewa.
"Maza ku shiga cikin gidan ku fito da dardumai da kilisai kuzo ki shimfiÉ—a.
Ina sarkin kiÉ—a maza a fito da gangaguna a fara sanarwa.
Mabusa ku fito."

Ai kuwa cikin abinda bai gaza 25 minutes ba aka gama shirya komai.
Tuni mutane sun cika sunyi maƙil ko ina ya cika da bani adam.
KiÉ—e-kiÉ—en da bushe-bushen sarewa da al'gaita kuwa tuni ya cika illahirin garin tako ina mutane ke shigowa.

Ba'ana da tun jiya yake cikin É—akin dodon tsafinsu Bonon.
Jin al'gaita ShaÉ—i ne, ya sashi fitowa bayan ya gama shafe magunguna.
Dama yayi zaton wannan hegen mai jajayen kunnuwan zaizo shiyasa tun jiya ya shiga É—akin sirri dan a dafashi da kyau.

Jinsu ne yasa ya fito dashi da tawagarsa suka nufi Rugar Bani.

Lamiɗo kuwa da tawagarsa a hankali cikin ƙasaita da kwarjini suke taku har i zuwa cikin rumfar karan da aka malale musu kujeru da kilisai.

Bayan sun zaunane duk dattawan wurin sukazo suka gaida LamiÉ—o da tawagarsa.
Jabeer kuwa ji yake tamkar ya kira Sojoji su zo su zazzane mishi mutanen garin gaba É—ayansu ko zaiji ya huce da abinda sukayi mishi.
Sam baya son ganin fuskokinsu, ga toshe mishi kunne da sukayi da wannan bushe-bushen sarewa.
Ga bugun zuciyarshin dake neman zautar dashi.
Allah ya sani baya son ganin ko ƙasar garinne.

Cikin kula da nitsuwa da kamala Bappa ya kalli Jabeer É—in tare da cewa.
"Yaro ya ƙarfin jikin naka".
Ba tare daya É—ago kanshiba ya amsa, sabida jin muryar tanada kamala.
A hankali yace.
"Alhamdulillah".
Gaba ɗayansu suna farin cikin ganin Jabeer yazo cikin ƙoshin lfy.
Sunyi masifar mamaki ganinshi garau ya worke cikin mako É—aya tak.
Wannane ya ƙara sawa Ya Salmanu wani farin ciki na ban mamaki.

A hankali Bappa yace.
"Masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi".
Idonshi ya É—an É—ago ya kalleshi, haka nan yaji dottijon ya cika mishi ido a hankali yace.
"Amin ya Allah".
Bukar ne ya É—an kalleshi tare da cewa.
"Yanzu yaron nan kaine? Ka sake zuwa garin nan lallai baka son ranka".
A daƙile Jabeer yace.
"Inuwa tace".
Galadima ne ya É—an kalleshi tare da mishi alamun kada yayi mgna.
Kwaffa yayi tare da murtuke fuska.

A hankali su ArÉ—o bani suka koma wurin zamansu.
Kana Barmuji ya fara sanarwan ana son ganin Ba'ana a tsakiyar fili.

Wannan abu shine na forko a tarihin shi a nemeshi yazo tsakiyar fili dan a rama gasar da yayi.
Haka yasa cikin karsashi da buɗa ƙwanji yayi wani irin tsalle ya faɗo tsakiyar taron.
Juyi ya farayi da ihu da É—aga hannunshi sama, saida yayi kusan sau goma kafin yacewa Barmuji.
"Ka gayawa yan kallo in dai an cini gasa zan tafi in bar ƙasar nan, zan koma ƙasar Cameroon nida ƙasar nan sai dai ziyara,
Dan ba'a yin jarumai biyu a gari É—aya kamar yadda ba'a sarakuna biyu a gari É—aya."
Wani irin ihu da shewa gaba É—aya mutanen suka ruÉ—e dashi lokacin da Barmuji ya sanar da ikirarin Ba'ana.

Kana dattawan garin kuma kowa da abinda ke cikin ransa Arɗo Bani dasu Bappa kamar su haɗiye haƙorinsu dan daɗi.

Arɗo Bani ne ya ronƙofo kusa da Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku yace.
"Allah rene, bisimilla GARKUWA ya fito fage shi ake jira."
Kai ya gyaÉ—a mushi kana ya juyo ya kalli gefen damanshi inda Jabeer ke zaune cikin shigarsa ta al'farma, yayi masifar kyau, yana zaune cikin kamala sai lips É—inshi ke É—an motsawa a hankali alamun tasbihi yakeyi.
Cikin yanayi girma da bada umarni da tsare fuska LamiÉ—o yace.
"Jabeer kai ake jira tashi kaje muyi abinda ya kawomu."
Fuskarshi ya tsuke tare da lumshe idonshi, muryar Galadima da yajune yasashi buÉ—e idonshi.
Shi kuwa Galadima hannu ya miƙa ya kamo hannun Jabeer, tare da fara ja alamun zai miƙar dashi tsaye.
Cikin mamaki Jabeer ya zubawa tsohon ido wanda yake Bappa ne ga Lamiɗo, in banda ƙarfin hali inashi ina iya ɗaga Jabeer.
Muryar LamiÉ—o yaji yana kuma cewa.
"Jabeer DAN ALLAH KA TASHI".
Tsaki ya ɗan ja kana ya yunƙura ya miƙa a hankali.
Cikin jin daÉ—i Galadima ya kama hannunshi yaja suka fara taku, zuwa cikin taron.
A hankali yake bin bayan Galadima kana fadawa na biye dasu.
Al'kyabbar shi ya É—an gyara mahaÉ—inta.

Suna isa tsakiyar taron. Mabusa da makaÉ—a duk suka kaceme wurin da bushe-bushen sarewa da al'gaita kana da kaÉ—e-kaÉ—en.

Barmuji ne ya matso bayanshi da alamun zai cire mishi Al'kyabbar shi.
Da sauri Barmuji ya dakata sabida ganin wani irin lallo da Jabeer ya watsa mishi cikin tabbatarwa yace.
"Kada ka sake gangancin ciremin suturar da Allah yayi min har abadan. In kuwa ka gwada tabbas zakaji yadda raÉ—aÉ—in marin tafin hannuna yake, in kunnenka ya kuramce ansan kuramtane yasa bazakaji gargaÉ—i da kashedi na ba!".
Ya ƙarishe mgnar da tafasar zuciya,
cikin tsuma Barmuji ya rusuna tare da cewa.
"Duk da dokar gasa ce, anyi maka wannan lamunin tunda kaine mai duka ba kai za'a dakaba".
Ba'ana kuwa wani murmushi jin daɗi yayi sabida yasan yin duka da ƙatuwar riga haka, zai takurashi bazai samu damar zage ƙarfin shi ya zabga mishi bulaliyar ba.
(Allah sarki Ba'ana bai san zafin hannun Sheykh bane.
Sarkin Shaɗi ne, ya miƙe tsaye tare da tanɗun shantun da a ciki suka zuro bulalin nasu.
Ya nufi wurinsu Jabeer yana zuwa.
Yasa hannunshi ya zaro bulala ɗaya daga cikin bulalin ya miƙa mishi.
Hannun yasa ya amshi bulalar.
Kana ya gyara al'kyabbar jikinshi.
Shi kuwa ba'ana gabanshi ya matso ya tsaya ya buɗa sawunshi, kana, yasa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙugunshi, ya buɗa ƙwanjinshi da kyau.

Sheykh kuwa ƙasar garin ya zubawa ido, yana tuno irin zafi da ƙunar sashi cire kayanshi da sukayi satin daya gabata, yana tuna raɗaɗin da zuciyarsa ta masa a wannan lokacin.
Busar sarewa da akayi azaban ƙarfi ne, tabbacin an bada dama a farane.
Yasa Jabeer gyara riƙon da yayiwa bulalar, yana maiji cikin ransa da jikinsa zai rama dukan azaba da wannan ya mishi.
Yanajin zai ramane kuma dan tsorotar dashi kan sake dukan wani.
Yasani in sha Allah daga kanshi baza'a sake wannan gasar daba adadin bane, yayi niyar yin ramuwar ne dan tare wannan ɓarakar zai ramane ko zai samu ya huce tsanar da yayi mutanen garin, sabida kasan cewarsu Musulmai ƴan uwansa baya son yayi musu irin wannan tsabar lokacin ɗaya fushinsa na ranar ya dawo.
Shiyasa ya murza yatsunshi da kyau tare da matsawa gefe kaÉ—an, Rumtse bubalar yayi a tafin hannunsa da kyau, kana É—agata tare kuma da cewa Bismillah, ya fara da sunan Allah kana ya É—aura da fara karanto ayatul shifa sannan ya zabgawa Ba'ana ita a tsakiyar bayanshi.

Gaba É—aya hankali da idon kowa bisa fuskar ba'ana yake.
Shi kuwa ba'ana wani irin murmushi yayi tare da kallon gefe da gefenshi kana, yayi fito alamun babu wani abu da yaji dai yaji tsikar jikinshi yana tashi yar-yar.

Arɗo Bani da sauran dattawan kuwa har ji sukeyi tamkar su kamo hannun Jabeer suyi ta zabgar Ba'ana babu ƙaƙƙautawa.
Chapter 64 · 0% Book details