← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 183

Sashe 173

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi takumayi kana tace
"Ai bako mai bazata sani ciwon jiki ba ai batada nauyi".
TafaÉ—a tana shigewa bathroom rike da hijab a hannunta.

Tana shiga ta rataye hijab ɗin kana ta tuɓe kayan jikin ta ruwa ta cika cikin bath tashige cikinm
Kana ta É—auki soso da sabulunta mai matukar kamshi tashiga wanke lungu da sako najikin ta.
Tana gamawa tajanyo towel taÉ—aura a kirjin ta
Kana taÉ—au hijab É—in data tashigo dashi tazura sannan tafito,
Lokacin har bacci yafara É—aukar Aunty Rahama sai dai tana É—an jiyo motsin ta sama-sama kasan cewar baccin nata baiyi nisaba.

Gaban mirror tazauna batare da tacire hijab É—in ba tashafa mai kana tamurza humra ta kowani lungu da sako najikin ta,
Tamike taje tabuÉ—e wardrobe wata rigar bacci mai santsi kalar pick mai siririn hannu da gidan bra taciro, taÉ—aki pant Shima kalar rigar,
Bathroom takoma tasaka kayan kana ta maida hijab É—in ganin rigar da kaÉ—an ya shige guiwar ta.
A hankali ta fito,
Tazauna bakin gadon ta gaban Isham wacce tuni ta matso bakin gadon. pillow ta gyara tare da kwan ciya ta kasan kusa da Ishma.
Matsawa tayi taɗan daɗa gyara kwan ciyar ta dan tayi baki-bakin gadon da yawa taɗanyi baya da hannunta tana gyara hijabin jikinta, nan hannun ta yaɗan bigi ƙafar Aunty Rahma,
Ita kuwa Aunty Rahma da baccin nata baiyi wani nisaba, buÉ—e idanu tayi zatonta ma Ishma ce uwar birgimar yakawota kusa da isa da É—an sauri tamike dan ta tarota kada tafaÉ—i.
Ido taware cike da mamakin ganin Shatu ce kwance a gun,mussuke Ido tayi cikin muryar bacci tace
"Ke Aysha me kike jira Anan da Baki tafi É—akin mijin kiba jika kwanta Anan?".

Gyara kwanciya tayi kana tace
"Aunty Rahma anan zan kwana kusa da Ishma na".
Ido Rahma taÉ—a waro tace.
"A'a Aysha tashi maza kitafi É—akin mijinki."
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba ganin haka yasa Aunty Rahma fahim tar kunyace ko rashin sabo da zuwa gareshin ke É—awai niya da ita,
Muskutawa tayi cikin dabara tace
"To ai kinga nan É—in ma gadon yakasa mana bazai É—aukemu dukaba ga Ishma da birgima zamu kwana a takure ke kije can.
Kinga den bazamu takuraba maza tashi kinji, ki kula da mijinki kada kiyi yaji haushina yace nina riƙe masa mata, kinga dama ya rainani".
Ta ƙarashe mgnar cikin sigar raha.
"Toh". tace a hankali tamike tasauko daga Kan gadon,
Ita kuwa Aunty Rahma gyara kwanciyarta tayi tace.
"Yauwa in kin fita ki jamana kofar".
Namma to É—in takuma cewa kana ta fita tare da ja musu kofar.
A hankali tanufi parlour'n shi.

A ɓangaren su Umaymah kuwa suna shiga ɗaki Ummi bathroom tashiga taɗan watsa ruwa dan taji daɗin jikinta, bayan ta fitone tayi shirin bacci Nan ta tadda Ummi harta kwanta Amma batayi bacci ba idonta biyu, Zama tayi bakin gado ta fuskanci Ummi da kyau cikin sauƙe numfashi tace.
"Niko Ummin Jabeer anya É—iyarnan taki ba cikine gareta ba kuwa?".
Da sauri Ummi ta mike zaune tana cewa
"Kai Anya kuwa?".
Gyara zama da kyau Umaymah tayi tare dayin murmushi tace
"Nikam dai naga kamar akwai abu tattare da ita. Amma dai sai da safe in Allah yakaimu zan ƙara zuba ido in dubata da kyau in ƙoƙƙofo mana".
Ciki da jin daÉ—i da fatan Allah yasa akwai É—in Ummi tace.
"Allah yakai mu".
Kana sukaa ta kwanta suna mai fatan hakan yazamo gaskiya.

Shatu kuwa a hankali ta kutsa kanta cikin parlour'n da sallama É—auke a bakin ta,
Shiru parlour'n babu motsin komai sai karar A/C da wani sassanyan ƙamshin dake tashi.
A hankali tanufi kofar bedroom É—in shi.
Tura ƙofar tayi a hankali tashiga da sallama kana ta ta mai da kofar tarufe, juyowa tayi cikin ɗan kin cikin nitsuwa da ɗan yanayin bacci.
Can ta hangoshi kan gado.
A dukunkune cikin blanket sai karkarwa yaka.
Cikin sauri haÉ—ida sassarfa tanufi inda yake,
cikin tashin hankali ta hayo kan gadon.
Da sauri tasa hannu tayaye blanket É—in,
Da sauri ta kuma matsoshi ganin yadda jikinsa yake wani irin karkarwa, cikin sananin tashin hankali da tausayi ganin halin da yake ciki takai hannu saman kafaÉ—ar shi tana faÉ—in
"Innalillahi Yah Sheykh meya sameka! dama baka da lfy ne!?.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!".
Ta kuma haÉ—i da karfi lokacin da tasauke hannunta saman kafaÉ—arsa jin wani irin zafin da jikinsa yayi.
Shi kuwa Sheykh kanshi ya ɗago cikin mawuyacin hali yaɗaura kanshi bisa cinyar ta, cusa kanshi ya farayi cikin jikinta cikin sananin zazzafan zazzaɓin da yarufeshi yace
"Aish sanyi, sanyi nakeji".
Yayi maganar cikin mawuyacin hali yana daÉ—a cusa kansa cikin jikinta,
Wani irin sahihin runguma tayi mishi gam-gam tana ƙara mannashi da jikin nata.
Da sauri cire hijabin jikinta.
Tare ƙara tallafe kansa tamanna da ƙirjinta ganin Yadda yaketa manna jikinshi da nata yana bin ɗumin jikinta,
Wasu irin hawayene suka fara sassafo Mata
Murya narawa cike da tausaya mishi tace
"Yah Sheykh da ma haka zazzaɓin yake maka?".
Kai kawai ya iya gyaÉ—a mata alamar Eh
Hannunsa yaɗago da kyar yasauke kan ƙirjinta yacusa cikin bra'n rigar baccin dake jikinta yaciro Cab'b'ulenta duka biyu fuskarsa yacusa sakan kaninsu wani irin numfashi yasauke wanda yasanya Shatu rumtse idanunta jin ɗumin numfashin sa a kirjinta,
Hannunta ta ɗaura kansa a hankali tariƙa shafa sumar kanshi yayin da gudun hawayenta suka d karuwa,
wani irin masifaffen tausayin sane yarufeta,
lamo sukayi a jikin juna. Sun jima sosai a haka.
Kana ta ɗan ronƙofo suka kwanta manne da juna dan ta fahimci ɗumin jikinta yake bi.

Daren ranar dai Shatu taga tashin hankali Danko haka suka kwana basuyi bacci,
Sai can wajen kiran sallar farko zazzab'in yafara tafiya nanne yasamu bacci yaÉ—an É—aukeshi.

Nan itama tasamu tad'an gyangyaÉ—a kaÉ—an.
Kiran sallar asuba kuwa a kunnen shi.
A hankali ya buÉ—e idanunshi tare da addu'a a bikinshi,
ido yatsurawa fuskarta ta kanainayeshi tayi lup a jikinsa tana fidda numfashi a hankali,
wani irin tausayinta ne yakamashi, tuno halin suka kwana jiya yadda baiyi bacci ba haka itama bata runtsaba.
Zame jikinsa yayi a hankali ya miƙe zaune.
Numfashin ya ɗan fesar kana ya sauƙo kan gadon.
Cikin lumshe ido ya nufi bathroom.
Yana mai mamakin yadda zazzaɓin nan yasakeshi watsai kamar ba shiba.
Wanka yayi tare da d'auro Al'awala kana yafito.
Farar jallabiya yazura tare da fesa turare mai sanyin ƙashi sannan ya murza hula bisa sumar kanshi.
Kana yaÉ—an maso bakin gadon da sauri jin ana kokarin tada ikama.
Ragowar ruwan hannunsa ya É—an shafa nata a fuska tare da cewa.
"Aish tashi kije kiyi sallah".
A hankali tayi miƙa tare da buɗe idanunta kana tace.
"Toh, ya jikin naka?".
Murmushi yayi mai cike da jin daÉ—i cikin lumshe ido yace.
"Alhamdulillah da sauƙin tashi kiyi salla ko Boɗɗon Ummey".
Miƙewa zaune tayi.
Kana shikuma yafita.

Wayewar garin ranar kuma.
Shatu Ummi Sara suka shirya lafiyayyen breakfast suka jerashi kan dinning area dake cikin babban parlour.
Abinci kuwa takowani sashi yana fitowa zuwa wannan sashi.
Tuni Aunty Juwairiyya ta iso da nata lafiyayyen breakfast É—in.
Bayan sunyi breakfast suka dawo cikin babban parlour nan suka buÉ—e sabon hira.

Shatu kuwa tun da sukayi breakfast É—in takama hannun Ishma suka koma É—akinta, wanka tayi sannan tayiwa Ishma.

Bayan tafiyar ta ba jimawa Sheykh yashigo parlour'n.
Cike da jin daɗin ganin ƙannen mahaifiyar tasu da aminta ciyar Jakadiyarsu mai kamar uwa.
Ya isa tsakiyar.
Suma cike da jin daÉ—i suke kallonshi.
A hankalu ya zauna kan kujerar dake fuskantar Umaymah.
Yayi wasai da shi kamar bashine jiya ya kwana da zazzafan zazzaɓi ba.

Hira sosai suka buÉ—e sunayi ana dariya da raha.
Shi kuwa Sheykh murmushi yake É—anyi kanshi a sunkuye kan wayarsa da yake É—an lasawa.
Umaymah kuwa gaba É—aya ta maida hankalin ta kanshi, sosai hankalin ta yatashi dan yau tafi ganin ramar tasa da yawa fiye da jiya,
cike da kulawa ta tsare fuskarsa da ido tare da cewa.
"Jazlaan."
A hankali ya É—ago kwayar idanunshi ya kalleta cikin maida hankalinshi kanta yace.
"Na'am Umaymah".
Gyara zamanta tayi ta fuskanceshi da kyau cikin sanyi tace.
"Jazlaan meke damun ka baka da lfy ne wannan ramar duka ta mecece?".
Tajero mashi tambayoyin cikin alamun tashin hankalin.
Mamma da Ummi da Aunty Rahma da Juwairiyya kuwa shiru sukayi suna kallonsu.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya É—an sa hannunshi ya shafi sajenshi.
Wayar hannun sa ya ajiye bisa hannun kujera da yake zaune.
ÆŠan gyara zamanshi yayi tare da gyara zaman al'kebbar jikin sa,
kansa ya É—an tankwasa gefe a hankali yace.
"Umaymah zazzaɓin dare ne yake damuna kullum , da rana kuma zan wuni lfy, da zaran yamma tayi sai zazzaɓin ya rufeni haka zan kwana da shi asuba nayi kuma zai tafi sai wani daren kuma".
Shiru sukayi baki É—ayansu.
Ita kuwa Umaymah hannunta tasa ta tallabe haɓarta.
Numfashi mai sanyi Umaymahn ta fesar tanamai nazartan kalaman sa wani irin yalwataccen murmushi mai faÉ—i Umaymah tayi.
Dai-dai lokacin kuma Shatu ta fito daga É—akinta ta nufosu.
Suma su Mamma duk murmushi sukayi.
Murmushi Mai had'e da dariya Umaymah tayi cike da tsantsar jin daÉ—i
tace.
"Toh Jazlaan ina ga dai ka gaji Abba'n kune fa".

Da sauri ya kalleta tare da cewa.
"Kamar yaya Umaymah da me na ganeshi?".
Cikin sauri ya juyo ya kalli Ummi da Mamma dake cewa.
"Ai kuwa da ala kam tabbas".
Aunty Rahma da Juwairiyya kuwa dariyar jin daÉ—i sukayi.
Shi kuwa Umaymah ya zubawa ido tare da cewa.
"Ban ganeba?".
Cikin sakin fuska tace.
"Eh inaga kam tabbas kayi gado.
Domin tunda Mamey take Bata taɓa yin laulayin cikiba, a rayuwarta, ko su Jalal da suke tagwaye wlh Abbanku ne keyi mata laulayin, shiyasa kafin ma tasan tanada ciki shi yake rigata ganewa.
Toh inaga kaima hakan ne tabbas Shatu nada ciki ni dama na zargi hakan tun isewarmu".
Cikin tsananin jin kunya, Shatu tajuya da sauri ta koma dakinta cikin wani irin masifaffen jin kunya meda ƙofar ɗakin ta rufe.
Bayan ta sukabi da kallo.
cikin wani irin.
Chapter 173 · 0% Book details