← Book details Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 183

Sashe 132

Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana shiga ta ɗan leƙo tare da cewa.
"Ayyah Yah Sheykh dan Allah a kawo min zani mana".
Shiru yayi itama shiru tayi tana leƙenshi.
da alamu abu yake rubutawa a wayarshi.
Saida ya gama har ta buÉ—e baki zatayi mgna.
Sai taga ya miƙe ya fita.

Bai kula su Jamil da Affan ba ya wuce.

Yana buɗe durowar, ya shaƙi ƙamshin sabbin kayayyakin dake jere.
Wata doguwar rigar material Sky blue ya É—auko da É—an kwalinta, ganin akwai rasin fari a jikine yasashi É—aukar mata farin gyale.
Har ya rufe zai juya sai kuma ya dawo.
sunkuyowa ya É—anyi. Inda yaga jerin bra and panties É—auka mata yayi fara.
Sai kuma yaga audugar mata a gefe.
Kwaya É—aya ya zaro kana ya juya ya fita.

A kan gado ya ajiyesu.
Kana ya juya ya fita ya koma falo bai ce mata komaiba.

Sake leƙowan da tayine bayan tayi wonka, taga ya ajiye mata kaya kuma ya juya ya tafi.

Da sauri ta fito da towel É—in shi a jikinta.

Sauri-sauri ta kimtsa jikinta,
ta shirya tsab, sabida taji sauƙin marar tata sosai.

Bathroom É—in ta koma ta wonke wanda ta ciren ta shanyasu a cikin, kana ta fito.
Gaban dreesing mirror ta tsaya, turaren shi ta fesa, kana ta juya ta fito.

Hanyar fita ta nufa, shi kuwa yana tsaye ta sameshi da alamun wani wurin ya nufa, har taje bakin ƙofa yace.
"Zo".
ÆŠan juyowa tayi ta kalleshi ganin kamar bashine yayi mgnarba, yasa ta juya ta nufi hanyar fita.
"Zo". Ya kuma cewa.
A hankali ta juyo, ta nufi inda yake gabanshi ta É—an tsaya.

Kanta a sunkuye.
"Waya baki izinin samin turarena?".
Da sauri ta É—an kalleshi tare da girgiza kai alalum a a.
Fuskar shi ya tsuke tare da cewa.
"Ƙarya nayi miki kenan".
Still kanta ta jujjuya, shi kuwa kallonta yayi sama da ƙasa ya kalli iya tsawonta da ɗan jikinta da wuraren da sukafi abki a jikinta welcome and bay-bay ɗinta.
"Baki da turaren ne?".

"Inada shi".

"To meyasa kika samin nawa".

Baki ta É—an zumbura tare da cewa.
"Nifa bansa maka tutarenka ba".
Tana faÉ—in haka ta juya ta nufi hanyar fita.

Da ido ya rakata, tana fita shi kuma ya buɗe ƙofar da zata sadashi da Garden ɗin da ke bayan sashin nasa.

Washe gari kuma ranar suyan jan nama, sosai Aysha ta tsaya kan aikin, dan cikinta yabar ciwon nanda nan sukayi aikinsu suka gama.

Haka dai akayi shagulgula bikin ƙaramar salla lafiya.

Yau kwana huÉ—u da yin salla a wuni na biyar ne.

Affan da Aunty Juwairiyya kusan a tare suka shigo.

Wani roba mai kyau Affan ya miƙa Aysha tare da cewa.
"Aunty ƙarama gashi inji, Mami a kawo miki".
Murmushi tayi tare da amsar robar.
Soyayyan namane yayi kyau ya samu kekyawan aiki sai nason mai yakeyu.
"Kai a lallai nako gode sosai".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Wai tasan naku duk muke haÉ—uwa muna cinyewa, wai kowa ya bar na gidansa yazo ya cinye naku".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Tayi gsky ai haka kuke gaku bakwa gajiya da cin nama kamar ba Fulani ba.
Gwara ma Jalal shi bai fiye damuwa da namaba amman Kai Affan Jamil Imran da Sulaiman ko kuraye sai haka".
Murmushi sukayi.
Kana Aunty Juwairiyya ma ta miƙo mata robar da tazo dashi tare da cewa.
"Gashi wannan a bawa Sheykh".
Fuska ta É—an yamutsa tare da cewa.
"A a barshi kawai".

Shiru Ummi tayi dan tasan za'ayi hakan.
Ta rasa dalilin da yasa Aysha batason kyautar komin na wurin Juwairiyya da Hajia Mama.
Su kuma basa gajiya da ba amsa takeyin ba sai sun bata.
Cikin tsareta da ido Juwairiyya tace.
"To aini ba ke na bawaba Sheykh nace a bawa".
Fuska a daƙile tace.
"Bazan bashi ba, bazai ciba.
Kije kici abunki. Baya buƙatar nakin".
Da mamaki Affan yace.
"To Aunty ƙarama meyasa".
Juyowa tayi ta É—an kalli Affan tare da cewa.
"Ita ai tasan dalili".
Daga nan ta juya ta nufi É—akinta.
Sosai Affan yayi mamaki.
Ita Juwairiyya kuwa, ciki takaici tace.
"Uhumm lallai ma yarinyar nan, bansan me take nufi da niba, ban san me nayi mata ba, shiyasa yanzu ni bana ko son shigowa nan".

Ta ƙareshe mgnar tana miƙewa zata fita.
A hankali Ummi tace.
"Kiyi haƙuri JUWAIRIYYA KINSAN abubuwan sai a hankali kada ki damu, kin san mutun in yanada ƴar matsala wasu lokutan ma, ba yin kanta bane".
Uhum kawai Juwairiyya tace ta fita.

Sukuwa sukaci gaba da hirarsu.
Washe gari Hajia Mama ta aiko hadimanta su kawowa Sheykh dambun nama.
Suna shiga tace, suje su rabashi an basu.

Dama Ummi kam tasan za'ayi hakan.
Sheykh dake shigowa kuwa cewa yayi.
"Ke aka bawa ne da zaki kyautar dashi".
Fuska ta É—an yamutsa tare da cewa.
"Bazaka ci bane".

Amsar kwanon yayi a hannun Ummi tare da cewa.
"Kuje kuce ngd".

Daga nan ya nufi É—auki shi.
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.

Yana shiga ya ajiye kwanon kan Bedside drower'n.
ÆŠauke kwanon tayi tare da cewa.
"Dan Allah dan Annabi kada kaci, ka barshi, in dambun kakeso ai nayi maka".
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Nata yafi daÉ—i akan naki ai".
Da sauri ta kalleshi idonta na cicciko da hawaye.
Juyawa tayi ta fita da kwanon.
"In kinje kin boye kizo".
Yace mata, to tace.
Ai kuwa taje ta zubar dashi ta bawa Saratu kwanon tace ta maida mata.

A zaune ta sameshi da wata leda a gabanshi.
Nuna mata ledar yayi tare da cewa.
"Gashi ni na mance tun zuwanmu Umrah Aunty Hafsat da Umaymah suka bada sukace in baki".

Sunkuyowa tayi ta É—auki ledar tare da cewa.
"Ngd matuƙa Allah ya biya musu buƙatunsu".

"Amin Amin". Yace.
Juyawa tayi ta fita.

Shi kuwa wayarshi ya zaro yabi bayan kiranda Haroon yaketa mishi.

Ita kuwa Aysha tana shiga É—akinta ta buÉ—e ledar.
Turarukane masu kyau da ƙamshi.
Harda setin na miski da manshi da samubulunshi da turaren.
Taji daÉ—in su sosai.
Dan dama yanzu take shirin tayi wonkan tsarki.
zata ci gaba da salla daga la'asar.

Wonkanma ta shiga, ta fitowa tasa É—aya daga cikin dogayen rigunan da suka turo mata.

Yau kwana goma da yin salla ya kama saura kwana sha biyar auren Haroon da Jannart ƙanwar Juwairiyya.
Tako ina shirye-shiryen biki ya kankama.
Washe gari kuwa su Aunty Hafsat da ahlinta duk suka zo.

Kai tsaye masarauta Leddi julɓe suka nufa.
DaÉ—i a wurin Sitti babu bayani.
Ga Æ´aÆ´anta ga jikokinta, dan Umaymah ma ta kasa jira su iso wurinta randa sukazo da safe suka iso ita kuma da yamma ta iso.
Farin cikin Sitti da Jadda basa faÉ—uwa.
sai dai duk sanda sukayi irin wannan haÉ—uwar, yana tono musu tabo da damuwarsu da tashin hankali su.

Hibba ce ta kira, Aysha, take sanar mata.
Su Aunty Hafsat sun iso. Yanzu an fidda ankon aure da tsara duk abubuwan da zasuyi.
Kwanan Umaymah uku a can ta koma ita da Hibba da Isha yar Aunty Hafsat budurwa, kamar Hibban komai na biki Umaymah ta shiryawa Aysha shi.

Yau auren kwana bakwai bikin.
Suna zaune shida Ummi suna tsara tafiyar tasu.
Dan dole Juwairiyya zataje, amman zata tafi da Ya Jafar da yaransu da Jalal.
Su kuwa zasu tafi da Jamil da Ummin.

Sai Hajia Mama da su Ramla da Batool da har yau bata komaba.

Kiran Haroon ne ya shigo wayarsa.
Bayan sun gaisa ne yake cewa.
"Wai kai Sheykh yaushe zaku zone? Dudufa yau saura kwana bakwai ne, kuma daga gobe za'a fara hidimomin".
Da sauri yace.
"Kai haba Haroon ka nitsu mana kaja numfashi kayi mgna a hankali.
Ni dai bazan je duk sauran shagulgula kiÉ—e-kiÉ—e da raye-raye kuba bazan ce kada kayi bane, sanin Abun harda Aunty Rahma iyayen bidi'a."
Cikin hatsala Haroon yace.
"Za dai kazo kayi mana walima kam".
Kanshi ya gyaÉ—a tare da cewa.
"Eh walimar maza ba, shima dan Abba da kanshi ne yamin mgn da dan ta kaine ba yi zamba sabida, ba amfani da abinda ake faÉ—a a walimar akeyi ba".
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"To Ustazu Allah ya kawo ka lfy".
"Amin". yace
"To yaushe zaku zone?".
Jibi ya bashi amsa a taƙaice."

Daga nan sukaci gaba da hira.

Yau saura kwana biyu bikin kuma yaune zasu tafi.
Aunty Juwairiyya da Ya Jafar da Jalal kuwa tun jiya suka tafi.

Su kuma yau zasu tafi da dare.

Ƙarfe takwas dai-dai jirginsu ya tashi zuwa jihar Tsinako.

Tara dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin birnin Tsinaku.

Bayan sauƙansu da wasu ƴan daƙiƙu, aka buɗe jirgin, kana aka fara fita, daki-daki.
Kasan cewar Ummi da Jamil na ta bakin ƙofar sune suka fara fita.
Sheykh Jabeer da Aysha kuwa suna can VIP Side. Hakan yasa kusan sune ƙarshen-ƙarshen fitowa.

A hankali yake taku cikin nitsuwa da kamala ta nitsastsun malamai magada annabawa.
A hankali ya saƙo ƙafarsa kan step ɗin forko na farfin jirgin.
ido ya lumshe tare da buɗesu yana son jihar Tsinako so mai tarin yawa sabida, yanada jigo shaƙiƙai masu sonshi fiye da yadda suke son kansu.
Su Umaymah, Haroon, ga ƙarinsu Aunty Hafsat, da Aunty Rahma, da ahlinsu.

Hannunshi yasa ya tattare bakin faffaɗan al'kyabbar jikinshi mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi.

Yanayin garin da ɗan hadari, ko ina yayi lib, garin yayi duhu yayi baƙi mai kyau, gajumare masu duhu sunyisa sararin samaniya ƙawanya.
Ga wasu kyawawan ciyawi kore shar da suka malale can baya kaÉ—an, iska mai sanyi ke busowa tana ratsa jiki da jinin mutanen dake wurin.
A hankali take biye dashi a baya inda ya taka ƙafarsa ya cire nan take taka tata ƙafar.

Tayi shigar larabawa tayi masifar kyau, kasan cewar tasa Niƙabi baka iya ganin komai sai fararen idanunta da take ɗan jujjuyawa.

A hankali ya gama sauƙa kan, steps ɗin.
Yayinda ita kuma take step ɗin ƙarshe.
Kanta ta É—an juyo jin dirin wani jirgi a bayansu yana tashi, yana keta gajumare.
Hannunshi yasa a hankali ya kamo nata, da sauri ta É—an juyo jin hannunshi cikin nata.
Takowa tayi ta sauƙo kana ta fara bin takunshi sabida bai rigaya ya sake mata hannun ba.
Chapter 132 · 0% Book details