Sashe 73
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan anyi sallan ne kowa ya kama sabgogin gabanshi.
Shi Jabeer komawa gida yayi.
Ya saka garen kayan jikinshin kana.
Ya fito, Ummi ya samu tsaye a tsakiyar falon, cikin kula tace.
"Zaka fitane?". Kai ya gyaÉ—a mata alamar eh.
ba tare da damuwar rashin bata amsarba tace.
"Da yan rakiya ko kai É—aya?".
Yana gyara zaman hular kanshi yace.
"Ni kaÉ—ai. Zanje gidan Malama Abubakar ne!".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ka gaida minshi".
"In sha Allah zaiji. Umaymah fa?".
Gane abinda yake nufine yasata cewa.
"Tana can sashin Gimbiya Aminatu, wurin É—iyarta Amarya Aysha".
Kanshi ya É—an sunkuyar ba tare da yace mata komai ba,
ya fita.
Malam Abubakar shine, malamin da ya fara É—iga mishi harafin Ba''un a allon shi, wato Be a fillance, Basinmi'arra a hausance ko?.
A wurin shi yayi sauƙan forko, sai dai zuwa yanzu, shi Jabeer shike ƙara wa Malam Abubakar sani, akan Nahawu da Tajwid sabida shi da karatun zaure yayi.
Umaymah kuwa, ita da kanta ta sanarwa LamiÉ—o cewa, gobe Sheykh zai gabatar da amaryarshi.
Haka yasa, ta fara shirya Aysha, shiri na musamman.
Cikin Hadiman Juwairiyya É—aya daga cikinsu.
Mai suna saratu, itace Umaymah tasa ta yarfawa Aysha zanen lalle mai É—an karen kyau.
Kana Ummi da kanta ta wonke mata kai sabida ita keyiwa Juwairiyya ma.
Sosai ta fito ras.
Ita kuwa Shatu duk abinda sukeyi Mata.
Tunanin Hibba al'hinin da tun randa tazo bata kuma ganinta ba.
tana son ta tambayesu ta rasa ta ina zata fara, dole dai haka ta haƙura tai shiru.
Washe gari ranar talata. Da hantsi, ko ina na sashin Gimbiya Aminatu sai ƙashi yakeyi, sabida shiri da kimtsa amarya.
Umaymah da kanta take kimtsata, wani irin dakekken wagambarine mai matukar kyau Royal blue, tasaka doguwar rigace. Tayi cib-cib da jikinta.
wani irin É—auri É—an kwali Aunty Juwairiyya ta murza mata a kanta, irin mai stpes É—in nan.
Kana sai wata farar al'kyabbar masarauta fara ƙal mai kolliyar zaren aiki da ulunta Royal blue.
da surkin Golding color mai sheƙi.
Wasu fararen takalma masu ratsin Sky blue ne a kekyawan kafarta da yasha jan lalle, takalman basu cika tsini da tuduba, sai dai kuma ba dab da ƙasa bane.
Tayi kyau iya kyau, sai ƙamshi da sheƙi take zubawa.
Umaymah ce ta kama hannunta har zuwa falon LamiÉ—o, wanda bai rigaya ya fita fadaba.
Gefen Gimbiya Aminatu ta ajiyeta, kana tace.
"Bari inje inzo da Angon."
Murmushi Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"To kuyi sauri dai".
To tace kana ta fita.
A can sashin Sheykh Jabeer, kuwa.
Da alamun wonka ya fito, a nitse yake kimtsawa, cikin wani fitinenne yadi mai taushin gaske.
yadin Royal blue ne mai masifar kyau.
rigar half jomfa yar tsukekkiya,
tsaki ya É—an ja lokacin daya gama dai-dai-ta zaman rigar a jikinshi sabida tayi kib-kib a jikinshi har kamar ta É—an matseshi.
Wondon kuma irin mai iya kuibin sawune, irin sakun wondunan ahlul sunna.
a hankali ya iso gaban drower'n da hulunanshi da hirami da baƙin abun saman hiramin ke jere a ciki.
Har yasa hannunshi bisa wani farin hula, sai kuma ya sunkuya ya É—an kalli. Kanshi.
Fuskarshi ya É—an tsuke, sai kuma ya É—an juyo jin muryar Haroon yana cewa.
"Wow masha Allah, gsky kayi kyau, Please ka fita haka mana, ka ganka É—an saurayi mai jini a jika, amman in kasa al'kyabbar nan, sai kwarjininka yayi yawa yaseen.
Ni kaina sai inji ina shakkarka,".
Kai ya ɗan shafa kana yasa hannunshi ya zaro hiraminshi fari da baƙin zagayen.
É—aya marfin drower'n ya buÉ—e tare da zaro wata dakekkiyar al'kyabbar fara mai ratsin blue na zaren aiki gaba da bayanshi.
Gaban gado ya dawo yana warware al'kyabbar tare da cewa Haroon.
"In na fita a haka ai ji zanyi kamar babu tufafi a jikina, sabida sunyi min kaÉ—an."
Ya ƙarishe mgnar yana zura al'kyabbar a jikinshi.
Masha Allah, Haroon yace.
Kana ya matsoshi yana tayashi gyara zaman al'kyabbar yana cewa.
"Duk shigar da kayi tana maka kyau, in na ganka ba al'kyabbar sai inga kamar kafi kyau.
In kuma kasa al'kyabbar sai inga kafi kyau".
Baice dashi komaiba yaci gaba da gyara sakun hiraminshi,
saida ya gama dai-dai-ta hiramin sai ya juya ya nufi, wannan drower'n da hulunanshi ke jere a steps biyu na sama.
Biyu na ƙasan kuma jerin takalmanshi ne.
Fararen takalma masu taushi ya saka ƙirar Gucci,
Zara-zaran yatsunshi sarari sabida ba sau ciki bane ba kuma half cover bane.
turare ya fesa, tare da sa hannunshin ya shafa sajenshi.
Kana ya kalli Haroon daketa É—aukar shi hoto.
Cikin tura baki Haroon yace.
"Na bari, nasan yanzu zakayi ƙorafi, yanzu ina zakaje?".
Yana fita yace.
"Valli Hospital, akwai yaron da zan duba aikin da akayi mishi".
Bayanshi ya biyo tare da cewa.
"To sai ka dawo".
Ni zamuje wurin Budurwar Jamil taga babban yayanshi.
Wani kallo ya mushi tare da cewa.
"Allah ya shiryeka babban kobo".
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"Eh naji na yarda, zanje yaro ya samu matsala da ita tanata wahal dashi ba dole inje in dai-dai-ta musu matsalar ba".
Juyowa yayi jin abinda Haroon yace cikin sakin gajeren murmushi yace.
"Uhumm yaushe ka zama luwali, bani da lbri, to kai taka matsalarma yaushe ka warware ta, kun iya cikamu da zancen ku Æ´an soyayya ne, kuma bakuma san yadda ake soyayya da magance matsalolin ta da tattalinta gudun ta lalaceba".
Wani irin dariya mai sauti Haroon yayi tare sara mishi.
Da sauri ya juya, da nufin tafiya,
sai kuma yaga Umaymah na tsaye a gabanshi.
Hannunta tasa ta kamo nashi tare da janshi suka fara tafiya.
Cikin sanyi yace.
"Oh Umaymah ina zamuje?".
Haroon kuwa baki ya taɓe tare da cewa.
"Wlh gobe zan koma in sha Allah, komai sai an nunawa mana Æ´an ubanci".
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya".
Da sauri yace.
"To na fasa tafiya".
Suna gab da fitane yace.
"Umaymah sakeni karmu fita a haka".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"To taho".
To yace mata kana yabi bayanta.
Suna tafiya cikin ƴar faffaɗan hanyar da bishiyoyin namijin gwanda yayi musu ƙawanya,
shiyasa wurin yayi sanyi.
A hankali ya kalleta lokacin da suka iso.
Bakin ƙofar Gimbiya Aminatu.
tare da cewa.
"Umaymah me zanyi a ciki?".
Hannunta tasa ta kamo nashi.
Kawai ta kutsa kai ciki. Dole ya bita a baya.
Yana saka ƙafarsa cikin falon yaji zuciyarshi ta buga,
da ƙarfi, lokaci ɗaya ta fara harbawa da sauri-sauri.
Cikin sanyi yace.
"Umaymah barni a nan".
Bata kulashi ba taci gaba da janshi tayi har bakin ƙofar falon Lamiɗo.
wani irin rumtse idanunshi yayi yin yadda zuciyarshi ke barazar fashewa.
Da sallama a bakinta, suka shiga.
Yayinda LamiÉ—o da Abbanshi suka amsa mata.
Cikin wani irin azabebben bugun da zuciyarshi keyi, yasa ƙafarshi cikin falon.
yayinda Umaymah ke riƙe da hannunshi tana mishi jagora har zuwa gaban Lamiɗo da Galadima da Abbanshi da kuma Malaminshi Malam Abubakar.
Kana ta tsaya dashi kusa da Aysha tare da rusunawa.
Yayinda shi kuma cikin fargabar yadda ƙirjinshi keyi ya rusa a hankali ya zauna bisa tattausan carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin.
Dib, dab, dib, dab, dib, dab. Haka zuciyarshi keyi.
yayinda itama Aysha da bai lura da ita Bama haka zuciyarta keyi,
sabida jin an mutun ya zauna kusa da ita.
A hankali ya lumshe idonshi, sabida bugawar da zuciyoyinsu keyi a tare yasa, ƙarfin nashi bugun ya ɗan ragu kaɗan.
Cikin nitsuwa ya kalli Abbanshi kanshi a sunkuye yace.
"Barka da safiya Abba".
Cikin kula yace.
"Barka dai".
Sai ya kuma kalli Malamin nashi cikin kamala yace.
"Allah hokke sabbugo, Malam Barka da zuwa ya gida?".
Cikin nitsuwa Dattijan yayi murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillah Sheykh Jabeer ya hidima".
Alhamdulillah yace, kana ya kalli LamiÉ—o da Galadima.
sai kuma ya kauda kanshi.
murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Mu bazaka gaishemu ba kenan?".
ÆŠan tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
"Gaggawa dai aikin shaiÉ—an ne".
Murmushi LamiÉ—o yayi sabida ya fahimci duk abinda zasuyi,
sai ya cisu gyara ta kuma fuskar gsky.
Galadima ne yace.
"To ni bari in gaisheka Ina kwana".
Kanshi ya jinina mishi tare da cewa.
"Kayiwa kanka tanadin lada ashirin, a madadin kaÉ—an da zaka samu in ni na É—aga maka gaisuwar.
Lfyta lau Alhamdulillah."
Ya ƙarishe mgnar da amsa gaisuwar.
Dariya sukayi kana, ya kalli Lamiɗo a daƙile yace.
"Ina sauri dan inada aikin yi, menene kasa aka jawoni nan".
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda Abbanshi da Malaminshi bazasu jiba.
Kana ya É—an muskuta ya matsa gefe yayi nesa da Aysha sabida wani tsalle da yakeji zuciyarshi nayi, a madadin bugun da takeyi kafin ya zauna kusa da ita.
Cikin zuba musu ido.
Lamiɗo yayi murmushi sabida sunyi masifar dacewa da juna, shigarsu da ta zamo iri ɗaya tayi matuƙar yi musu kyau.
Cikin wasa irin na kaka da jika yace.
"Ga amaryar taka baku gaisaba, ku gaisa sai ka kaita kuje ka gabatar da ita".
Fuskarshi a haÉ—e yace.
"Hakan addinine ko al'ada?".
Da sauri Galadima yace.
"Al'adace kuma sai kayi ta".
Ta gefen ido ya kalli Galadima tare da cewa.
"Da ba Galadima za'a bakaba, da sarkin raya al'adu za'a baka".
Shiru yayi jin Abbanshi na cewa.
"Allah ya bamu nisan kwana, kaima watan watarana a gabanka yaranka zasuyi min haka Muhammad".
Cikin yin ƙasa da kai cikin girmamawa da karrama mgnar mahaifin nashi yace.
"Sun isa! Suyi maka haka in barsu".
Murmushi Malam Abubakar yayi tare da cewa.
"Kamar yadda ka isaba".
Shiru yayi gane manufarsu.
Jin duk sunyi shiru ne, yasashi É—ago kai ya kallesu.
Suma shi suka zubawa ido, da sauri yayi ƙasa da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tamkar ruwa ya cinyeta, tanajin yadda suke musayan kalamai. Sai dai bata fahimtarsu domin, tuno nata ahlin.
Gyaran muryan da Abbansa yayine yasashi É—ago kai ya kalleshi.