Sashe 3
Garkuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Parvina kuwa da sauri ta faÉ—a jikin baiwar Allah'n tare da ruggumeta.
Baki na rawa ta fara addu'a.
"Allahumma inni as'aluka khairaha wa'azubika min sharri ha".
Da ƙarfi take fidda sautinta tana maimaita addu'ar.
Wanda sanadin haka suma kab suka fara bin bakinta.
Allah cikin ikonsa da ƙudurarsa sai ga iskar nan ta fara lafawa a hankali.
Cikin al'ajibi da tsoron ƙudurar Allah suka ware idanunsu baki ɗaya a kan baiwar Allah'n nan, da
shigar suturar dake jikinta ne yayi masifar sasu ruÉ—ani.
Cikin dakiya da ƙarfin zuciya Arɗo Babayo ya kalli Buba a hankali yace.
"Buba É—auki su GiÉ—aÉ—o ku tafi garke kuje kuyi tatsa".
Kai ya gyaÉ—a mishi domin baki da jarumar Buba sun tafi,
Dan a iya tsawon tarihin rayuwarsa ko a films ko a books story bai taba ji da katari da makamancin abinda ya yagini a zahiriyaba, tsuntsuwar Kurciyar ta zama mutun mace a gabanshi ba labari aka bashiba ra'anul ayni.
Cikin yanayin tarin kaÉ—uwa da rawan jiki yasa hannu ya jawo hannun GiÉ—aÉ—o daya kifa kanshi jikin babanshi.
Cikin fillanci yace.
"Zo GiÉ—aÉ—o zomu tafi".
Da sauri ya miƙa hannunshi ya kama na Buba kana suka juya suka fita.
Appa kuwa kanshi ya kauda daga kallon wannan kekyawar halittar dake gabanshi a cikin ransa yace.
"Anya kuwa, wannan mutunce ba iskaba".
Inna kuwa gefe ta É—an matsa cikin rawan murya na tsoro da hausar da sai ka dage zaka gane me take cewa tace.
"Ra ga Allah bewar Allah mutun ko al'jan?".
Ido suka tsurawa matar a zatonsu ko zata basu amsa.
Sai dai ganin yanayin da take cikine ya sasu cire tsammanin samun amsarta.
Domin gaba É—aya jikinta karkarwa yakeyi, tamkar mazari.
Kana sai zufa dake tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta,
ta rumtse idanunta da azaban ƙarfi, tasa haƙoranta ta datse lip ɗinta na ƙasa,
duk mace data taɓa haihuwa in ta ganta tasan naƙudace ke azazzabarta.
Tausayin ta ne ya cika zuƙa tansu baki ɗaya.
Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace.
"Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al'jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al'amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace".
Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa.
Appa ne ya kalleta tare da gyaÉ—a mata kai, alamun eh ta taimaketa,
Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace.
"Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata".
Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace.
"Zo nan Parvina za'a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta,
kinga ki dena danne mata hannun da cikinta".
kai ta gyaÉ—a kana ta kalli matar cikin sanyi tace.
"Sannu!". Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu,
haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba.
cikin sanyi tace.
"Taso muje daga ciki".
ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji,
hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye.
Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas.
Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin É—akinta ta kaita,
a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta,
da sauri ta koma woje wuta ta hura ta É—aura ruwan zafi.
Kana ta dawo ciki.
Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta.
Gefenta ta zauna ta zuba mata ido.
Jin an zauna gefen tanne yasa ta buÉ—e kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace.
"Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji,
murmushi inna tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana".
Kanta ta jujjuya mata alamun.
"Bazan iyaba".
Jin muryarsu ArÉ—o Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito,
Ganin ArÉ—o Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa.
"Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa".
Taburma ta shimfaÉ—a musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa.
"A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?".
"Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne".
Inna ta faÉ—a cikin alhini.
Sarkin bakanne yayi É—an gyaran murya kana yace.
"Ina son ganinta".
ArÉ—o Babayo ne yace.
"To bisimilla, shigo daga ciki".
ÆŠakin suka nufa Inna na gaba ArÉ—o Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya.
Suna shiga suka sameta zaune ta haÉ—e jikinta wuri É—aya,
jin motsin shigowar mutanene yasa ta É—ago kanta,
da sauri ta kauda idanunta.
Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al'hini yake cewa.
"Mutun ce ba al'janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki."
Sai kuma ya kalli ArÉ—o Babayo cikin sauri yace.
"Maza a bani madarar shanu mai É—umi wanda aka tatsa yanzu".
To ArÉ—o Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono,
da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin.
Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan,
yana amsar ƙoryar,
ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar,
saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace.
"A bani zuma da zam-zam".
Da sauri tace.
"To". Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,'.
Kana ya bawa Malam Liman da ArÉ—o Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar.
Inna ya miƙawa kwaryar yace.
"Gashi bata tasha".
Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta.
Tare da cewa. "Bismillah ki Sha".
A hankali ta buÉ—e bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haÉ—e da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa.
Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta.
Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna.
Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar.
Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin É—akin ta wuce.
Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa.
Bayan sun yanke cibiya sun gyara,
komai na wurin.
Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka,
ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haÉ—eta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle.
Koda suka fito daga wonka,
konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da Æ´ar a gabanta.
Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa,
Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al'ƙur'ani mai girma da tarin addu'o'in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma.
Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje.
Sashin ArÉ—o Babayo suka nufa,
suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy.
Shiru sukayi baki É—ayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana.
"To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah".
Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa.
"Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka.
Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaÉ—anne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana".
ArÉ—o Babayo ne yace.
"Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al'ajabi".
Kai ya gyaÉ—a mishi tare da cewa.
"ÆŠan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi É—an adam dare".
Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa.
"Yanzu tayi magana ne?".
Da sauri Inna tace.
"A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace zan bata magunguna kuma,
sannan kada kuji tsoronta ko kaÉ—an in sha Allah ba mai cutarwa bace".
Malam Liman ne ya gyara babbar rigarshi tare da cewa.
"To wannan baiwar Allah'n ko daga ina ta fito? Ko ta yaya zamu gano yan uwanta danginta ahlinta ko wani nata a duniya?".

"In sha Allah ita in ta dawo haiyacinta, zatayi mana bayanin komai zata faÉ—a mana sunanta sunan garinsu sunan iyayenta sunan mijinta da anguwarsu sai mu mikata garesu".
Appa ne ya É—anyi ajiyan zuciya tare da cewa.
"Allah ya bata lfy ya kuma dawo da ita cikin haiyacinta, kuma in sha Allah duk wani abu daya kamata ayimata a duniya zan mata har sai munga ta samu' lafiya ta koma ga iyayenta".
Da haka sukayi ta tattauna duk abinda ya dace ayi mata.
Anan kuma sarkin baka yaje da kanshi ya É—aure mata karayar hannunta yayinda Parvina kuwa ke like da ita...!
Haka Inna da iya laure sukayi ta kula da ita a cikin wannan satin sunan...!
************